Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsine Wa Talauci

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

 

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ina jin mutane sukan ce Allah ya tsine ma talauci, hakan da suke fada daidai ne???

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Toh wannan ba daidai bane, kuskurene babba domin yin hakan kamar mutum yana nuna fushine a kan ƙaddarar Allah, wanda kuma hakan ba al'ada ta musulmin ƙwarai bace domin shi musulmin kirki idan Allah ya jarrabeshi da wata ƙaddara wacce ransa bayaso toh komawa yakeyi ga Allah ta hanyar tuba da istigfari seya zargi kansa bawai yakama aibanta ƙaddarar Allah ba domin ƙaddarar ba ita ce takeda ikon sarrafa kantaba A'a Allah ne kuma zunubinmu yana janyo wasu abubuwan. Amma zagin Ƙaddara wannan munana ladabine ga Allah wanda kuma baya halasta ga musulmin ƙwarai.

Allah ya sa mu dace

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DVpHjgfRdK9IRWvkB23lbE

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments