Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Azumin Wanda Ba Ya Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam Barka da safiya. Malam don Allah meye matsayin Azumin Wanda baya Sallah kwata kwata, amma kuma zai ɗauki Azumi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Wanda ba ya sallah ba'a karɓar aikinsa na azumi ko zakkah ko hajji, ko duk wani aiki.

Imamul bukhari yaruwaito hadisi (520) daka buraida ya ce: Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce:( Duk wanda ya bar sallar la'asar hakika ya rusa aikinsa).

Ma'anar ya ɓata aikinsa shi ne ya rushe ba zai amfane shi ba, wannan hadisi yanuna wanda baya sallah ba'a karɓar aikinsa, wanda baya sallah ba zai amfana dakomai na aikinsa ba, aikinsa ba za a kaishi zuwa ga Allah ba.

Ibnul ƙayyeem rahimahullah ya ce: dangane da ma'anar wannan hadisin acikin littafinsa Assalah (65) " Abun da ya bayyana acikin hadisin, barin sallar iri biyu ne, barin sallah na har abada shi kwata kwata bayayi wannan yana ɓata aikinsa gaba ɗaya, da kuma barinta na wani lokaci kamar wuni guda sananne wannan yana ɓataa aikinsa na aiya wannan yinin, Barin sallah gaba ɗaya shike lalata aikinsa gaba ɗaya, barinta na wata rana yana ɓata aikin wannan ranar ko ranakun dabaya sallar.

An tambayi Shaik Usaimin acikin fatawarsa (87) game da hukuncin azumin wanda baya sallah. Sai ya amsa; Wanda baya sallah azuminsa ba ingantacce bane ba karbabbe bane, domin wanda baya sallah kafirine wanda ya yi ridda saboda faɗin Allah maɗaukakin sarki a Suratul Tauba aya ta 11:

 

فَإِنْ تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَإِخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ ۗ

Idan sun tuba sun tsai da sallah sun bada zakkah to sun zama 'yan'uwanku a'addini.

Da faɗin Annabi sallallahu Alaihi wasallam ( Banbanci da ke tsakanin musulmi dawanda bashiba shi ne yin sallah wanda ya bar sallah hakika ya kafirta) Turmuzi ( 2621) Albani ya inganta shi acikin sahihu turmuzi.

Saboda kuma shi ne maganar sahabbai gaba dayan imma baizama ijma'insu akaiba, Abdullahi bin shaƙeeƙ rahimahullah yana cikin tabi'ai wadanda suka shahara ya ce: Sahabbai sunkace ba sa ganin wani aiki cikin ayyuka wanda barinsa kafircine inba sallah ba, a bisa wannan idan mutum ya yi azumi kuma baya sallah to azuminsa anmayar masa ba za a karɓa masaba, kuma ba zai amfane shiba ranar alkiyama, zamuce da shi yi sallah sannan kayi azumi, amma kai azumi baka sallah azuminka ba karbabbe bane za a mayar maka saboda kafiri ba'a karɓar duk wata ibada tasa.

An tambayi malaman lajnatul da'imah (10/140) tambaya kamar haka: idan mutum yakanyi kwada yin yin azumi kuma yana sallah da azumi amma kuma dazarar azumi yawuce shikenan ya dena sallah, shin yana da azumi? Sai suka amsa: sallah rukunice daga cikin rukunan musulunci muhimmai wanda daka kalmar shahada sai ita, tana cikin farillai na tilas wajibi, duk wanda ya bar sallah yana maikore wajabcinta ko kuma saboda wula kantata ko saboda kasala hakika yakafirta, amma masu azumi suna sallah acikin azumi kawai waɗannan suna yaudarar Allah ne, tir da mutanen dabasu san Allah ba sai awatan azumin Ramadan, azuminsu bai ingantaba tare dabarin sallarsu alokacin da ba na azumi ba, sudin kafiraine kafirci babba, koda basu kore wajabcin sallar ba amafi inganci maganganun malamai.

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/ECƘsg2ycfS0FUI3fHfIdjƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments