Ticker

6/recent/ticker-posts

Musan Hukunce-Hukuncen Fiƙhu [21] Hukuncin Sufra Da Kudra

Wannan yana daga cikin matsaloli masumutuƙar muhimanci, amma ga bayani a sauƙaƙe game da

hakan:

 Sufra na nufin: wani ruwa mai fatsi-fatsi kamar ruwanciwo, mai fitowa daga gaban mace.

 Kudra na nufin: Wani ruwa da yake fitowa daga gaban mace, kalarsa ta kasance tsakanin fatsi-fatsi dabaƙi, wato kamar ruwa gurbatacce,

DANGANE DA HUKUNCINSU KUWA

Idan ɗaya daga cikinsu ya kasance ya fitowa mace tana tsakiyar haila, ko kuma yana fitowa tare da hailarta, to wannan ana saka shi a cikin haila,

Idankuma bayan tsarki ne, to ba haila ba ne, saboda faɗin Ummu Adiyya (R.A) cewa:

 Mu mun kasance bama ƙirga sufra da kudra bayan tsarkia cikin haila.

[Abu Dawud ya rawaito shi]

A hadisin Nana A’isha (R.A) kuma

mata suna aiko mata da abinda sukesawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra (wato ruwanda yake kama da ruwan ciwo),

 Sai ta ce musu kada ku yi gaggawa har sai kunga farin ruwa ya fito, to a nan zamuyiamfani da hadisin Ummu Adiyya ne, bayan an sami tsarki,

Ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta ƙirgasu a cikin hailaba,

Hadisin Nana A’isha (R.A) kuma zamu yi amfani da shi idan tana

cikin haila ne, domin zatayi lissafi da sufra da kudra ɗin, tunda sun zo mata ne tana cikin hailarta.

Domin neman ƙarinbayani duba:

Dima'uddabi'iy a shafi na: 8

ALLAH shi ne mafi sani.

Duk mai neman ƙarin bayani ya tuntuɓemu ta private.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments