Daga taskar Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau.
HAMSHAƘIN MALAMI SHEHU ADIBI NA GUSAU
(PROF. SA'IDU
MUHAMMAD GUSAU)
Jagora: Hamshaƙin Malami,
: Shehu Adibi Na Gusau.
Jagora: Mashahurin Malami,
: Shehu Adibi Na Gusau.
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau,
: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau.
G/waƙa: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Allahu Abin yabo,
: Taimake ni nayo yabo,
: Za na waƙe abin yabo,
: Malami gwiwar rabo,
: In zubo shi tsubo-tsubo,
: Yadda nai katarin yabo,
: Yabo na adibi na Gusauuuu..,
: Na Gusau,
: Adibi Na Gusau.
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Ɗan Muhammadu,
: Jikan Muhammadu,
: Uban Muhammadu na Gusau,
: Wani ya zama Malami,
: A kira shi da Malami,
: Daga sani yake Malami,
: Wani ya zama Malami,
: Daga kama yake Malami,
: Wani an ce Malami,
: A furuci yake Malami,
: A kira wani Malami,
: A suna yake Malami,
: Ya abin nan yake ne,
: Ya abin nan yake ne,
: Ku tattaho mu tafi Gusau,
: Waiwayo mu tafi Gusau.
Jagora: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Jikan Muhammadu,
: Uban Muhammadu,
: Ɗan Muhammadu Na Gusau,
: In an zama Malami,
: Da sani a kai ilimi,
: In an zama Malami,
: Da sani a kai ilimi,
: Babu aiki da sani,
: Da nuƙusani a Malami,
: Wanda yazzama Malami,
: Daga kama yake Malami,
: Babu aiki aikace,
: An ci amanar Malami,
: Ya abinnan yake ne,
: Ɗan Muhammadu na Gusau,
: Shehu Adibi Na Gusau,
: Karimin Malami,
: Majitahidin Malami.
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi Na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Kantarar ga masani,
: Yana ta aiki da sani,
: Sai Sa'idu Na Gusau,
: Na hango kuma Malami,
: Ya yi kama da Malami,
: Sa'idu Na Gusau,
: Ka isko Malami,
: Yana bayanin ilimi,
: Sai Sa'idu Na Gusau,
: Shehu karimin Malami,
: Na kira mutafannani,
: Adimi Na Gusau.
Jagora: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
: Kiɗa da Busa
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Inda gadon ilimi,
: Shehu Muhammadu Na Gusau,
: Salsalatai ta isa,
: Shehu Muhammadu Na Gusau,
: Ɗan Muhammadu ɗan kullum,
: Shehu Sa'idu Na Gusau,
'Y/amshi: 2 : In ado ne ilimi,
: Kama da Sarki Na Gusau,
: Don Sa'idu Na Gusau,
: Yana da tsafta ta isa.
Jagora: Idan ado ne aka so,
: Da shi a gane ilimi,
: To ku daina tasarrafi,
: Ado na harshe aka so.
'Y/amshi: 2 : Gangaran ya fi gwani,
: Shehu faƙilin wasali,
: Shi Sa'idu Na Gusau,
: Yana da faɗin ilimi.
Jagora: Baharu gun Na Gusau,
: Da furu'a Na Gusau,
: Da su lugga Na Gusau,
: Manɗaƙi gun Na Gusau,
: Da sarfa Na Gusau,
: Da shari'a Na Gusau,
: Da Hadisai Na Gusau,
: Da Haruf gun Na Gusau,
: Gangaran na saman gwani,
: Ga Ƙur'ani wajen Gusau,
: Mutafannuniiiiiiiiiiiiiiiiii
: Mutafannuniiii
: Adibi Na Gusau,
: Shehu karimin Malami.
Jagora: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Dakata ka ji salsala,
: Ta Sa'idu Mamman Na Gusau,
: Salsala daga Malamai,
: Ya zo wa sarauta Na Gusau,
: Jinin Muhammadu Ɗan Kulum,
'Y/amshi: Malam Sa'idu Na Gusau.
Jagora: Malam Muhammadu Ɗan Kulum,
'Y/amshi: Malam Buhari Kakan Gusau
Jagora: Shi ko Buhari dogo ya zamto
'Y/amshi: Ɗa ga Tukur mutafannuni
Jagora: Shi kwa Tukur ɗan Amma ne
'Y/amshi: Mai Hani ɗa ga Usamatu
Jagora: Usamatu ɗan Haji Ummaru
'Y/amshi: Ummaru ɗa gun Mustafa
Jagora: Mustafa ɗan gun Zangi
'Y/amshi: Zangi ɗan Dawudu ne
Jagora: Dawudu ɗan Zangina ne,
: Zangina ɗan Zakariyya ne,
: Zakariyya ɗan Salihu,
: Salihu ɗan Ummaru ne,
: Kun ji zubin wasu Malamai,
: Basarake jinin Gusau,
: Kadimi Na Gusau,
: Salsala ta gurin Gusau.
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Kun ji dai nasabar uba,
: Na waiwayo nasabar uwa
'Y/amshi: A'isha Ummin Na Gusau.
Jagora: Uwargida Nana A'isha,
: A'isha Indo Malama.
'Y/amshi: Indo Ummin Na Gusau
Jagora: 'Yar Alƙali Muhammadu,
: Ɗan Idrisu abin yabo.
'Y/amshi: A'isha Ummin Na Gusau
Jagora: 'Yar Alƙali Muhammadu,
: Ɗan Idrisu abin yabo
'Y/amshi: Indo Ummin Na Gusau
Jagora: Idirisu abin yabo,
: 'Yar Attahiru sha yabo
'Y/amshi: A'isha Ummin Na Gusau
Jagora: Attahiru sha yabo,
: Ɗan Usmanu gidan yabo.
'Y/amshi: Indo Ummin Na Gusau
Jagora: Salsalar Indo uwargidan,
: Muhammadu Malami,
: Ɗan Kullum na gurin Gusau,
: Shehu fasihin Malami,
: Mujtahidi,
: Mujahidi,
: Karimi Na Gusau.
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Bari in ɗan muku tsakure,
: Kaɗan a taskar Na
Gusau,
: Ku ji kaɗan daga littafan,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau,
: Ya yi a kan shari'a Gusau,
: Ya yi na mazzahaba Gusau,
: Ya yi a kan Islamiya,
: Da bayyanar Islamiya,
: Ya yi na tarbiyya Gusau,
: Yai na Ibada abin yabo,
: Karimi Na Gusau,
: Diwani Na Gusau,
: Diwanin Waƙar Baka,
: Hanyar nazari na waƙar baka,
: Ya yi a kai Gusau,
: Gusau Ta Malam Sambo ma,
: Adabin Hausa A Sauƙaƙe,
: Makaɗa da Mawaƙan,
: Baka ya yi a kansu ma,
: Waƙoƙin Makka a ƙasar Hausa,
: Lamarin Gusau,
: Wasannin Yaran Gusau,
: Wasannin Yaran Gusau,
: Na Gusau,
: Shehu adibi Na Gusau,
: Malamiiiii
: Mutafannuniiii
: Jarumi,
: Hamshaƙin Malami.
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Hamshaƙin Malami,
: Shehu adibi na Gusau.
: Mashahurin Malami,
: Shehu adibi Na Gusau.
: Mashahurin Malami,
: Shehu Muhammadu Na Gusau,
: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi Na Gusau.
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
'Y/amshi: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
Jagora: Gangaran ka fi gwani,
: Shehu adibi Na Gusau,
: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
'Y/amshi: Mashahurin Malami,
: Sa'idu Muhammadu Na Gusau.
0 Comments
Rubuta tsokaci.