Ticker

6/recent/ticker-posts

Kabilu a Tunanin Bahaushe: Duba Cikin Labaran Barkwanci

Cite this article: Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2022). Ƙabilu a Tunanin Bahaushe: Duba Cikin Labaran Barkwanci. In Sarcouncil Journal of Humanities and Cultural Studies 1.1, pp 27-32. ISSN (Online): 2945-3658 DOI:  https://zenodo.org/record/6418660. Accessible at: https://secureservercdn.net/160.153.138.177/16g.514.myftpupload.com/wp-content/uploads/2022/04/SJHCS-6-27-32.pdf.

Zamantakewa

Ƙabilu a Tunanin Bahaushe: Duba Cikin Labaran Barkwanci

Adamu Rabi’u Bakura1
Abu-UbaidaSani2
1&2 Department of Languages and Cultures, FederaL University, Gusau, Nigeria

 Tsakure

Manufar wannan maƙala ita ce nazartar nau’ukan labaran da ke yawo a bakunan Hausawa game da ƙabilun da ke hulɗayya tare da su. An zaɓi biyar daga cikin ƙabilun a matsayin samfurin wannan bincike. An bi manyan hanyoyi biyu domin tattara bayanan binciken. Na farko shi ne tattarawa da taƙaita tarihin haɗuwar Hausawa da ƙabilun da aka zaɓa cikin samfurin binciken. Na biyu kuwa shi ne nazarin fitattun labarai game da waɗannan ƙabilu. An ɗora aikin a kan tunanin Bahaushe na “da wayo ake faɗa wa wawa gaskiya.” Binciken ya gano cewa, bayan kasancewar waɗannan labarai abinci ga adabi, suna kuma da amfani ta fuskar faɗakarwa da nishaɗantarwa. A bisa haka ne takardar ta ba da shawarar samar da kwas na musamman game da barkwanci tare da inganta shi domin cin gajiyar hikimomi da damarmaki da ke tattare da wannan ɓangare na adabi tare da kauce wa ƙalubalen da ke ƙunshe cikinsa.

Fitilun Kalmomi: Barkwanci, Labarai, Fulani, Buzaye, Nupawa, Yarbawa, Inyamurai

1.0 Gabatarwa

Mafi yawan Hausawa Musulmai ne. Yawancin suna gudanar da rayuwarsu ne a kan tafarkin da addinin ya shimfiɗa. Duk da haka akan ci karo da ɗan abin da ba a rasa ba da ya jiɓinci al’adunsu na aure da haihuwa da mutuwa. Yawancin ire-iren waɗannan al’adu sun gaje su ne tun kaka da kakanni, kuma addinin Musulunci ya yi kawaici game da su. Wato bai hana ba. Ta fuskar mu’amala da iyaye ko dangi ko abokai ko shugabanni ko maƙwabta ko wanin waɗannan, yawanci ana gudanar da su ne kamar yadda addini ya tanada.

Sakamakon irin tasirin da addinin Musulunci ya yi a rayuwar Bahaushe Musulmi, shi ya wanzar da zaman lumana a tsakaninsa da sauran jinsin ƙabilu da zaman tare ya haɗa su. Sakamakon wannan zama ne, har Bahaushe ya sami damar fahimtar halayen ƙabilun, musamman na wauta, son abin duniya, rowa, ƙazanta da sauransu. Fahimtar ire-iren waɗannan halayyen mutane shi ya bayar da damar samar da labarai da suka dace da halayensu. Bahaushe ya riƙa bayar da waɗannan labarai da niyyar tsokana don a yi dariya. Ana iya samun ƙarin gishiri kan haƙiƙanin yadda al’amarin yake. Wannan bincike ya nazarci ire-iren waɗannan labarai domin sharhin waɗansu darrusa da ake iya tsinta daga cikinsu.

1.1 Dabarun Gudanar Da Bincike

Farfajiyar wannan bincike ta taƙaita ga cuɗanyar Hausawa da al’ummomin da suka kasance cikin samfurin binciken. Al’ummomin da aka ɗauka a matsayin samfuri sun kasance Fulani da Buzaye da Nupawa da Yarbawa da Inyamurai. An yi la’akari da kusanci da daɗaɗɗiyar cuɗanya da ke tsakanin Hausawa da waɗannan ƙabilu yayin ɗaukar samfurin.

Binciken yana ɗauke da nau’ukan bayanai guda biyu. Na farko tarihi ne da ya shafi cuɗanyar Hausawa da waɗansu ƙabilu. An bi hanyar nazartar rubuce-rubucen da ke tattare da waɗannan tarihai domin fitar da yadda abin yake a taƙaice.  Nau’in bayani na biyu shi ne labaran da Hausawa ke bayarwa game da ƙabilun. An zaɓi labari guda fitacce game da kowace ƙabila da ke cikin farfajiyar binciken. Abubuwa biyu da aka yi la’akari da su wajen zaɓen labaren su ne (i) daɗewar labari, da (ii) yaɗuwar labari tsakanin Hausawa (sanuwarsa).

Kasancewar binciken bai fita daga cikin farfajiyar fahimtar Bahauhe ba, an ɗora shi kan tunanin Bahaushe na: “Da wasa ake faɗa wa wawa gaskiya.” Ko da ma dai, waɗansu daga cikin labaran barkwancin Hausawa faɗakarwa ake yi a fakaice. A bisa wannan fahimta, binciken na da hasashen cewa, labaran barkwanci da ake shiryawa game da halayen mutane na mazaunin hannunka-mai-sanda. Yana iya faɗakarwa da ankararwa domin guje wa munanan halayyar mutanen da aka kawo cikin labaran. Yana kuma iya kasancewa faɗakarwa ga su kansu waɗanda abin ya shafa.

2.0 Kallon Da Bahaushe Ke Yi Wa Waninsa

Ana iya kallon kalmar Hausa a matsayin suna na harshe. Masu wannan harshe su ake kira Hausawa. Al’ummar Hausawa ba su ɗauki kansu ƙabila ba, don kuwa a gurinsu duk wanda ba Bahaushe ba shi ne ƙabila, ko kuma bagware. Wato tamkar dai yadda Larabawa suka ɗauki duk wanda ba Balarabe ba a matsayin Ba’ajame (Baubawa). Masana da dama sun bayyana ƙabila a matsayin: “Al’umma ce mai asali ɗaya da yare ɗaya da kamannu (ƙirar jiki) kusan ɗaya da al’adun gargajiya iri ɗaya da ra’ayin zaman duniya (falsafa) ɗaya, da sauran irinsu. Kuma lallai ne cikin wannan al’umma kowa yana da’awar shi ɗan ƙabilar ne (Kwakwachi, 2010).[1]

A ɓangare guda kuwa, akwai masu ganin bai kamata a kira Hausawa da suna ƙabila ba, sai dai a ce, su taro ne na al’ummomi daban-daban da suka cuɗanya da juna, kuma suka taru suna magana da harshe ɗaya. Ita kanta kalmar Hausa a wurin Bahaushe tana nufin harshe. Saboda akan ji ya ce: “Ban ji wannan Hausar ba. Wato bai gane wannan yare ke nan ba. Ko kuma ya ce: “Ya ji wata Hausa.” Wato ya ji ana magana da wani harshe, ko gwalangwanto. Sau da yawa akan sami haifaffen ƙasar Hausa, a tambaye shi ƙabilarsa, zai ce shi Bafillace ne ko Babarbare ko Banufe, amma bai san ko zo-in-kashe ka ba cikin harshen da ya ambata. Haka ana samun wasu jinsin mutane zaune tare da wasu ƙabilun da ba sa jin Hausa, amma duk da haka suna da’awar su Hausawa ne. Misalan waɗannan sun haɗa da Abakwa Riga na Wukari da Takum na Lafiya. Wannan kan faru ne a sakamakon cuɗanya da auratayya.

Bahaushe ya ƙaga labarai da dama game da ƙabilu daban-daban. Bincike ya tabbatar da cewa, waɗansu daga cikin ire-iren labaran an samo su ne daga abubuwan da suka faru a zahiri. Daga ciki kuwa akwai waɗanda ‘yan ƙabilun suka aikata bisa ƙarancin ilimi ko ƙauyanci ko suɓutar baki. Ire-iren labaran nan akan yi musu ƙarin gishiri. Akan kuma samu abubuwan da waɗansu ƙabilu na daban suka aikata, amma sai a juya labaran a danganta su da waɗansu ƙabilun na daban. A ɓangare na uku kuwa, akan ƙagi labarin da kwata-kwata bai faru ba. A irin wannan yanayi, ana tsara labari na raha da ke nuna wata halayyar wauta ko ƙauyanci domin a danganta ga wata ƙabila. A bisa haka, labaran da za a ci karo da su game da ƙabilu na iya faɗawa cikin kaso ɗaya daga cikin waɗannan:

i.                    Labaran abubuwan da ƙabilun suka aikata a zahiri

ii.                  Labaran abubuwan da ƙabilun suka aikata waɗanda aka yi wa ƙarin gishiri

iii.                Labaran abubuwan da waɗansu ƙabilu na daban suka aikata, sai kuma aka danganta su da waɗansu ƙabilun na daban

iv.                Ƙirƙirarrun labarai da ba a aikata su a zahiri ba

2.1 Ƙagaggen Labari Game Da Fulani

Fulani, mutanen Fula ne. Suna zaune a ƙasashe kamar Mali da Senigal. Fulani nau’i biyu ne, Fulanin daji (Bararoji) da Fulanin Soro. Fulanin daji su ke kiwon shanu. Suna yawo daga wannan wuri zuwa wancan domin neman makiyaya da ruwan sha saboda dabbobinsu. Su kuwa Fulanin Soro rukuni-rukuni ne da suka haɗa da: Torankawa da Sulluɓawa da Jahunawa da sauransu. Ana kyautata zaton sun fara zuwa ƙasar Hausa zamanin Sarkin Kano Yakubu wanda ya yi mulki a tsakanin shekarar 1452-1463 (Ibrahim, 1970: 103). Fulanin daji a koyaushe suna cikin jeji. Babban abin da ke haɗa su da Hausawa shi ne kasuwanci, wato cinikin mai da nono ko shanu da kuma sayen kanwa da gishiri da sauransu.

Fulanin Soro kuwa suna zaune cikin garuruwa suna karatu da karantarwa. Daga cikinsu ne aka sami Malam Musa Jakollo kakan Shehu Usman Ɗanfodiyo wanda ya zauna a Birnin Ƙonni da ke cikin ƙasar Gobir a wancan zamani (Ibrahim, 1970; T/Mafara, 1999). An sami muhimmiyar alaƙa tsakanin Hausawa da Fulani bayan kammala jahadin Shehu Usman Ɗanfodiyo, wanda ya yi sanadin mayar da ragamar mulkin ƙasar Hausa hannun Fulani har zuwa farkon ƙarni na ishirin lokacin da Turawa suka ƙwace mulki daga hannunsu. Irin wannan zama na masu riƙe da mulki da waɗanda aka ƙwace wa mulki, ya wanzar da kusanta ta ƙud-da-ƙud da hulɗa tsakanin Bahaushe da Bafillatani da ta haifar da raini a tsakaninsu. Kuma ita ta ba Bahaushe damar fahimtar halayen Bafillatani musamman wajen wauta da rashin wayewar kansa, har ma yake ganin sa a matsayin sakarai maras wayon zaman duniya.[2] A kan haka ne Bahaushe ya gina labarai don ya nuna wautar Bafillatani.

Akwai labari game da Bafillatani da ke cewa:

Wai wani Bafillatani ne ruwan sama ya dake shi, ga sanyi, ga dare ya yi. Sai ya zo ya sami mafaka. Ya tarar an hura wuta, ana gasa gyaɗa. Da gyaɗa ta gasu, aka ba Ɗanfulani. Bayan ya ci sai ya ce: “Mhm! Aka ce: “Yaya dai Ɗanfulani?” Sai ya ce: “Ai mu oya, wallahi ko lahira wuta muka zaɓa da kwandon gyaɗa.

Idan aka dubi wannan labarin da idon basira, za a ga cewa da farko labarin ya ƙunshi kwaikwayo. Akwai kuma wani abu da ke tabbatar da abin da ake kira santin furuci/magana. Wata ƙila ya ɗauki dogon lokaci bai ci abinci ba, wanda hakan ya sa har yunwa ta addabe shi. Yayin da ya ci abinci, sai waɗannan kalamai suka fito daga bakinsa ba zato ba tsammani a sakamakon galabaitar da ya yi.

Bincike bai tabbatar da aukuwar wannan al’amari ba. Duk da haka, abu ne mai yiwuwa. Tana kuma iya kasacewa ƙirƙira ce ta Bahaushe don ya bunƙasa adabinsa na baka, tare da samar da annashuwa da nuna wa na baya daɗaɗɗiyar dangantakar da ke tsakaninsa da Fulani. Ko kuma an ƙirƙiro ne don koyar da ladubban ƙasar Hausa na cin abinci. Ko ba komai, wannan labari ya fitar da tunani ko al’adar Bahaushe game da santi. Bayan haka, a kaikaice yana nuna raunin ilimi ko ƙauyanci Bafillace. Ko da ma dai, akwai barkwanci tsakanin Hausawa da Fulani.

2.2 Ƙagaggen Labari Game Da Buzaye

Azbinawa suna zaune tare da Bugaje (Buzaye) a bakin saharar Yashi, arewa da ƙasar Hausa. Buzaye kuwa asalinsu bayin Azbinawa ne (Ibrahim, 1970). Dukkansu suna Magana ne da harshe ɗaya. Suna da al’ada iri ɗaya. Suna ado da baƙaƙen tufafi. Sannan ba a raba su da naɗa rawani a kowane lokaci

Azbinawa da Buzaye sun fara cuɗanya da Hausawa tun kusan lokacin da aka kafa ƙasashen Hausa bakwai.[3] Kamar yadda Ibrahim, (1970) ya nazarta, an kawo cewa a shekarar da su Bagauda suka sara Kano tare da manya-manyan gonaki, kasancewar wurin sabo ga kuma taki mai yawa, sai Allah ya ba su amfanin gona mai yawa. Da shekara ta zagayo sai aka yi yunwa mai tsanani wadda ta shafi kusan dukkan sassan ƙasashen Hausa har ma da ƙasar Azbin. Wannan yunwa ta haifar da kwararar mutane zuwa Kano don su sami abinci. Cikin mutanen da suka yi ƙaura zuwa Kano har da Azbinawa da Buzaye.

Da aka sami ƙoshi da yalwar abinci a ko’ina, sai yawancin al’ummomin da suka zo Kano, suka koma ƙasashensu, amma su Buzaye sai suka ƙi bin Azbinawa suka yi zamansu a Kura ta ƙasar Kano (Ibrahim, 1970). Kasancewar Buzaye gwanayen ƙira da rinin baƙaƙen tufafi, sai suka duƙufa ga sana’arsu. Wannan ya sa ‘yan uwansu suka rinƙa zuwa Kano suna sayen baƙaƙen tufafi. Ta haka ciniki ya kankama har Hausawa suka tsunduma cikin safarar, suna kai hajar baƙaƙen tufafi ƙasar Azbin.

Babbar hanyar nan ta ciniki ta da, wadda ta tashi daga bakin kogin Bahar Rum ta ratsa ta hamadar yashi ta zarce zuwa ƙasashen Hausa, ita ta ƙara kawo cuɗanyar Hausawa da Buzaye. Dalili kuwa shi ne hanyar ta ratsa garin Azbinawa. An yi amfani da ita wajen fataucin bayi da wasu kayayyakin ƙasashen Turai zuwa ƙasar Hausa. An ci gaba da amfani da hanyar har bayan zuwan Turawa, musamman daga kudanci sahara zuwa ƙasashen Hausa, wajen cinikin gishirin da mangul da manda da kanwa da dabbobi. Madugai a wannan tafiya su ne Buzaye. Idan sun sayar da kayayyakinsu sai su sayi baƙaƙen tufafi da goro su tafi da su ƙasarsu.

Wannan daɗaɗɗiyar mu’amala tsakanin Hausawa da Azbinawa da Buzaye ta ba Bahaushe sararin fahimtar ɗabi’ar Buzu. Daga nan ne Bahaushe yake kwatanta Buzu a matsayin mai tsananin son kuɗi. Har kullum Bahaushe na misali da yadda matansu kan tafi suna bin mutane suna cewa: “Muna bara muna kitso muna karuwa.[4]

Ɗaya daga cikin labaran da Bahaushe ke bayarwa game da Buzu shi ne:

Wai wani Buzu ne mai sayar da kanwa ya kamu da ciwon ciki. Sai aka ce, a nemo kanwa a jiƙa masa. Buzun da ke kwance sai ya ce a je cikin kindinsa a saka sisin kwabo a ɗauko kanwar a jiƙa masa.

Idan aka kalli wannan labarin, za fahimci cewa ba wai an tsara shi ba ne don raha da annashawa kaɗai, har da ƙoƙarin nuna aibin matsolanci. Hakan na iya shafar lafiya da rayuwar matsolon shi kansa. Misali, idan da an yi biris da Buzun aka ƙi jiƙa masa kanwar, sakamakon rasa wanda zai sadaukar da sisin kobon da ya ce a saka kafin a ɗauko kanwar cikin kyandinsa, ciwon cikin na iya zama sanadin ajalinsa. Ko ba komai dai Bahaushe na cewa ruwa ba ya tsami banza. Ko da wannan abu bai faru ba a zahiri, ana iya hasashen cewa lura da matsolancin Buzu ne ya sa Bahaushe ƙirƙira wannan labarin.

2.3 Ƙagaggen Labari Game Da Nupawa

Ƙasar Nupe tana gefen Kogin Kwara da ke kan hanyar da Hausawa kan bi wajen zuwa fataucin goro a ƙasar Yarbawa. Hasali ma an sami mu’amalar cinikayya a tsakanin Nupawa da Hausawa. Hausawa kan sawo irin manyan rigunan nan da Nupawa ke ɗinkawa masu aiki da ake kira girken Nupe da kwakwata waɗanda suke da farin jini a wajen Hausawa, musamman attajirai da sarakuna. Haka ma ana fataucin kayan ƙarau da manja da suke samarwa. Irin waɗannan sana’o’i da Nupawa suka ƙware, sun wanzar da kyakkyawar mu’amala a tsakaninsu da Hausawa tun kafin zuwan Turawa (Tukur, 1978).

Sakamakon jahadin Shehu, an ƙara samun danƙon cuɗanyar Hausawa da Nupawa. Shi ne ma sanadin zamansu a ƙarƙashin daula ɗaya, domin mafi yawansu Musulmi ne. A dalilin wannan cuɗanyar har an sami ƙulluwar auratayya a tsakanin Nupawa da Hausawa. A daidai shekarar 1807-1833 Sarkin Katsina Ummarun Dallaje ya auri Banupiya wadda ta haifa masa ‘ya’ya kamar yadda Tukur, (1991) ya nuna. Ana kyautata zaton irin wannan dangantaka ta ɗan namiji da ɗan mace ita ta wanzar da samuwar labaran raha a tsakanin Hausawa da Nupawa. Misali, a tunanin Bahaushe, Banupe mutum ne mai maƙo. Wannan ya sa ya samar da labari game da shi kamar haka:

Wai Banupiya ce ta ɗora wa ɗandako kaya mai nauyi ya kai mata gida. Ya kai kayan da ƙyar. Da aka sauke, sai ta ce da shi ya shiga rumfarta. A cikin rumfar ya shiga ɗaki. A cikin ɗakin (uwar ɗakan) ya duba ƙarƙashin gado akwai tukunya. Cikin tukunyar akwai gwangwani, a cikinsa akwai ƙunshin leda ya ɗauko ya duba zai tarar da ƙullin tsumma. Ya kwance zai ga kwabo. Ya ɗauki ɗari ladan dakonsa. Ganin wannan wahalar da zai sake sha wajen neman haƙƙinsa na dakon, sai ɗandakon ya gwammace ya tafi ya bar kuɗin.

Idan muka dubi wannan labari za a fahimci an gina shi ne a kan fahimtar Bahaushe ta mutsiltsila da tsananin matsolancin Banufe. Irin wannan ɗabi’a kan sa alumma ƙaurace wa mai ita kamar yadda ɗandako ya bar ladan dakonsa ga Banupa. Gobe in ta haɗu da ɗandakon ba zai ɗauka mata kayanta ba. Bayan haka, duk wanda ya ji abin da ya auku gare shi, ba zai yi mata duk wani nau’in aiki ba, face sai sun yi tsada da ita ta kuma biya.

2.4 Ƙagaggen Labari Game Da Yarbawa

Ƙasar Yarbawa tana kudu maso yamma da Kogin Kwara. Cinikin goro shi ne farkon abin da ya haifar da cuɗanya tsakanin Hausawa da Yarbawa. Hausawa al’umma ce mai sha’awar cin goro. Matansu kuma suna cin hannun ruwa (goro mai yauƙi), wanda ba a samun su sai a ƙasar Yarbawa. Wannan ne ya sa Hausawa tafiya ƙasar Yarbawa domin fataucin goro a ƙasa da kuma kan jakuna. Sun kira waɗannan ƙasashe da suna “Gonja.” Wannan suna bai keɓanta a kan ƙasashen Yarbawa ba, har ya haɗa da ƙasashen Ghana, domin suna tafiya can wajen safarar goro.

Jahadin Shehu ya ƙara kawo cuɗanya tsakanin Hausawa da Yarbawa. Shi ne sanadin zaman ƙasar Ilori da wasu sassan ƙasashen Yarbawa a ƙarƙashin daula ɗaya tare da Hausawa (Ibrahim, 1970). Irin wannan zaman tare ya ci gaba da wanzuwa har zuwa kafuwar mulkin mallakar Turawan Ingila. Kafa mulkin mallaka ya ƙara haɗe ƙasashen Yarbawa suka kasance a ƙarƙashin ƙasa ɗaya da suna Nijeriya, wanda hakan ya ƙara haɓaka mu’amala tsakanin Hausawa da Yarbawa. Irin wannan shaƙuwa ta tsawon lokaci ta ba Bahaushe damar fahimtar halaye da ɗabi’un Yarbawa. Shi ya sa Bahaushe ke kallon Bayarbe da wasu halaye da suka danganci tsattsauran ra’ayi da tsumulmula game da kuɗi ko dukiya. Wannan ya ba Bahaushe damar tsara labari domin ya shammaci Bayarbe a kan halayensa da ya sani game da dukiya. Misali, akwai labari game da Bayarbe kamar haka:

Wai wani Bayarbe ne mai suna Baba Alabi, ya yi adashi tare da Hausawa. Sai Bahaushe ya karɓi kwasar farko. Ana cikin haka sai kwasa ta zo ga Baba Alabi. Da ya zo karɓar kuɗinsa, sai ya taras da wanda ya ɗauki kwasar farko ya mutu. Kowa ya ba shi zubi saura na mamaci. Sai aka gaya masa cewa, ya mutu. Daga nan Baba Alabi, ya ce: Kai! Wannan filan ni.” Wai a nan yana nufin bai tashi mutuwa ba sai da ya karɓi kuɗin mutane? Don haka shi bai yarda ba, tsara mutuwar ya yi.

Idan aka duba yanayin ƙunshiyar labarin, ana iya fahimtar yadda Bahaushe ke kallon falsafar Bayarabe game da lamarin rashin ɗaukar ƙaddara a kan abin da ya shafi dukiya, musamman kuɗi. Irin wannan lamarin ne ya sa Baba Alabi bai ma yi juyayin mutuwar abokin adashensa ba, ballantana ya yafe wani kaso daga cikin kuɗin. Wannan ya nuna a sarari cewa, ba mutuwar ta dame shi ba, hasarar da yake hangen zai yi ita ta dame shi.

2.5 Ƙagaggen Labari Game Da Inyamiri[5]

Zuwan Turawan Mulkin Mallaka da tabbatuwar kafuwar mulkinsu na ɗaya daga cikin sanadin cuɗanyar Hausawa da Inyamiri. Wani sanadiyyar cuɗanyar shi ne samuwar hanyoyin sufuri kamar titunan motoci da layin jirgin ƙasa da ya taso daga Legas ya zarce zuwa Kano. Yana da tsawon mil 704. An kammala shi a shekarar 1911. Ita ma hanyar jirgin ƙasa da ta taso daga Port Harcourt zuwa Kano mai tsawon mil 600 da aka sami kammalawa a 1926 ta taka muhimmiyar rawa wajen zama sinadarin haɗuwar Bahaushe da Inyamiri (Crowder, 1968). Hasali ma hanyoyin sun haɗa babbar cibiyar kasuwancin ƙasar Hausa da sauran sassan manyan garuruwan da ke cikin Nijeriya. Irin waɗannan hanyoyi sun taimaka matuƙa wajen cuɗanyar Hausawa da wasu ƙabilu, musamman ƙabilar Ibo da suka taso daga garuruwa kamar Legas da Inugu da Ibadan suka zauna a wurare kamar Kano da Zariya da Jos da Gusau da Sakkwato domin neman riba ta hanyar kasuwanci (Osaghae, 1994). Ta wannan mu’amala ce Bahaushe ya fahimci cewa, Ibo na matuƙar ƙyamar kuturu. Wannan ya sa ya ƙirƙiri labari kamar haka:

 Wai wani inyamiri ne yana tsaye bai san cewa wani kuturu mai zubar mugunya na tsaye a bayansa ba. Sai Inyamiri ya yi hamma ba tare da ya sa hannu ya rufe bakinsa ba. Ganin haka sai kuturu ya cusa dungun hannunsa a bakin Inyamiri, ya ce: “Shege, kafiri, ba salati ba rufe baki.” Sai Inyamiri ya rufe baki da dungun kuturu. Ba a ankara ba sai Inyamiri ya faɗi sumamme saboda tsananin ƙyama. Aka yayyafa masa ruwa.

Idan aka dubi wannan labara da idon basira, za a fahimci yadda Inyamiri ke tsananin nuna ƙyamarsa ga cutar kuturta, wanda hakan ne ya sa ba ya son ya sha innuwa ɗaya da kuturu. Ba Inyamiri kawai ke gudun kuturta da kuturu ba, har ma shari’ar Musulunci ta ja hankalin Musulmi game da mu’amala da mai ciyon kuturta. Wannan ne ya sa aka hana mai cutar ya jagoranci salla musamman idan tana zubar da miyaku, don gudun kada wasu su kamu da cutar. Ta fuskar adabi kuwa, an ƙara wa labarin gishiri ne domin samar da raha a tsakanin al’umma. Irin wannan rahar ce kan sa Inyamurai sake jikinsu tare da walwala a farfajiyar ƙasar Hausa, har suka kasance sun fi mu’amala da Hausawa fiye da sauran al’ummomin da ke zaune a ƙasar.

3.0 Sakamakon Bincike

Hausawa na cuɗanya da al’ummomi mabambanta. Mafiya kusanci da Hausawa su ne Fulani. Akwai dalilai da suka fara samar da hulɗayya tsakanin Hausawa da waɗannan ƙabilu. Misali akwai jahaɗin Shehu Ɗanfodiyo wanda ya mayar da mulkin garuruwan Hausawa da dama ƙarƙashin Fulani. Sauran hanyoyin sun haɗa da fatauci da kasuwanci da samuwar hanyoyin sufuri kamar hanyar jirgin ƙasa da ta haɗa Kano da garuruwan Inyamurai.

A ɓangare guda kuwa, Bahaushe ya gina labarai daban-daban da suka shafi waɗannan al’ummomi da yake cuɗanya da su. A dalilin raha da nishaɗi da barkwanci da waɗansu daga cikin labaran ke samarwa, sukan ƙara tabbatar da haɗin kai da taimakon juna tare da wanzar da dauwamammen zaman tare cikin annashawa tsakanin Bahaushe da waɗannan ƙabilu. Hakan kan ƙara danƙon zumunci da mutunta janu a duk inda aka haɗu. Ta fuskar mu’amalar kasuwanci kuwa, yana taimakawa a wajen samun rahusa da lamuni a tsakanin mai saye da mai sayarwa.

Yawanci labaran kan gudana ne a cikin hira yayin da aka haɗu. Hakan kan wanzar da abubuwa da suka ƙunshi: nishaɗi, kawar da damuwa, ɗebe kewa, sanya raha tare da shauƙin juna bayan an rabu. Haka kuma, labaran na koyar da abubuwa da dama da suka haɗa da: nasiha cikin nishaɗi, gargaɗi, tarbiyya, hannunka-mai-sanda, da sauransu. Duk waɗannan na kasancewa cikin raha da lumana, tamkar dai maganar Bahaushe na faɗa wa wawa gaskiya cikin wasa.

A gefe guda kuwa, labaran na ƙara bayyana falsafar Bahaushe ta son zaman lafiya da yadda yake sarrafa fasahar harshe da lugga wajen kwaikwayon yanayin lafuzzan wasu ƙabilu da zama ya haɗa shi da su. Bugu a ƙari, suna ƙara cusa alfahari da tinƙaho da kai, kishin zuci, kishin ƙasa, sanin ciwon kai da kuma fito d halayyar Bahaushe ta girmama baƙi da mutunta su tare da sakar musu fuska. Wanda hakan ya haifar da bayyanar martabarsa ta wajen son zaman lafiya da ƙulla kyakkyawar dangantaka a tsakaninsa da sauran al’ummomin da zaman tare ya haɗa su da shi.

Sau da dama waɗannan labarai na bayar da haske wajen taskace tarihin yanayin zamantakewar Hausawa da wasu al’ummomi. Hakan zai bayar da haske wajen kallon jiya da yau da kuma yadda ya dace a fuskanci gobe da jibi. Haka ma, labaran na wayar da kai tare da haɓaka ilimin dabarun zaman rayuwar duniya.

4.0 Kammalawa

Allah Ya yi wa ɗan Adam baiwa da basiri da tunani ta yadda zai iya ƙwanƙwance abubuwa ta kowace fuska ya same su. Wanna ne ya ba shi damar bayyana ra’ayinsa game da duk wani abu da yake kusa da shi. Ba Bahaushe ne kaɗai ke da wannan sifa ba. Kowace al’umma ma akwai yadda take kallon wata al’umma da zaman tare ya gama su, da yadda suka fahimci juna, fahimta mai kyau ko maras kyau ko da kuwa iyaye ne. A sakamakon haka ne aka kalato ire-iren labaran da Bahaushe ya ƙaga a kan al’ummomi daban-daban da suka haɗa da: Fulani da Buzaye da Nupawa da Yarbawa daga ƙarshe aka cika da Inyamurai (Ibo). Sai dai idan aka nazarci ire-iren waɗannan labaran barkwanci za a tarar akwai birbishin kishi a mafi yawansu. Bisa duk waɗannan, ya kamata a yi ƙoƙarin samar da darasi na musamman da za a koyar da barkwanci tsagoronsa. Yin haka shi ne zai ba da ƙwarin guiwar gudanar da bincike a kan yadda wasu al’ummomi suka gina nasu labaran barkwancin da ya shafi Hausawa da kuma wasu al’ummomi na daban. Yin haka zai ƙara ƙarfafa zaman lumana a tsakanin al’ummomin Nijeriya baki ɗaya.

Manazarta

Abdullahi, S.U. (1985). Gaskiya Dokin Ƙarfe. Kano: Mainasar Printing Press.

Adamu, M. (1978). The Hausa Facto in West African History. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Adamu, M.T. (1997). Asalin Hausawa Da Harshensu. Kano: Ɗansarkin Kura Publishing Limited.

Adamu, M.U. (2011). Sabon Tarihin Asalin Hausawa. Kaduna: Espee Printing & Advertising.

Afigbo, A. E. (1981). Ropes of Sand: Studies in Igbo History and Culture: Ibadan and Oxford: University Press.

Augi, A.R. (1977). “Tarihin Ƙasar Hausa Gabanin Mulkin Mallaka Na Turawa.” Muƙala, Makon Hausa, Jami’ar Bayero, Kano.

Bakura, A. R. (2013). Kishi A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensa, Kaduna: Garkuwa Media Services, No. 15, Lawal Abukur Road, Unguwar Dosa.

Galadiman Daji, A.N.U. (2008). Daular Fulani A Kano. Kano: Bechmark Publishers Ltd.

Ibrahim, M.S. (1978). “Are-Aren Kalmomi cikin Hausa” shafi na 94-116, Studies in Hau-Sa Language, Literature, and Culture. The International Conference. Kano: Jami’ar Bayero.

Kwakwachi, K.H. (2010). Asalin Hausawa, Harsashi Publishers Limited.

Lovejoy, P.E. (1980) Caravans of Kola: The Hausa Kola Trade 1700-1900, Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Olusanya, G.O. (1967). The Sabon Gari System in Northern States of Nigeria, Nigeria: Magazine.

Osaghae, E.E. (1994). Trend In Migrant Political Organization In Nigeria: The Ibo In Kano, IFRA, University Of Ibadan.

Talata Mafara, M.I. (1999). Daular Usmaniyya: Rayuwar Shehu Usman Ɗanfodiyo Da Gwagwarmayarsa, Zaria: Hudahuda Publishing Company Limited.

Trevallion, B.A.W. (1966). Metropolitan Kano: Report on the twenty-years Development Plant, 1963-1983. Greater Kano Planning Authority, Glesgou.

Tukur, A. (1991). Wasannin Barkwanci A Ƙasar Hausa, Kano: Rukhsa Publications. Wazirin Sakkwato, (B.SH.) Tarihin Fulani, Zaria: N.N.P.C.



[1] Wannan ra’ayi ya yi daidai da na Adamu, (19787) da Adamu, (1997) da Adamu, (2011).

[2] Yana da kyau a lura cewa, wannan takarda ba ta ɗauki matsaya ko ta yanke hukunci game da wayewa ko wautar wata al’umma ba. Hasali ma, abin da yake wayewa ga wata al’umma, yana iya kasance ƙauyanci ga wata al’ummar ta daban. Takardar ta mayar da hankali ne kawai kan nazartar labaran ƙauyanci da Bahaushe ya samar domin zolayar Bafillatani. Nazarin ya karkata kan fitar da ire-iren hikimomi da ke cikin labaran.

[3] Wato (1) Birom da (2) Daura da (3) Gobir da (4) Kano da (5) Katsina da (6) Rano da (7) Zazzau

[4] Wato a nan idan sadaka ta samu ko kitso to suna so. In kuma akwai mai buƙatar su a shirye suke. Ta la’akari da wannan ne ya sa Bahaushe ya tsara labari don ya nuna irin yadda yake kallon Buzu.

[5] Bahaushe na kiran duk wani ɗan ƙabilar Ibo da suna Inyamiri.

Post a Comment

0 Comments