Ticker

6/recent/ticker-posts

Duk Wani Jinin Da Ya Zo Wa Mace Matukar Bai Zo Da Siffar Jinin Haila Ba, Ba Ya Karya Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam ina da tambaya ne mlm ina yin period kwana uku bana haura sama da haka to wannan lokacin Kuma bayan nagama Kuma na tabbatar da tsarkina Harma nadauki azumi sai sake ganin alamar daukewar jini irin wannan brown colour din to can Kuma Rana sai na ga jini ahade da wannan brown color din ya zo Kuma take ya dauke nidai sainayi sallah ta nacigaba da azumi na can Yama sai wani jinin me irin Jan Nan yasake zubowa nanma na yi tsarki na yi sallah daga Nan Kuma har aka Sha ruwa bai zo ba still nasake daukar azumi Nan ma saina sake ganin irin wannan nidai ban karya azumi naba Kuma na yi sallah har dare saiya zo saiya ɗauke Kuma bemin kala da irin period Dina ba sai Kuma the next day bai zo ba sai wannan alamar ta brown color tasake zuwa can ma Sai inji Abu yazubo Inna duba saina ga wannan brown color din to MLM meye hukuncin azumina zan rama biyar ne ko Kuma guda ukun zan rama?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To matukar dai kwanakin da kika saba yin hailar sun cika kuma kin samu tabbacin samun tsarki ta ɗaya daga cikin hanyoyin nan guba biyu da mata suke gane cewa sun samu tsarki Sannan kika yi wankan. To duk wani jinin da ya dawo matukar bai zo da siffar jinin haila ba ba zai karya miki azumin ba kuma ba za ki dena sallah ba. Sabida haka yanzu tunda kince beyi kamannin jinin hailar ba kinga ke nan ba jinin haila bane tunda ya canza daga asalin jinin haila to azumin yana nan in Shã Allahu kuma sallolin suma sun yi in Shã Allahu. Amma da a ce kinga jinin ya yi siffa da jinin haila misali kamar kalarsa, karninsa kaurinsa dasauransu to shi ma za ki daukeshi a matsayin haila ne ke nan azumin ya lalace sannan za ki dakata da ibada har sai ya sake yankewa

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/LsA4LWfGSme0umoxks5785

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments