Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne "SO"?

Daga Tsangayar Mai Bazazzagiya... Darasi na farko a jerin darrusan ba da amsar tambayoyin Farfesa Ibrahim Malumfashi game da “SO.”

MENE NE SO?                 

Wannan ita ce tambayar farko da malaminmu Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi mana a cikin aji.

AMSA

Sosuwar zuciya na shauk'in kusantar ko mallakar wani da ido ya gani, ko kunne ya ji labari ko hannu ya taba, har zuciya ta sakankanci da shi ko ita, da nufin biyan wata bukata na takaitace ko yalwataccen lokaci da nufin biyan bukata mai kyau ko akasin haka, wannan yanayin kawa-zucin da zuciya ta shiga, shi ne so.

A INA SO YAKE?

So dabi'a ne wanda ya kebu ga falalen zuciyar: Mutum da dabba da kwari.

YA YA KAMANCEN SO YAKE?

So ya yi kama da kishin ruwa ko yunwa. Ba a ganin k'ishi sai dai a ji makogwaro ya bushe. Da zarar mak'ogwaro ya harbu da k'ishin ruwa, idan ido ya ga ruwa, sai shauk'in son shan ruwa ya zo ga mak'ogwaro. Makogwaro ba zai sami salama ba, sai ya kwankwadi ruwa.

Idan mutum ya sha ruwa fiye da kima, yana iya halakar da shi ko ya shak'e ya amayar da shi. Idan mutum ya sha ruwa daidai gwargwado, sai ya amfanar da jikinsa.

Kamar yadda ba a ganin k'ishi, shi ma so ba a ganin sa. Amma idan zuciyar mutum ta kamu da son wani ko wata, tsigar zuciya kan tashi mutum ya rasa sukuni. Tsigar ba za ta sami salama ba, sai bukatarta ta biya.

Idan mutum ya nutsa a zuzzurfan kogin so, yana iya halaka shi ko ya raunata shi. Amma idan mutum ya yi kurme a gefen kogin so, sai ya fita lami lafiya.

Wannan shi ne kamanceceniyar SO da K'ishi.

Ke nan idan akwai k'ishi, to akwai so.

RABE-RABEN SO

So ya kasu zuwa gida da yawa. Daga ciki akwai:

1. Son da Allah ke yi wa bayinsa

2. So na bautaka

3. So na jagorantaka

4. So na burgantaka

5. So na jinintaka

6. So na abokantaka

7. So na dabbantaka

8. So na tsirantaka

9. So na abuntaka

10. So na yanayinta

11. So na sana'antaka

12. So na gamontaka

A duk wadannan nau'o'i na so, a so na gamontaka ne kawai ake samun cikakkiyar soyayya.

So na gamontaka shi ne son da namiji kan yi wa mace. Ko son da namiji kan yi wa namiji ko son da mace kan yi wa mace, da nufin gama jiki.

KAIFIN SO NA GAMONTAKA

1. Lamin so

2. Matsakaicin so

3. Matsanancin so

4. Sakakken so

MABUƊAN KAMUWA DA SO NA GAMONTAKA

1. Gani

2. Jin magana

3. Jin labari

4. Taɓawa

MATAKAN SO NA GAMONTAKA

 

1. Mataki na 1. So kan mamaye kaso daya a cikin hudu na zuciyar wanda ya kamu da son wani ko wata. Wannan shi ne lamin so.

2. Mataki na biyu: So kan mamaye kaso biyu na zuciyar wanda ya kamu da so. Wannan shi ne matsakaicin so

3. Mataki na 3: So kan mamaye kaso uku na zuciya na wanda ya kamu da so. Wannan shi ne matsanancin so.

4. Mataki na 4: A wannan matakin so kan mamaye daukacin zuciyar wanda ya kamu da son wani ko wata. Wannan shi ne sallamammen so.

MANAZARTA:

1. Bello S. (1973) Dausayin Soyayya. NNPC Zariya.

Sulaiman S.M. (2010) Asiran Mallake Miji 99. Amina Gifted Publishers

2. Sulaiman S.M. Mizanin Tantancewa Tsakanin Fara da Bak'ar Soyayya. ( Ba a buga shi ba)

TSOKACI:

Darasi na gaba za mu amsa tambaya ta 2

'Mece ce Soyayya? In sha Allah.

Malam Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya

soyayya

Post a Comment

0 Comments