Ticker

6/recent/ticker-posts

Har Ila Yau Akan Kisan Haneefa... Darussa Daga Abinda Ya Biyo Baya

Sace Haneefa Abubakar da garkuwa da ita da wani wanda ta amincewa ya yi daga baya ya ci amanarta ya raba ta da duniya abu ne na kaico, wayyo da kuma tir a wajen dukkan wani mai imani da tausayi.

Hanifa Abubakar

Har Ila Yau Akan Kisan Haneefa... Darussa Daga Abinda Ya Biyo Baya

Daga

gogi dabandaban dan cimma wata ɓoyayyiyar manufa tasu ni wani haske abin ya haska mun a cikin duhu har hakan ya sa na gano wani abin da zai iya amfanar al'umarmu baki ɗaya.

Yanzu dai al'amarin kisan gillar da aka yiwa yarinyar nan Haneefah Abubakar na nema ya zama tushen ɗora damban neman kuɗi, neman suna, neman mabiya da ma wasu abubuwan dabandaban.

Da farko dai akwai waɗanda bil haƙƙi da gaskiya suke baƙin cikin abin da ya salwantar da ran yarinyar nan maza da mata musamman iyaye masu ‘ya’ya kamarta.

Sai dai a ɗaya bangaren wasu gani suke wannan ɗaukan hankali da salon kashe ‘yar shekara 5 ɗinnan ya ɗauka kuma labarin ya karaɗa duniya dama ce ta samun baje kolinsu.

In kun tuna wasu ne suka fara fitowa a ƙungiyance wai zasu nemawa iyayenta tallafin kuɗi suka kuma bada asusun banki ga mutan gari a turo taimako. Iyayenta suka ce ba sa so.

Can sai wasu suka ce wai a ƙirƙiro wata gidauniya sabuwa da sunanta wai don taimakon yaran da suka afka cikin irin wannan ibtila'in da Haneefa ta faɗa.

Kwatsam sai muka ji wasu sun ce gwamnati ta tabbatar anyi wani abinda zai sa kar a manta da yarinyar ta hanyar sakewa dokar hana cin mutuncin yara suna Haneefa Bill.

Sai kuma raɗeraɗin cewa iyatenta na nan suna ta karb'ar miliyoyi daga masu zuwa ta'aziyya har kusan yanzu ma sun kuɗance inda suka fito suka ƙaryata wannan batu.

Duk dai a ƙoƙarin cin kasuwar ibtila'in da ya samu wannan baiwar Allaah wasu sun ce a sawa makarantar da yarinyar take zuwa inda aka binneta sunanta don tunawa da alhinin.

Wata jami'a ta yi hoɓɓasa irin nata na sawa sunan ɗaya daga titinan harabarta sunan wannan yarinya marigayiya Haneefa Abubakar Abdulsalam.

Daga baya-bayan nan kuma mun ji wasu ‘yan Kannywood zasu shirya wani sabon fim mai suna Haneefa wai don jan hankalin iyaye su dinga kula da ‘ya’yansu a fannin tsaro.

Banda fa gwamnatin Tarayya da ta Jiha, kanana da manyan ‘yan siyasa ga malamai a nasu bangaren duk suna ta ƙoƙarin nuna yadda jimamin abin ya taɓa su.

Masu fasaha da baiwar rubutu, mawaƙa, manazarta da dai sauransu duk suma sun tofa albarkacin bakinsu ta sigogi kalakala a dandaloli dabandaban kan batun wannan yarinya.

Akwai kuma ‘yan soshal midiya da suma ba sa sanya wajen yaɗa bayanai cikin gaggawa da hanzari don tara "Likes, Comments, Reactions" da dai sauransu ko da kuwa basu tabbatar da haƙiƙanin gaskiyar al'amari ba.

Dama ‘yan jarida da ba a ta tasu. Wasu na ƙoƙarin sanarwa duniya abinda ya faru kuma yake faruwa a kan lamarin a yayin da wasu ke fafutukan yiwa addinin Islama yarfe sanadiyar makashin yarinyar Musulmi ne.

Toh haka-haka dai. Amma da yawa cikin masu nazari da sharhi akan lamuran rayuwa sai tambaya suke wai shin me yasa irin wannan ya faru akan wannan ‘yar talika sai ka ce kanta farau?

Haneefa Abubakar dai ba a kanta aka fara irin wannan sata da garkuwa, a nemi fansa daga bisani a kashe su ba. Wasuma ƙananan yara mazansu da mata sai anyi musu fyaɗe tukunna.

Amma sai gashi kowa Haneefa! Haneefa! Kuma abin kullum sai ka ji wata sabuwa ta faso kai a dabarun ‘yan cin wannan kasuwar.

Wasu dai sun ce abin ya ta'allaƙa ne da irin rawar da hanyar sadarwar zamani wato intanet da kuma dandaloli sada zumuntan soshal midiya suka taka akai wato yadda sauƙin isar da saƙo yanzu ya zama.

Amma fa kafin hakan ta kasance sai da labarin kisan gillar Haneefa ya taɓa zukatan mutane tukunna. Irin cin amanar da aka yi mata da kuma kasancewarta maras haƙƙin kowa akanta ya sa da yawa an tausaya mata.

Sai darasin da ya kamata mu ‘yan Arewa mu ɗauka daga wannan tashin hankalin da mu ka gani.

Shin idan za mu dinga yiwa dukkan lamuran da suka shafemu irin wannan rubdugu kowa ya zama amsa amo wajen koje da jan hankali akai anya ba za mu ci nasara akan ɗaukacin korafe-korafenmu ba kuwa?

Abinda fa sauran ƙabilu abokan zamanmu a Ƙasar nan musamman ‘yan kudu maso yammaci da kudu maso gabashinmu suke yi ke nan a kan dukkan lamuran da ya shafe su. Taron dangi suke wa komai su zam amsa-kuwwa a kai har sai kowa ya ji.

Dole ne Arewa ta dauki wannan salo itama ta zam haka in har ana son a samu wani ci gaba mai dorewa a yankin. Muna kira ga mutanenmu da a duba da kyau a kuma nazarci wannan fahimta a kuma ɗauka.

Sai mun gamu a jiƙo na gaba.

Post a Comment

0 Comments