Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne hukuncin namiji mai biye-biyen mata bayan yana da aure?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Namiji Mai Biye-Biyen Mata Bayan Yana Da Aure Iyalinsa Tana Iya Kokarinta Wajan Bashi Hakkinsa.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Lallai wannan mijin bai kyauta ba kuma abun da yake aikatawa haɗarine mai girma agareshi anan duniya da kuma lahira, kuma abun bakin cikine yakamata yagane bashi kaɗai keda hakki a kanki ba, kema kina da hakki a kansa ya nuna kulawa da kishi da kuma barin abun da duk zai ɓata miki rai, kozai saki damuwa matukar wannan abun ba saɓon Allah ba ne.

Shi ne wanda shari'ar musulunci take kira da dayyus, wato sakarai shasaha wandaba ya kishin matarsa ko kannensa mata ya kyalesu sakaka suna abun da sukaga dama, ko kumaba ya kishin matarsa kwata-kwata, kawai yadauki matarsa amatsayin mai dafa masa abunci ba ruwansa, zaije ya yita mu'amala da wasu matayen, wannan sharri ne mai girma, domin irin waɗannan matayen ne in ba a samu mai tsoran Allah ba, itama sai tafaɗa wasu dabi'u da ababe marasa kyau, akwai waɗanda tsabar lalacewa sune suke baiwa matayan nasu dama cewa suma suna iya yin mu'amala da kowa, hakika matarka tanada daraja da mutunci domin ita ce suturarka kamar yanda Alƙur'ani yanuna, ba daidai ba ne kabarta gida kaje kana biyewa wasu akwararo, kuma ya kamata kasani waɗannan waɗanda kake biyewa bawani abu sukafi taka matarba, kai takama tafisu kawai saboda su sun tuɓe rigar mutunci suna fito na fito da Allah ne har kake ganin wani abu atare dasu, domin suɗin kamar shaddar kasuwa suke kowa zai hausu ya yikashi.

lallai wanna miji naki yakamata yaji tsoran Allah yatuba yadena, kuma kicigaba da rokon Allah Allah ya shiryar miki dashi, sannan kibi duk wasu hanyoyi na hikima da fasaha ki nunar masa abun da yake yana matukar kona miki rai, kuma ki tunatar da shi lallai wannan mugun aikine yake, inda hali ki haɗa da abokansa iyayensa da duk wanda kika san yanajin nauyinsu danya dena wannan dabi'a yadawo gareki, inkinbi duk waɗannan hanyoyin bai daina ba, kinemi taimakon Allah kawai a raba aurenku Allah ya musanya miki da mai kishinki mai kiyaye addinin Allah madaukakin sarki.

Hadisi yazo daka manzan Allah sallahu Alaihi wasallam, daka abdullahi dan umar Allah yakara masa yarda ya ce manzan Allah ya ce, (mutane uku Allah yaharamta musu aljannah, wanda ya dawwama yana shan giya har yamutu, da kuma maiyawan saɓawa iyayensa, da kuma dayyus sakaran da yake tabbatar da ɓarna a cikin iyalinsa ba ya kishinsu,) Imamu Ahmad.

Malam haisami ya ce: a cikin mu'ujamul zawa'id a cikin hadisin akwai rawin da ba a ambata ba, amma sauran mutanen da suka ruwaito shi dukansu amintattu ne, Dabarani ya ruwaito daka Ammar bin yasir Manzonn Allah ya ce: (Mutane uku, ba za su shiga aljannaba har abada, Mace mai kamanceceniya da maza, da kuma wanda yake shan giya har yamutu, da dayyus sokwan da ba ya damuwa da wanda yake shiga wajan ahlinsa,ba ya kishinsu.

A bisa wannan duk wanda ya yi duba da hadisn farko duk da hadisi nabiyu akwai rauni a cikin ruwayarsa, zai fahimci dayyus shi ne wanda yake kyale ɓarna a cikin iyalinsa tana wakana kuma baidamu ba, ko yake bada kofar da kowacce irin ɓarna za ta iya faruwa a kan iyalinsa, domin duk wanda bai damu da matarsa baba ya kishinta yana bin wasu awaje, hakika yakyale babbar kofa ta faruwar fitina a cikin iyalinsa. Sa'annan kuma wadda keda miji irin wannan kuma ta tabbatar da yana wannan biye-biyen matan, ba zargi ba ne to sai ta fara masa nasiha cikin hikima da kuma rokon Allah ya shiryar mata da mijinta da cigaba da gyara jikinta sosai ta hanyoyin da suka halatta (maganar gaskiya da yawan matanmu na arewacin ƙasarnan suna wasa da gyaran jikinsu) da yawan mazaje shi yasa shaiɗan ke samun galaba a kansu sai na wajen suke ba su sha'awa kuma alhali ba komai suka fi na auren ba kawai su na auren basa gyara jikinsu ne, to idan tabi duk waɗannan matakan tayi-tayi yaƙi dainawa to sai ta janyo magabata a cikin lamarin, idan ya ƙi bari to za ta iya neman rabuwa da shi Allah ya musanya mata da wani nagari saboda yana iya dauko musu wani ciwo can wajen fasikancin nasa. Allah ya kiyaye!

ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments