Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne hukuncin matar da ta yi zina da aurenta kuma a cikin watan Ramadan mai girma?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Meye hukuncin matar da ta yi zina da aurenta kuma a cikin watan Ramadan mai girma?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Zina Ko ba a watan Ramadan ba haramun ne ga namiji ko mace, matar aure, bazawara da budurwa, dukkansu haramun ne su aikata zina.

Hukuncin matar aure da ta yi zina a guraren da ake Shari'ah ta Musulunci shi ne; hukuncin kisa ta hanyar jefewa.

Duk macen da ta yi zina alhalin tana da aure haƙiƙa taci amanar mijinta, kuma ta tonawa 'yayanta da danginta asiri, saboda duk wani mutum kirki zai ƙyamaci auren 'yayanta don gudun gori daga bakunan mutane. Kuma ga babban cin mutuncin da ta yi wa mijinta wanda tabbas sai Allah ya bi ma sa haƙƙinsa a ranar alƙiyamah matuƙar be yafe mata ba.

Saboda haka se ta yawaita Istigfari wato neman gafarar Ubangiji da tuba zuwa gare Sa cikin nadama da ƙasƙantar da kai.

Sannan ta nemi yafiya a wajen mijinta cikin salo ba tare da ya gane abin da ta aikata ba.

Sannan kuma ta yawaita neman tsarin Allah daga Shaiɗan a duk lokacin da zuciyarta ta fara raya mata ta yi zina da wani. Domin Shaiɗan ne ya ke son tunzura ta zuwa ga halaka.

WALLAHU A'ALAM.

🏿Ayyoub Mouser Giwa.

08166650256.

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/ECƘsg2ycfS0FUI3fHfIdjƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments