Ticker

6/recent/ticker-posts

Fa'idar Sautin Zakara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Malam da fatan duk kuna nan lafiya, don Allah tambayata ita ce: mene ne hukuncin zagin zakara, kuma shin kukan da zakara ke yi yana da wata fa'ida ce a addinance? Don Allah a taimaka a amsa mani wannan tambayar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, 'yar uwa gaba ɗaya ma zagin dabbobi ko la'antarsu bai halasta ba, saboda Imrana ɗan Husaini Allah ya ƙara masa yarda ya ba da labari cewa: wata rana Manzon Allah yana cikin halin tafiya, sai ya ji wata mata da take kan raƙuma ta tsine wa raƙumar, da Manzon Allah ya ji haka sai ya ce: "ku ɗauke kayan da ke kan raƙumar nan, ku ƙyale ta, saboda an riga an tsine mata". Kamar yadda Muslim ya ruwaito a hadisi mai lamba ta (2595).

Sai wannan ya nuna bai halasta mutum ya zagi wata dabba ko ya tsine mata ba, ko kuma mutum ya zagi abin hawansa ko ya tsine masa ba.

Game da kuka ko carar da zakara ke yi, ya tabbata daga Abu Hurairata Allah ya ƙara masa yarda cewa: Lallai Annabi ya ce: "Idan kuka ji carar zakara to ku roƙi Allah daga falalarsa, saboda lallai ya ga Mala'ika ne, idan kuka ji kukan jaki kuwa to ku nemi tsari daga Allah, saboda lallai Shaiɗan ya gani". Albukhariy (3303), Muslim (2729).

Wannan hadisin sai ya nuna cewa idan zakara ya zo yana cara ba zagin sa ya kamata a yi ba, addu'a aka sunnanta a yi, saboda Mala'iku suna kusa da su ɗaga addu'ar bawa zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Sai dai wasu malaman sun ce: Ma'anar hadisin nan ba yana nufin zakara ba ya yin cara har sai idan ya ga Mala'ika ba ne, haka ba yana nufin jaki ba ya yin kuka har sai idan ya ga Shaiɗan ba ne, sau da yawa sukan yi kukan saboda wani abu da ya bijiro masu, ba don saboda da ganin Mala'ika ko Shaiɗan ba, duk da kukan nasu yakan zamo saboda ganinsu ɗin, to amma dai ko ma dai mene ne, an so a yi addu'a a lokacin da aka ji carar zakara, sannan a nemi tsari idan aka ji kukan jaki...

Duba Mir'átul Mafátih Sharhu Mishkátil Masábih (8/167).

Allah Ta'ála ne mafi sanin dai-dai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments