Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yaya Zan Rage Yawan Yin Mantuwa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam ina so a ba ni addu'ar maganin mantuwa idan da akwai, na kasance ina yawan manta abubuwa gaskiya kwakwalwata ta daina daukan abu, ina dauka sai ba da jimawa ba sai na manta.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, A gaskiya ni ban san wata addu'a keɓantacciya da ta gangaro daga Manzon Allah wadda take taimakawa wajen hana mantuwa ba, sai dai kawai shawarar da zan ba ki shi ne, ki riƙa yin addu'a da kanki a kan Allah ya raba ki da yawan yin mantuwa na rashin kiyaye abu, kuma ki ƙara ƙoƙari wajen nesantar saɓa wa Allah Ta'ala, sannan kuma ki yi ƙoƙari wajen ƙara kiyaye waɗannan abubuwa:

1. Rage yawan surutai da ba a buƙatar su.

2. Samun isasshen barci a kullum.

3. Naci wajen haddace abin da ake da nufin haddacewa ta hanyar yawan maimaita shi.

4. Rage wa kai yawan hidindimu, da kaucewa yawan zullumi.

5. Lizimtar karatun Alƙur'ani.

6. Sa ikhlasi a cikin al'amura, wato duk abin da za ki yi, ki yi shi don Allah.

In Allah ya so Allah zai yaye maki yawan mantuwa idan kika kiyaye waɗannan abubuwa.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

 Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments