𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan mace hailarta ta yanke kafin fitowar Alfijir amma ba ta yi wanka ba
sai bayan fitowar alfijir yaya azuminta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan mace jinin hailarta ta ya yanke kafin fitowar Alfijir ko da da minti
daya ne matukar ta tabbartar da jinin ya yanke da auduga ko da farin kyale to
azuminta bai ɓaci ba.
Don ta yi azumi ne lokacin da jininta ya ɗauke.
Koda yake ba ta yi wanka ba sai da Alfijir ya keto, to ba komai a kanta,
hakanan kuma da za ta wayi gari da janaba amma ba ta yi wanka ba Sai bayan
fitowar Alfijir to Azumin ya yi.
Da wannan ne na ke so na ja hankalin mata don wasun su sukan yi buɗe
baki bayan rana ta fadi amma ba su yi sallah ba sai jini ya zo musu suna gani
kamar ba su da wannan azumin.
Wannan magana tasu ba ta da asali tun da ta riga ta sha ruwa kuma rana ta
fadi, ko da minti ɗaya ne sai jini ya zo mata to babu abin
da ya shafi azuminta.
Allah ta'ala ya sa mu dace
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.