Ticker

6/recent/ticker-posts

Al'adar Wasan Tashe A Ƙasar Hausa

 Al'adar Wasan Tashe A Ƙasar Hausa

ABUBAKAR S SABIU (SARKI)
07039311880

Tashe 

MA'ANAR TASHE

Masana da dama sun bayyana ma'anar tashe kamar haka:

Umar M.B (1987) Ya bayyana ma'anar tashe da cewa, "Tashe wata al'ada ce da ake yi a lokacin azumin watan Ramalana.

Da wannan ana iya cewa tashe wani wasan kwaikwayo ne da ake yi cikin raha da annushuwa da kayatarwa a a goma farko ta cikin watan azumin Ramalana.

ASALIN KALMAR TASHE

 kalmar 'tashe' ta samo asali ne daga kalmar 'tashi' wato mutum ya tashi domin sahur yayin ɗaukar azumi. Wasannin tashe sun samo asali ne daga Nalako, wanda sarki

ne yake naɗa shi a matsayin sarkin gwagware - wadanda suka daɗe ba su yi aure ba.

Nalako yana kewayawa ne yana wasanni don tashin gwagware daga bacci saboda ba su da matan da za su riƙa tashin su. Kuma da daddare ne Nalako yake wasa bayan an gama sahur, daga nan ne mutane suka fara kwaikwayonsa suna yin tashe.

Wannan Al'ada ce bayan zuwan addini musulunci ƙasar Hausa, don haka galibi irin waƙen da ake yi ana shigar da abin da ya danganci addini, musamman kalmomi da ke nuna Bahaushe addininsa musulunci ne.

RUKUNONIN MASU TASHE

Akwai rukuni na masu aiwatar da Tashe.

1-Tashen Maza

2-Tashen Mata.

1- Tashen maza: akwai wasan yara maza na nuna jarumta misali: wasan tashen 'inda hali ya yi ba gudu ba tsoro"  yara na sanya kayayyaki na al'ada kamar guru da laya da wuƙa da takobi na katako suna zagaya wa cikin gari suna nishaɗantar da magidanta.

2- Tashen mata:  akwai wasan "Mairama da Daudu inda 'yan mata sukan yi shiga ta namiji a shimfiɗa tabarwa ana rera baituka kamar

"Dauko ruwansa ki ba shi

Dauko tuwonsa ki ba shi

Dauko furarsa ki ba shi

Sai kin durƙusa ki ba shi, sai kin rausaya ki ba shi".

Wa ake yi wa tashe?

Nalako yana yi wa sarakuna tashe

Lokacin Tashe ana shiga gidaje ne in da yara suke shiga gida-

gida suna aiwatar da wasanninsu na tashe. Wani lokaci ana

tashe da rana amma an fi yi bayan sallar isha'i.

Muhimmacin tashe

1- Tashe yana taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihi.

2-Tashe yana nishaɗantar da masu azumi.

3-  Tashe yana ɗauke ko mantar da gajiyar Azumi.

Kammalawa

Tashe Al'ada ce da take koyar da kyawawan abubuwa kala-kala. A gefe guda kuma tana nishaɗantar da al'umma da saka mutane raha.

Yana da kyau a ƙara farfaɗo da wannan Al'ada ta tashe, duba da yadda ake nema a yi watsi da ita.

Post a Comment

0 Comments