Ticker

6/recent/ticker-posts

Jini Ya Dawo Bayan Ya Ɗauke

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum

Malam ni ce na haihu toh sai na yi wanka na fara ibada sai jini ya dawo har yadauke na fara ibada sai nazo nagan shi ɗan kaɗan wanda bekai ya stain pant ba amma kuma jini ne jajur nagani da asuba sai bangane ba, kuma ya hukuncin azumi na kuma mene ne kayadadden lokacinsa don nakai kwanaki 40.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikumus salamam

Idan mace ta haihu Jini yakan zo mata a dalilin haihuwa. Wannan jinin shi ake kira Nifaas (Jinin biƙi), ita kuma macen ita ake kira Nufasa'u (Mai jinin biƙi), idan mace na cikin jinin haihuwa, toh baza ta yi sallah ko azumi ba, kuma mijinta bazai zo mata ba har sai ta samu tsarki ko ta cika adadin kwanakin jinin haihuwa, adadin kuwa shi ne kwanaki 40.

Imam Tirmizi (rahimahullah) ya ce: Mutanen ilimi daga Sahabban Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) da tabi'ina da wadanda suke bayansu sun haɗu a kan cewa mace mai jinin biƙi za ta daina yin sallah da azumi na tsawon kwanaki 40 har sai idan ta samu tsarki kafin cikar kwanaki 40 din. Idan Jini ya dauke kafin cikar kwanaki 40 toh za ta yi wanka ta yi sallah.

Idan ta ga Jini bayan kwanaki 40, mafi yawan malaman ilimi sukace bazata daina sallah ba bayan kwanaki 40, za ta cigaba da sallah da ibaada. Wannan shi ne ƙaulin mafiya yawan malamai. Daga cikinsu akwai Sufyaan Athuuriy da Ibn Mubaarak da Shafi'i da Ahmad da Ishaaƙ. (Sunan Tirmizi, 1/256).

Malaman Al-Lajnatu al-da'imah lil iftaa'a sunce: Idan mace ta ga tsarki (Jini ya dauke) kafin cikar kwanaki 40, toh za ta yi wanka ta yi sallah da azumi kuma mijinta ya zo mata (ya sadu da ita). Idan Jini ya cigaba da zuwa mata bayan kwanaki 40, toh za ta cigaba da daukar hukuncin tsarki ne. Saboda kwanaki 40 su ne adadin kwanakin da jinin haihuwa yake hana ibaada a cikinsu abisa zancen malamai mafi inganci. Jinin da ya zo mata bayan kwanaki 40 za ta dauke shi a matsayin jinin rashin lafiya kuma yana daukar hukuncin istihaadha ne. Saifa idan jinin ya zo mata ne a lokacin da ta saba yin al'adarta.

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/I08Ƙc4ehEctLMSfks5awuZ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments