An Ɗaura Aure Da Sunan Wata

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Ina son ayi mini bayani a kan wannan kuskure da ya faru , mutum aka wakilta shi ya zama waliyin ya yarinya za a daura mata aure sai aka zo yin sigar daure aure aka tambaye shi sunan yarinyar da yakewa walittaka maimakon a ce sunanta Fatima sai ya manta y ace Hadiza a haka aka daura auran da sunan Hadiza kuma Hadiza sunan kanwarta ne uba daya uwa daban ba a gane wannan kuskure ba sai bayan an gama biki amarya ta tare a gidan mijinta da kwana uku. Dan Allah ya matsayin wannan ɗaurin aure?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Toh asali dai abun da Annabi (s.a.w) yace kowanne aiki yana tafiyane tareda niyyarsa, dan haka tunda wannan suma taronda sukayi sunsani cewa sun tarune domin su ɗaura auren fatimar toh duk sunanda aka ambata wannan bashida wani matsala tunda dai su sunsan ga wacce suke ɗaurama aure toh ita ɗin suka ɗauramawa. Kuma ko da aka ambacin sunan waccan ɗin toh wadda aka ɗauka aka kaita gidan ango aikaga ita ce aka ɗaurama aure. Dan haka wannan kuskuren faɗin suna bashida wani damuwa domin bafa dole banema se ankama suna awajan ɗaura auren ana iya cewa ina neman auren ƴarka, shikuma seyace nabaka aidai kai kasan wacece ake nema nima kuma nasan wanake bayarwa. Dan haka yin kuskure a wajan ambaton suna wannan bashida wani tasiri.

    Allah ya sa mu dace

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/DVpHjgfRdK9IRWvkB23lbE

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.