Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Ai-Sufrah Ko Al-Kudrah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum warahmatullah Malam Allah ya taimaka na yi wankan daukewar haila bayan na ga alamar discharge babu jini sai dai karni karni kaɗan bayan awanni na kuma dubawa sai na ga wani discharge din da ya fi na farkon haske sai na kuma sake wankan to Malam yaya ibaduna sannan na taɓa ji ance shi discharge din da yake fita bayan Al'ada yana kanshin hudar dabino wanda yake ni ban san kanshin ba abunda ya sa na yi wankan shi ne sabida azumi kar na wayi gari ba tare da na dauki azumi ba Malam sai na sake wani wankan da kuma azumin da nake yi bayan wankan Allah ya saka da Alkhairi ya taimaka na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To, wannan nau'in ruwan da kika ga yana fito miki shi ake cema AI-SUFRAH ko AL-KUDRAH, shi ne yake ma mace kamar ruwan Siminti (Cement) ko ruwan ciwo wani lokaci ma gauraye da baki-baki. To, irin wannan ruwan yana da hukunci dayan biyu ne:

1. Idan kin gashi ne a lokacin da kike Haila ko a karshen Haila amma hade da Hailar to, hukuncin shi hukuncin jinin Haila ne, kamar yadda ya tabbata a Hadisin Nana Aisha (RA).

2. Idan kin gan shi ne a cikin tsarki lokacin da baki Haila to, hukuncinsa, hukuncin tsarki ne, kamar yadda ya tabbata a Hadisin Ummu Adiyyah (RA), za ki cigaba da Sallah, Azumi da sauran aiyukan na Ibada, duk abin da aka hana mai Haila bai shafe ki ba, sai dai duk lokacin da za ki yi Sallah sai kin yi tsarki kin sake Alwala har zuwa lokacin da wannan ruwan ya daina zuwa. Allah ya ba mu ikon ganewa da gyarawa.

Amsawa:-Mal. Ibrahim Jushi, Zamfara

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/I08Ƙc4ehEctLMSfks5awuZ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments