Ticker

6/recent/ticker-posts

Ni ce tun da Azumi ya wajaba a kaina ina yi. Sai dai kwanakin da nake haila ba na biyan su. To mene ne hukuncina?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam. Ni ce tun da Azumi ya wajaba a kaina ina yi. Sai dai kwanakin da nake haila ba na biyan su. To mene ne hukuncina?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

Amma abin akwai bakin cikin in wannan abin ya faru tsakanin matan muminai, to ita wannan alamun abubuwa biyu: ko don jahiIci, ko don wula kanta addini. Dukkansu biyu masifa ne. Amma dai shi jahilci, maganisa neman iIimi da kuma tambayar abin da ba ka sani ba. Amma sakaci maganinsa tsoron Allah (SWT) da kuma kiyaye dokokinSa da kuma jin tsoronSa. In mutum yana aikata wannan to, ya yi gaggawa zuwa ga nemam yardar Allah. Don haka shawara ga wannan mata dangane da wannan aiki, ta tuba ga Allah, sannan ta yi kirdado ta biya gwargwadon ikonta abin da ta sha. Da wannan ne za ta kubutar da kanta. Muna kuma roka mata Allah Ya karbi tubarta

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/I08Ƙc4ehEctLMSfks5awuZ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments