𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam dan Allah ina da tambaya, ni ce ina tare da mijina, to ni na kasance me yawan sha'awa ne ba na iya kwana uku ba tare da namiji ba, kuma mijina ya san matsalata sarai, shi ya sa ko da bai bi ni ba ni ina bin sa, amma idan ya tashi mugunta, to ko na bi shi sai ya ce mini shi ba zai iya wani abu ba, ko kuma sai ya dunga gudu na kamar ya ga dodo, amma kuma sai ya dunga tafiya waje gurin matan banza yana kwana da su, idan na yi mishi magana me ya sa yake gudu na sai ya ce mini yana min horo ne, ni kuma na san har ga Allah ban yi mishi komai ba, wallahi a sanadiyyar haka na fada wata mummunar hanya, ga ni da aurena amma ina bin mazan mutane a waje, don na ga ni ba ya damuwa da ni, ni ma shi ne na fita harkanshi, dan Allah ina neman mafita, kuma ina neman ku taya ni da addu'a Allah ya ba ni maslaha tsakanina da mai gidana, na gode a tashi lafiya.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu, Allah shi kyauta! A gaskiya wannan abu da kika aikata babban laifi ne ‘yar
uwa, kuma shi ma mijin naki ya aikata babban laifi, in har maganar da kika faɗa cewa shi ma yana kwana da
matan banza ya tabbata, don haka ya wajaba a kanku gaba ɗaya ku nemi gafarar Allah Mai Girma da Buwaya,
ku yi ta istigfári a kan wannan cin amana da kuke wa junanku, in Allah ya so
Allah zai dube ku da idon rahama idan kun yi tuba ta gaskiya, saboda Allah mai
amsar tubar bawa ne matuƙar ya nemi tuba.
Kuma ki ji tsoron
Allah, ki riƙa
haƙuri
da ƙarfin
sha'awarki a duk lokacin da ta motso maki, ki yawaita yin azumin Litinin da
Alhamis, da azumi ukun nan da ake yi a kowane wata. Idan kuma akwai wani
mummunar abu da kika san kina wa mijin naki wanda ba ya so, sai ki ji tsoron
Allah ki daina yi masa wannan abun, idan akwai rashin tsafta ma duk sai ki yi ƙoƙari ki
gyara, saboda wasu mazajen da yawa sukan guji matansu ne saboda ƙazanta.
Ki riƙa ƙoƙarin
kasancewa da alwala da shagaltuwa da yawan karatun Alƙur'ani a kowane lokaci
idan hakan ya samu, ki yawaita yin addu'a a kan Allah ya raba ki da aikata duk
wani mugun hali, da ƙarfin Ubangiji Allah za ki sami mafita.
Kuma yana daga
cikin haƙƙi
na wajibi na kowane ɗaya
a kan ɗaya a tsakanin
ma'aurata, shi ne sauke haƙƙin saduwa ga kowane ɓangare
gwargwadon buƙata, duk wanda ya tauye ma wani a cikin ma'aurata, to Allah
zai kama shi da rashin cika wannan haƙƙi, saboda rashin biya wa juna buƙata a
tsakanin ma'aurata yana iya sa ɗayansu
ko su duka su faɗa wa
hanyar haram. Allah shi yaye ma duk masu wannan matsala, amin.
Allah ne mafi
sani.
Jamilu Ibrahim
Sarki, Zaria.✍🏻
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.