Shin Zakkar Fidda Kai Tana Faɗuwa Idan Lokacinta Ya Wuce?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin Zakkar Fidda Kai Tana Faɗuwa Idan Lokacinta Ya Wuce?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Ya zo acikin Nailul Audããr (4/218) "Jinkirta zakkar fidda-kai daka ranar idi, ibnu raslan ya ce: Haramunne a ittifaƙin malamai, domin zakkah ce ta wajibi, dolene wajan jinkirtata asamu zunubi, kamar kin fita sallah ne alokacinta.

    Ya wajaba ga wanda bai fitar da itaba ashekarun dasuka gabata yafitar da ita tare da tuba da istigfari, domin hakkin talakawace da miskinai, bata faduwa face ka bayar da ita garesu.

    Akan haka malaman mazhabobi huɗu sukai ittifaƙi.

    Hanafiyyah suka ce: Idan mutum ya jinkirta fitar da ita aranar idi bata fadi akansaba, dole yafitar da ita koda andauki lokaci mai tsawo bai fitar da itaba. jauhara (1/135).

    Ya zo a sharhin muktasrul khalil mawahibul jaleel (2/376)

    " Bata faduwa dan lokacinta ya wuce, acikin mudawwana " idan wani ya jinkirtata wajibine ya ramata koda bayan shekarune.

    Ya zo Acikin Almugni Muhtaaj (2/112)

    Haramunne jinkirtata daka lokacinta, batare dawani uzuri ba, kamar mutum yarasa dukiyarsa, idan ya jinkirtata batare da uzuri ba yayi saɓo.

    Marudi ya ce: wajabcinta baya faduwa dan mutum yaki bayar da ita alokacinta babu wata jayayyah a'abun da nasani, Al'insaaf (3/1177).

    Malaman lajnatul da'imah suka ce:

    "Wajibine ga wanda bai fitar da zakkar fidda-kai ba yatuba ga Allah, yanemi gafara, domin shi mai Saɓo ne na kin fitar da ita, kuma ya tashi wajan fitar da ita zuwa ga waɗanda suka can-canta, bayan sallar idi ana daukarta sadaka daka cikin sadakoki.

    WALLAHU A'ALAM .

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.