Ticker

6/recent/ticker-posts

Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai (2)

Habaici suka ce da ake yi kaikaice cikin wasu ɓoyayyun kalmomi na hikima masu ban sha’awa da ban dariya ga mai sauraro tare da cusa haushi da ban takaici da ɓata rai ga wanda ake wa. Habaici ba kai tsaye ake gane da wanda ake ba, sai wanda ya san abin da ke faruwa.

Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai (2)


NA

SHEHU HIRABRI
08143533314

 

Kayan Kiɗan Hausawa

BABI NA BIYU

TAƘAITACCEN TARIHIN RAYUWAR ALHAJI MUSA ƊANBA’U GIDAN BUWAI

2.0 Shimfiɗa

        A babin da ya gaba an yi bitar ayyukan da suka gabata tare da bayyana ƙudurin bincike. Shi kuma wannan babin za a yi bayanin tarihin rayuwar Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai. Tarihin zai ƙunshi haihuwarsa da iliminsa da matansa da ‘ya’yansa da fara waƙarsa da makaɗansa da maroƙansa da nau’in waoƙoƙinsa da nasarorin da ya samu a cikin waƙa da yawace-yawacensa har zuwa rasuwarsa. Haka kuma za a bayyana dangantakarsa da sauran mawaƙa da kuma sauran al’umma baki ɗaya.

2.1 Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Musa Ɗanba’ub Gidan Buwai

2.1.1 Haihuwarsa

        An haifi Alhaji Musa Ɗanba’u a shekarar 1958 a shekarar da aka yi wata yunwa a ƙasar Hausa wadda ake kira muɗa. An haife shi ne a garin Gidan Buwai da ke cikin ƙaramar hukumar Mulkin Rabah ta jahar Sakkwato. Duk da yake wasu manazarta da suka yi rubutu a kan Alhaji Musa Ɗanba’u sun sha bamban dangane da shekarar da aka haife shi, Bala da wasu (1993) sun bayyana cewa, an haife shi a shekarar 1955. Shi kuma Shagari, (2011) ya bayyana an haifi Ɗanba’u a shekarar 1962.

          Ganin irin wannan bambanci ya sa na zage dantse domin samun tabbacin shekara da aka haife shi inda na yi tafiya har zuwa garin Illela inda wazirinsa mai suna Shehu waziri wanda a yanzu shi ne halifan Ɗanba’u domin shi ke waƙa tare da duk makaɗa da maroƙa da kuma kayan kiɗan da Alhaji Musa ya bari inda ni yi hira da shi da kuma wani makaɗin Ɗanba’u Adamu Tozai inda suka bayyana mini wannan shekara. Mun tattauna da su ne a ranar Lahadi 19-03-2017 a garin Illela inda ranar 20-03-2017 na ga littafin Sa’idu Muhammad Gusau mai suna Makaɗa da Mawaƙan Hausa na Biyu wanda aka buga a shekarar 2016 a ɗakin karatu na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo inda a shafi na goma sha ɗaya (11) ya tabbatar da an haifi Alhaji Musa Ɗanba’u a shekarar 1958, wanda wannan hujja ta tabbatar mana cewa an haifi Alhaji Musa Ɗanba’u a shekarar 1958.

2.1.2 Iliminsa

        A wajen ilimi, Alhaji Musa Ɗanba’u ya yi karatunsa na addini tun yana ƙaramin yaro a wajen kakansa, inda ya sauke Alƙur’ani mai girma kuma ya karanci littafai da dama kamar Ahalari da Ishmawi da Iziyya da Risala da Hadisai haka kuma kamar yadda Waziri Shehu da Adamu Tozai suka faɗa mini cewa ya hardace ishiriniya gaba ɗaya.

          A ilimin zamani kuwa, Alhaji Musa Ɗanba’u bai yi zurfi ba domin mahaifinsa ya sa shi firamare yana aji uku kakansa ya fitar da shi domin ya yi zurfi ga iliminsa na addini domin kakansa liman ne da ma ba su cika son boko ba.

2.1.3 Iyayensa

        Sunan mahaifin Musa Ɗanba’u Abdullahi Maiɗanjaki, wasu kuma na kiran sa Audu jikan Liman. Asalin kakan Ɗanba’u daga wani gari ne mai suna Kurgaba a ƙaramar hukumar Mulki ta Wurno ya taso ya komo Gidan Buwai.

          Abdullahi makaɗin goge ne amma haye ya yi domin bai gaji kiɗa daga iyayensa ba. Hasali ma, mahaifin Abdullahi, Liman Muhammadu, malami ne wanda ya kafa makarantar ilimi sannan ga shi liman. Shi kansa Abdullahi mahaifin Musa malami ne har kuma ya fara limanci sai ya daina ya ci gaba da kiɗan goge.

          Sunan mahaifiyarsa Aminatu (Amo ko Umma). Ita ma haifaffiyar Gidan Buwai ce, ita ma mahaifinta malam Musa malami ne. Ɗanba’u ya yi karatu wurinsa a nan ya hardace ishiriniya kamar yadda wazirinsa Shehu da makaɗinsa Adamu Tozai suka sheda mini.

2.1.4 Matansa

        Alhaji Musa Ɗanba’u ya yi aure a ranar 11 ga watan 10 na shekarar 1979 yana da mata uku kafin rasuwarsa waɗanda suka haɗa da:

1.     Hajiya Asabe

2.     Hajiya Sadiya

3.     Hajiya Aminatu

Bayan waɗannan matan uku, ya auri wasu uku amma sun rabu kafin rasuwarsa. Daga cikinsu akwai:

1.     Jumma

2.     Ta’Allah

3.     Asabe ƙarama

Jumma ita ce matarsa ta farko wadda ita ce mahaifiyar babbar ɗiyarsa Hauwa’u (Kulu).

Ta’Allah ita ce matarsa ta biyu. Ita ma sun haihu sun samu ɗa mai suna Zayyanu.

2.1.5 Yaransa

          Wazirin Alhaji Musa Ɗanba’u ya sheda min cewa, Alhaji Musa na da ‘ya’ya goma sha tara (19) da jikoki bakwai (7). Daga cikinsu akwai maza da mata.

Jumma Gidan Buwai

1.     Hauwa’u Kulu

Ta’Allah Gwaddodi

2.     Zayyanu

Hajiya Asabe Illela

3.     Ubaida

4.     Abdullahi

5.     Bashari

6.     Aminu

7.     Mas’udu

8.     Mustapha

Hajiya Sadiya Wurno

9.     Zara’u

10. Amina (Uwani)

11. Mas’uda

12. A’isha

13. Aliyu

14. Abubakar

15. Nana Firdausi

16. Maryam

Hajiya Aminatu Ƙauran Namoda

17.  Hadizatu

18.  Kabiru

Asabe Ƙarama Illela

19. Murjanatu

2.1.6 Fara Waƙarsa

          Wazirin Alhaji Musa Ɗanba’u Shehu Waziri ya sheda min cewa, Ɗanba’u ya fara waƙa shekara bakwai kafin kafuwar jam’iyoyin NPN da GNPP da UPN da kuma NPP. An kafa waɗannan jam’iyyun ne a shekarar 1978 (Birniwa, 1987) da Funtua (2003: 37). Kenan ya fara waƙa ne a shekarar 1972. Kuma ya fara ne da waƙoƙin kokawa. Daga ciki akwai waƙar Isiya Zakinsu Ɗanba’u ga yadda waƙar take:

Amshi: Isiya zakinsu Ɗanba’u

Kowaj ja da kai bai ji daɗi ba,

 

Jagora: Wahabu Allah ka kiyaye bayinka,

Yara: Wahabu Allah gyara gyararre

          Isya zakinsu Ɗanba’u

Kowaj ja da kai bai ji daɗi ba.

(Shagari, 2011; Gusau, 2014).

          Haka kuma akwai wata waƙar kokawa wadda wazirin Ɗanba’u ya rera min ya ce tana daga cikin waƙarsa ta farko waƙar ita ce:

Ya ci maza giyen Ɗanba’u,

Kadi maza suna saunatai.

 

Wannan ɗan bara ya kaka,

Ya ci tsakin miya yai ƙarhi.

 

To irin yanda ya taho maka Buba,

Buba ka faɗi rwahin gulbi,

Ga ‘yan yara na dwaga tai.

 

          Daga waƙar kokawa wazirinsa ya ce ya fara haɗawa da waƙar noma. Inda ya yi wata waƙa ta Abba na Ɗanladi. Ga yadda waƙar take:

Kana da noma,

Ɗan Aba na Ɗanladi.

Na ɗanguje,

Na Ɗanladi,

Na Akki mai aiki,

In dai ina da raina,

Sai kowa ya ji sunanmu.

Haka ko ya tabbata domin dun inda ake jin harshen Hausa an san Ɗanba’u daga nan ya ci gaba da waƙoƙinsa har zuwa shekara ta 1978 lokacin da siyasar jamhuriya ta biyu, inda aka samu jam’iyyun NPN da GNPP da UPN da kuma NPP inda wasu ‘yan jam’iyyar NPN suka buƙaci ya yi musu waƙar jam’iyyarsu ta NPN sai ya fara tunanin, shi da ke waƙar kokawa yaya zai yi waƙar siyasa? Daga ƙarshe ya yanke shawarar ya waƙe jam’iyyar. Daga cikin mutanen da suka buƙaci ya yi wa NPN waƙa sun haɗa da:

1.     Umaru Jikan Macca

2.     Arzika Maikujera Ciyan Party

3.     Wakili Buhari

Ga yadda waƙar take:

Amshi: Aminci ya fi kuɗi,

            Mu yarda da NPN

 

Jagora: in kag ga mutum kajin-kajin

            Kag ga mutum maƙal-maƙal,

            Ba rigar dala garai,

Yara:    Alhaji haske ne,

            Alhaji mai zamani,

            Allah magaba,

            Allah raba mu da ɗan kwakwa.

Amshi:  Aminci ya fi kuɗi,

              Mu yarda da NPN.

 

          Wannan waƙa da ya yi ta burge jama’a ƙwari da gaske. Daga nan sai ya kama harkar waƙar siyasa gadan-gadan har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

2.1.7 Yaransa Makaɗa da Maroƙa

        Lokacin da na yi hira da wazirin Ɗanba’u ya tabbatar min da cewa yana da yara goma sha ɗaya da maroƙa huɗu. Su goma sha biyar (15) kenan. Amma Mande direba ya riga shi rasuwa.

Yaransa

1.     Shehu Waziri Gidan Buwai

2.     Garba Ƙyamashi Gidan Buwai

3.     Muhammadu Bello Gidan Buwai

4.     Adamu Tozai Illela

5.     Muhammadu Ɗanmafara Gidan Buwai

6.     Muhammadu Nasiru Acida

7.     Baba Garba Tsaumawa/Jangebe

8.     Abdu Bagobir, Kadagiwa/Wurno

9.     Muhammadu Wandon Ƙarfe Gidan Buwai

10.  Mande Direba Acida

11.  Ɗanladi Dogo Illela

Maroƙansa

1.     Abdu Wakili Huci/Gwadabawa

2.     Muhammad Ɗanmaraya Kalmalo/Illela

3.     Zakari Ya’u Darma/Illela

4.     Muhammadu Nakogo Gidan Buwai

Waɗannan mutanen Wazirin Ɗanba’u da Adamu Tozai su sheda min cewa duk inda Ɗanba’u yake yana tare da su. Kuma shi ne cinsu da shansu, da suturarsu da su da iyalansu gaba ɗaya. Kuma daga cikinsu akwai masu mata biyu akwai masu mata uku. Kuma shi ke yi musu kowace lalura.

          Yanzu haka Wazirin Ɗanba’u ne halifan waƙa kuma duk yaransa da maroƙansa da kayan kiɗansa duk da su yake amfani wurin gudanar da waƙoƙinsa kamar yadda maigidansu ke yi. Yanzu haka suna nan suna waƙoƙinsu daga cikin waƙoƙin da waziri ya yi akwai waƙar Aminu Waziri Gwamnan Jihar Sakkwato da Waƙar Madawakin Daura Sanata Mustapha.

Waƙar Aminu Waziri

Amshi: Riƙa ƙwarai ka hi su sa’a,

          Sabon gwabna ɗan waziri,

          Aminu mai halin bajinta.

 

Jagora: Yara ku shirya za mu Sakkwato,

Yara: Don in iske Aminu gwamna.

Jagora: Yara ku kimtsa za mu Sakwkato,

Yar:   Don in iske Aminu gwamna.

 

Amshi: Riƙa ƙwarai ka hi su sa’a,

          Sabon gwabna ɗan Waziri,

          Aminu mai halin bajinta.

 

Jagora: Mun san Allah ad da mulki,

          Sannan shi ke ba da mulki,

          Inda ya so zai ba da mulki,

          Yau kai ne matawalle Sakkwato,

          Kai ne gwamnan Sakkwato

          Ɗauki halin da Aliyu ya yi.

Yara: Riƙe talakawanka da kyawo,

          Ka riƙe amana ɗan waziri.

 

A cikin wani ɗan waƙar yake cewa:

 

Jagora: Ga gwamna da mataimaki nai,

          Ga Ahmad Ali ga Aminu,

          Akwai wani ɗan saƙo gare ni,

          Kun san Ɗanba’u ya hurce,

To ku riƙe mu amana Allah,

          In kun riƙe mu kun yi daidai,

          In kun aje mu babu komai

Yara: Mu mun tsaya ga sarki Allah,

          Mun san Allah shi ka baiwa.

 

 

Waƙar Madawakin Daura Sanata Mustapha

Amshi: Maganin maza,

          Yaro ba ya hwaɗa ka wargi,

          Ɗan Abubakar,

          Sanata Mustafa madawaki.

 

A wani ɗan waƙa yake cewa:

Jagora: Ka ga halinta duniya,

          Wata rana a sha zuma,

          Wata rana a sha maɗaci,

          In yau anai da kai,

          Wata ran ba a yi da kai.

Yara: Ai ta bi ɗa mutum,

          Ba a ganai ba.

 

Amshi: Maganin maza,

          Yaro ba ya hwaɗa ka wargi,

          Ɗan Abubakar,

          Sanata Mustafa Madawaki

 

Jagora: Ɗanba’u ya wuce,

          Ga yaran da ya bari,

          Baba riƙe mu amana.

Yara: Sanata Mustafa Maigidana.

 

Jagora: Ɗan Audu riƙe mu da ƙima,

Yara: Sanata Mustafa maigidana

 

Jagora: Ɗan Garba riƙe mu amana,

Yara: Sanata Mustafa maigidana.

 

          Haka wazirin Ɗanba’u yake gudanar da waƙoƙinsa yana biyar zubi da tsarin waƙoƙin Ɗanba’u da kuma amfani da irin salailansa.

2.1.8 Nau’in Waƙoƙinsa

        Alhaji Musa Ɗanba’u ya shahara a fagen waƙa saboda haka ya zama hantsi leƙa gidan kowa. Don haka yana da waƙoƙi iri-iri kamar haka:

1.     Waƙoƙin kokawa

2.     Waƙoƙin noma

3.     Waƙoƙin siyasa

4.     Waƙoƙin sarauta

5.     Waƙoƙin masu mulki

6.     Waƙoƙin sauran jama’a

7.     Waƙoƙin yekuwa/faɗakarwa/gargaɗi

Haka kuma duk wata waƙa da aka buƙata a yi, Ɗanba’u na yin ta.

2.1.9 Yawace-yawacensa

          Shagari (2011) cewa ya yi, ya yi hira da Ɗanba’u inda yake cewa: “mawaƙin ya tabbatamin cewa ba ya iyakance wurare da ya tafi amma nan gida Nijeriya babu jihar da bai tafi ba. Haka kuma Nijar ma ya shige ta kamar Nijeriya. Wato babu jihar da bai shiga ba a cikin jamhuriyar Nijar. Sana’arsa ta waƙa da kiɗa ita ce ta kai shi jamhuriyar Nijar. Sannan kuma ya je Makka wajen aikinhajji da Umra ba sau ɗaya ba.

          Ni kuma hira da na yi da wazirin Ɗanba’u ya sheda min cewa, a Nijeriya jihar Barno (Maiduguri) can ne kaɗai ba su je ba. Domin sukan je cin rani a shekara ƙasashen kudu kamar Anaca da Benin da Okene da Wari da Legas da sauransu. A Nijar sun zagayi ciki da wajenta sunje Difa da Agadas da Zandar da Maraɗi da Tawa da Doso da Birni Bayero da Niamey da Tiliberi da sauransu.

 

2.1.10 Nasarorin da Ya Samu a Cikin Waƙa

        Waziri Ɗanba’u a hira da muka yi da shi ya sheda mini cewa duk wata nasara da ake samu a rayuwa Ɗana’u ya samu a cikin waƙa domin a cikinta yake ci, cikinta yake sha, a cikinta yake sutura, iyalansa da makaɗansa da maroƙansa da duk wani wanda ke ci ƙarƙashinsa duk waƙa ce. Haka kuma a cikin waƙa ya yi gida, ya yi wa yarana, motoci da kujerun Makka duk a dalilin waƙa ne.

          Wazirin Ɗanba’u Shehu da Adamu Tozai sun sheda min cewa, ko Ɗanba’u bai iya bayyana adadin motar da suka samu a dalilin waƙa wanda ya fara ba shi mota shi ne Abu Zahara ƙaura lokacin jam’iyar NPN a shekara ta 1978. Sannan sanata Ila Gada ya ba su Bus mai rubutun NPN, kuma ya samu mota ta ƙarshe bayan an bayyana sakamakon zaɓen gwamna na 2015 inda aka bayyana Aminu Waziri ya lashe zaɓe, sai gwamnan ya ba shi mota ƙirar honda mai suna Anaconda.

          Wanda ya fara ba shi kujerar Makka shi ne sanata Ɗanmalam Ila a Legas. Amma asalinsa ɗan jihar Kebbi ne. Haka kuma waziri Shehu ya faɗa min cewa ya samu lambar girmamawa a wurare kamar haka:

1.     Rima Rediyo Sakkwato

2.     Ƙungiyar ‘Yanjarida ta Jihar Sakkwato

3.     Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

Haka kuma shis ne Ambasadon mawaƙan Hausa na Nijeriya da Nijar.

2.1.11 Sha’awarsa

        Alhaji Musa Ɗanba’u mutum ne mai sha’awar wasanni. Hasali ma sha’awar wasanni shi ya sa ya fara waƙar kokawa kuma yana sha’awar wasar ƙwallon ƙafa kusan duk wanda ya san Ɗanba’u a Illela ya san yana sha’awar ƙwallon ƙafa musamman ta ƙasashen Turawa domin yana cikin riƙaƙƙun masu goyon bayan ƙungiyar Barcelona ta ƙasar Spain. Haka kuma yana sha’awar tafiye-tafiye. Ta ɓangaren abinci kuma Ɗanba’u bai da kamar tuwon dawa da hurar gero.

2.1.12 Rasuwarsa

          Kullu nafsin za’iƙatil mauti, duk mai rai mai ɗanɗana mutuwa ne. Allah ya yi wa Alhaji Musa Ɗanba’u rasuwa ranar talata 7-4-2015, jim kaɗan bayan bayyana sakamakon zaɓen 2015.

Babangida Kaka Dawa a cikin waƙarsa yana cewa:

Mutuwa mai yanke ƙauna,

Da duk kake son mutum,

Bai tsayawa in ta zaka.

 

Mutuwa mai ɗauke sheɗa,

Da duk kake ƙin mutum,

Ya mutu sai kai ka mutu.

 

 

Gindi: Murna mukai,

 Ka yi sarkin Musulmi,

 Muhammad Sa’adu,

 Ya gadi halifan Bubakar.

 

Allah ya jiƙan Alhaji Musa Ɗanba’u amin.

 

 

2.2 Dangantakarsa Da Sauran Mawaƙa

          Alhaji Musa Ɗanba’u kamar yadda na tattauna da mutane sun sheda min da cewa yana da kyakkyawar hulɗa tsakaninsa da sauran mawaƙa domin mutum ne da bai da hasada kuma duk inda haƙen mawaƙi ya kai zai bi don amsar masa haƙinsa. Haka kuma idan wani mutum ya yi wa wani mawaƙi alƙawali bai cika ba, Ɗanba’u yakan bi wannan mutumin har sai ya karɓo wa mawaƙin alƙawalin. Shi ya sa mawaƙa ke kiran sa Ambasadan mawaƙan Hausa Nijeriya da Nijar. Haka kuma sun faɗa min cewa, yana kyautata wa mawaƙa har ta kai karnan makaɗan Nijeriya da Nijar da sauran mawaƙa ke zuwa har gidan Ɗanba’u suna yi masa waƙa. Daga cikin mawaƙan akwai:

1.     Sani karen makaɗa Gwadabawa

2.     Shehu karen makaɗa kurya

3.     Makaɗa Dauro da dai sauransu.

Akwai lokacin da mawaƙa suke ƙorafi cewa idan aka je taro da an gabatar da Ɗanba’u to ba za a sake gabatar da wani mawaƙi ba, ko kuma duk wanda aka gabatar hikimar Ɗanba’u za ta dushe tashi ba a ganin ƙoƙarinsa. Da Ɗanba’u ya ji haka duk inda aka je taro yakan ce a bar shi ƙarshe.

          Game da kyautata wa mawaƙa ni kaina na sheda a lokacin da aka yi taron siyasa lokacin da shugban ƙasa Obasanjo ya zo Sakkwato a filin sukuwa, da idona na ga Ɗanba’u yana wa Gambo mai waƙar ɓarayi karin kuɗi naira ɗari-ɗari.

2.3 Dangantakarsa da Sauran Jama’a

        Dole makaɗi ya yi hulɗa da mutane musamman waɗanda yake shirya wa waƙa da kuma masoya masu ra’ayin waƙoƙinsa. Kuma yana waƙoƙin siyasa yana zuwa kamfe kuma yana hulɗa da saurakuna da masu mulki da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da sauran jama’a daban-daban.

          Wannan ya ba ni damar tattaunawa da wasu mutane da nake jin yana yawan ambaton su a cikin waƙoƙinsa da kuma wasu waɗanda ya yi wa waƙa da kuma sauran mutane da ke zaune wuri ɗaya da shi. Daga cikinsu akwai Alhaji Bala Musa Yabo da Sardaunan Hamma’ali Malami Maigandi da Muhammadu Galadima Horo (Ɗan’ige Horo) da Yusuf Bello Ɗancaɗi da Alhaji Audu na ƙofa (Sarkin baƙi) da Alhaji Hadi Ɗanmalam da Musa Damo da Alhaji Sanusi Ɗanwali da Alhaji Mani Sardaunan Illela da wasu daga cikin yaransa kamar waziri Shehu da Adamu Tozai da sauran mutane da dama. Sun faɗa min cewa Alhaji Musa Ɗanba’u mutum ne mai kyakkyawar hulɗa tsakaninsa da jama’a. Kuma mutum ne wanda ba shi da girman kai. Yana da yawan son wasa da mutane manya da yara kuma yana girmama mutane manya da yara.

          Wannan ni ma sheda ne domin mun haɗu da shi a gidan mai martaba Sarkin Musulmi Muhammdu Macciɗo a ranar da aka yi naɗin sarautun sarkin yamma da sarkin Arewa da Jarma da Katuka da Durumbun Sakkwato. Na je wurin Ɗanba’u muka gaisa kuma ya karɓe ni hannu bibiyu.

2.4 Naɗewa

        A taƙaice a cikin wannan babin an kawo bayanai kan taƙaitaccen tarihin makaɗin da ake nazari a kansa watau Alhaji Musa Ɗanba’u tun daga haihuwarsa da iliminsa da iyayensa da aurensa da matansa da ‘ya’yansa da yaransa makaɗa da maroƙa da nasarorin da ya samu da nau’o’in waƙarsa da yawace-yawacensa da abubuwan da yake sha’awa da dangantakarsa da ‘yan uwansa makaɗa da mawaƙa da kuma sauran jama’a. Kai! Har rasuwarsa.

Post a Comment

0 Comments