Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kallon Hotunan Batsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Kallan Hotunan Batsa Masu Motsi Wato (Blue Film) Da Marasa Motsi (Photo Graphy)

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Haramunne ga musulmi namiji ko mace kallan hotonan batsa, ajaridane ko a set lite ko TV koma tawacce kaface harammun ne, yana cikin manyan laifuka munana da halaye na kaskanci da wulakanci, haramcin yafi girma idan mutum yamaida abun al'adarsa bayajin komai wajan aikata hakan kaitsaye, kuma babu shakka yana cikin zina da ido, Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Allah yana rubutawa ɗan Adam kasansa na zina, zai riski wannan kasan babu makawa, zinar idanuwa shi ne kallo, Zinar baki magana zance, zuciya tai buri ta yi sha'wa, farzi shizai gaskata koya karyata) Bukhari da Muslim.

Dawwama a kan haka yana gadarwa da mutum da kekashewar zuciya, da raunin addini, da raunin tunani da basira, da lalacewar fidra dabi'a ta mutum kaga mutum yana fita daka dabi'a irinta sauran mutane, da firgici azuciya, da duhun fuska, yana fatattaka kunya irinta mace dakame kai irin na mace, duk da wannan aikin baikai zina ta asali girman laifiba kuma babu wani haddi da shari'a tahukuntar ayiwa mutum anan duniya a kansa akwai muni sosai a cikinsa.

Kallon irin waɗannan videos da hotuna na batsa akwai ɓarna maiyawa atattare da illar dakallansu ke haifarwa maiyin sa, daka ciki yakan zayyanawa mutum ganin kyawun alfasha wato zina mutum yadauketa bakomaiba, tayarda sha'awa datasirantuwa da irin hanyoyin damasu aikata laifin suke wajan yin zina dawasu dabi'u nayahudawa irin na dabbobi, mace tadunga gudun mijinta, miji yadunga gudun matarsa.

Wajibine ga musulmi yaruntse ganinsa daka dukkan abun da Allah yaharamta kallansa, Allah madaukakin sarki ya ce:

قُلْ لِلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ

kace da mumuinai maza da mata su runtse idanuwansu ganinsu daka haram, sukiyaye farjinsu (daka aikata zina) wannan shi ne abun da yafi tsafta agaresu lallai Allah mai baiwa mutane labarin abun da suka aikatane ranar alkiyama.

Makiyan musulunci da musulmai suna yaɗa waɗannan hotuna na batsa agaruruwan musulmai dakafofin sadarwar zamani na internet. Sun kuma samar da gurare da dama a kan internet kebantu na yaɗa waɗannan bala'o'i.

Haramunne musulmi yadunga ziyartar ko kallan waɗannan hotuna na batsa ko zuwa inda ake yaɗasu ko ɗauka yakai gidansa da kansa harma yadunga nunawa iyalinsa da kansa tsabar tambadewa da lalacewa, ko haɗuwa sukallah shida iyalinsa, ko yaɗasu ko janyo wani wanda bai taɓa kallaba kajanyoshi danya dawo yanajin dadin kallonsu, kotarayya damasu akaitasu takowanne irin salo.

Duk wanda yadauki wannan bala'i yakai gidansa, ko yayarda akallah agidansa to hakika yaci amanar Allah da Manzonsa da Amanar iyalin da Allah yadamka ahannunsa, akwai nau'in rashin kishin iyali atattare da shi wanda Annabi sallallahu Alaihi wsallam ya ce: Mara kishin iyalinsa tsinanne ne.

Allah ya yi mana tsari da Shaiɗan Abokin gabarmu na hakika dare da rana.

والله أعلم وصلى اللهم وسلما على نبيينا محمد وآله وصحبه ومن تبعهم بإحسان إلى يوم الدين

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments