Mene ne hukuncin ajiye azumi saboda aikin gida?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mace ce takeda juna biyu, to idan ta ɗau azumi tana aikin gida kamar girki tana shan wahala sosai, in ba aiki tana iya kai azumin lafiya, za ta iya ajiye azumin in aiki zai mata yawa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Toh aikin gida wannan asali baya cikin uzurorin da zesa mace ta ajiye azumi. Kuma mata nawane suke yin azumin alhali suna yin aikin gida? Akwai matanda har gona suke zuwa suyi aiki alhali kuma suna azumi. Kaga kenan asali aikin gida baya hana mace ta yi azumi, sai dai in ba ta da lafiyane kawai kokuma wata larurar daban amma ko gidansu idan ta koma za ta ga mahaifiyarta bata gaza yin azumi saboda kawai tana aikin gida. Toh itama wannan ya kamata tadai bincika tagano abunda yake hanata yin azumi. Amma aikin gida bazesa ta ajiye azumiba, inyaso seta dinga yin aikin a cikin dare kokuma tasan yadda za ta yiwa kanta tsari amma kowacce mace tana azumin kuma ahakan take gudanarda aikin gida, to babu dalilinda zesa ke a ce ki ajiye azumi saboda aikin gida. Sai dai idan akwai wata matsalane seku nemi magani kokuma ku nema wata mafita amma dai azumi kam ba'a ajjeshi dan aikin gida.

    Allah ya sa mudace

    🏼Jameel Alhasan Haruna Kabo (ABU ZULAIKHA)

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.