Ticker

6/recent/ticker-posts

Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Wakokin Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai (1)

Habaici suka ce da ake yi kaikaice cikin wasu ɓoyayyun kalmomi na hikima masu ban sha’awa da ban dariya ga mai sauraro tare da cusa haushi da ban takaici da ɓata rai ga wanda ake wa. Habaici ba kai tsaye ake gane da wanda ake ba, sai wanda ya san abin da ke faruwa.

Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai (1)

 

NA

SHEHU HIRABRI
08143533314

 

Kayan kida

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki ga kakannina Alkali Ahmadu Alkanci da ƙanensa Alkali Attahiru Maiwandon Ƙarfe, da fatan Allah ya jiƙansu da rahama, ya haskaka kabarinsu, ya sa aljanna ce makomarsu amin.

 

GODIYA

          Da sunan Allah mai Rahama mai jinƙai. Tsira da amincinsa su ƙara tabbata ga shugaban manzanni kuma cikamakon Annabawa, Annabi Muhammad (S.A.W.). Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki, wanda ya yi mini ni’ima ta lafiya da fahimta da nasarori, waɗanda su ne suka yi min jagoranci zuwa wannan matsayi na rubuta wannan kundi na neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

          Haka kuma ina godiya ga mahaifana Malam Shehu Alkali da Mahaifiyata Hajiya Hadizatu Ahmad (Dije) a kan tarbiyar da suka yi mini suka kuma aza ni bisa turbar ilimi tare da ba da kulawa ta musamman ga duk wani abin da zai kawo nasara da ci gaban rayuwata. Allah ya saka masu da mafificin alkhairinsa, sauran rayuwarsu Allah ya sanya albarka a cikinta, gobe ƙiyama ya sa su aljanna firdausi bi gairil hisabi amin. Ni kuma Allah ya hore min abin da ni kyautata masu.

          Ina godiya ƙwarai da gaske ga malamina da ke da alhakin duba wannan aikin bincike a kan kulawa da gudunmuwar da ya bayar ga samun nasarar kammala wannan bincike Farfesa A.B. Yahya Allah ya saka masa da alhairi ya sanya albarka ga dukan lamuransa.

          Haka kuma ina miƙa gagarumar godiya ta musamman da fatan alheri ga Malamina Dano Balarabe Bunza a kan gudummuwa da shawarwari da kulawar da ya ba ni ganin cewa aiki na ya tafi yadda ya kamata tare da samun nasara. Allah ya saka masa da mafificin alherinsa.

          Ina kuma miƙa godiya ta musamman ga shugaban sashe Farfesa A.A. Dumfawa da dukkanin malaman sashe musamman Malam Naziru Ibrahim Abas da Dr. Abdullahi S. Gulbi da Dr. Umar Aliyu Bunza da farfesa Haruna Abdullahi Birniwa da Farfesa Ibrahim Mokoshy Allah ya saka masu da mafificin alheri.

          Haka kuma ina godiya ta musamman ga kawona Tukur Ahmad da Abubakar Attahir da Aliyu Abdulƙadir da malam Usman yakanare da Murtla Moh’d yakanare a kan taimakona da suke yi a kowane lokaci da sharwarwari da suke ba ni ta hanyar da zan kammala karatuna cikin nasara.

          Ina godiya ta musamman ga yannena Bashir Malami da matarsa Umaima Bashir da Zara’u Shehu Alkali waɗanda su ke kan gaba dare da rana rani da kaka wajen ba ni tallafi ga harkar karatuna da sauran lamuran cigaban rayuwata. Allah ya saka masu da mafificin alherinsa. Haka kuma ina godiya ga uwargidana Hauwa’u Abubakar S. Baƙi Shinkafi a kan gudummuwa iri daban-daban da take ba ni, da ɗawainiyar da take yi ganin na samu nasara ga dukan al’amuran rayuwata Allah ya saka mata da alheri.Kuma ina godiya ga Bature Ibrahim (Ɓ.I.O) da Alhaji Aliyu Ibrahim Noway da Ahmad Midnight Star da Kabiru Oga Osusu da Hussaini Aina da Zayyanu Ibrahim (President) da Mansur Abubakar Aja’aya da Malam Mujittaba Abdullahi da Abubakar Usman Agame da hajiya Hadi Alkanci da Asma’u Tukur Attahir. Haka kuma ina godiya ga ƙannena musamman Mudassiru Buhari Hubbare da Mukhtar Abubakar Gidan Kanawa da Bashar Attahiru da Shamsu Shehu Alkali da Usamatu Abubakar Gidan Kanawa da Maryam Bello Aliyu (Mamu) da Asiya Mustapha da Rashida Shehu Alkali da Sadiya Ahmad Midnight da Marigayiya Hauwa’u Abubakar Gidan Kanawa da Usmanu Buhari Hubbare da Umar Dangi Allah ya saka masu da alheri.

          Haka kuma ina godiya ga masoya da abokan arziki musamman malam Aminu Abdullahi da ƙanensa Mukhtar Abdulahi Umar da matarsa Aisha a kan yadda suke kai da kawo ganin dukanin abin da zai kawo cigaba a rayuwata baki ɗaya. Allah ya saka masu da alheri. Haka kuma ina godiya da yabo da jinjina ga abokan karatuna Zaharadeen Abububakar Mainiyo da Malami Muhammad Yabo da Mansur Suleiman Gamji a kan yadda suka yi ɗawainiya da ni musamman zuwa na da dawowata daga makaranta da maigidana Ahmad G. Musa da Ɗalhatu Maigandi da Hassan Ahmad da Sirajo Hassan da Abu-Ubaida Sani da Bello Muhamamd da Nuhu Ibrahim Bayawa da Usman Aliyu Kangiwa da Marigayiya Fauziya Buhari, sai godiya ta musamman ga Mudassiru Rilwanu Alkanchi a kan tsayin daka da ya yi wurin gyara ciki da wajen wannan kundin bincike,  Allah ya saka masu da Mafificin alhairinsa.

          Daga ƙarshe ina godiya ga ɗiyana musamman Saudatu Garba da Balkisu Adam da Asma’u Bashir da Yusuf Bashir da Nafisa Shehu Natayo da Al’amin Bashir da Mufida Abubakar da Abdulshakur Bashir da Fahad Abubakar da Muhammad Yasir Bashir da Hauwa’u Bashir da Ahmad Muhammad Hirabri da Muhammad Bashir Bashir da Fatima Muhammad Hirabri da Attahiru Umar Ahmad. Allah ya saka masu da alherinsa.

 

 

BABI NA ƊAYA

GABATARWA

1.0  Shimfiɗa

Nazarin adabin Hausa wani teku ne mai matuƙar girma wanda masana suka kasa gida biyu, wato na baka da rubutacce; ko na gargajiya da na zamani. Masana da manazarta da ɗaliban ilimi da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da kowane fage. Ba fannin adabi kaɗai ba, har ma da sauran takwarorinsa wato ɓangaren harshe da al’ada. Da yake hikima tana da faɗi, sai wannan bincike ya ga akwai buƙatar ƙara fitowa da wani abu na adabi wanda ya danganci wata hikima da mawaƙa ke amfani da ita, amma wannan aiki zai keɓanta ne ga wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.

Da yake binciken ya shafi waƙar baka ne, sai wannan aiki ya ga ya dace a yi shimfiɗa kan ma’anar adabin Hausa wanda yake waƙa tana cikinsa ne tsundum. Saboda binciken ya samu wurin zama ma’ana abubuwan da za a tattauna su fito fili ga mai karatu.

Masana sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar kalmar adabi. Sai dai wani abin gwanin ban sha’awa a nan shi ne, duka ra’ayoyin suna da makusanciyar manufa da alaƙa ta ƙud-da-ƙud da junansu dangane da ma’anar.

Gusau, (2011:3) cewa ya yi: “Adabin Hausa, adabi ne wanda ya shafi hikimomi da sarrafa harshe da kuma hanyoyi waɗanda suka shafi tafiyar da rayuwa ta yau da akullum, kuma yakan zama mai yin darasi da hannunka-mai-sanda ko mai barbaɗa gishiri a rayuwa.”

Galadanci da wasu (2011: 27) cewa suka yi: “A Hausa ma’anar ‘adabi ta yaɗu i zuwa bayyana rayuwar al’umma ta fuskar al’adunsu, dabarunsu, harshensu, abincinsu, makwancinsu da dai duk sauran abubuwan da suka shafi rayuwarsu. Saboda haka muna iya cewa, ‘adabi’ shi ne nazarin rayuwar al’umma. Ta nazarin adabi za a iya sanin dabarun zaman duniya iri daban-daban.” A dunƙule dai adabi ya ƙunshi halayen rayuwar al’umma da ayyukan fasaha da al’adu da ɗabi’u da abinci da muhalli da waƙoƙi da wasanni da tarihi da makamantansu.

A taƙaice dai an yi wa wannan aiki tsarin gudanarwa na babi-babi domin sauƙaƙawa wajen fito da abubuwan buƙata bisa ga tafarki daidaitacce. Babi na ɗaya ya ƙunshi gabatarwa da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar cigaba da bincike da hanyoyi da muhali da muhimmancin da matsalolin bincike. A babi na biyu za a kawo tarihin rayuwar Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai tun daga haihuwarsa har zuwa rasuwarsa. A babi na uku za a kawo bayanai a kan zambo da rassansa tare da sharhin zambo a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u. A babi na huɗu za a kawo bayanai a kan habaici tun daga asalin kalmar har bayyana amfaninta tare da yin sharhi a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u. A babi na biyar za a kawo bayanin kammalawa tare da sakamakon bincike, sai manazarta da ratayen waƙoƙi su biyo baya.

1.1 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata

          A nazari da bincike irin wannan ya zama dole a yi waiwaye wanda Hausawa ke yi wa kirari da ‘adon tafiya’ na wasu ayyukan da suka gabata. Bincike ya nuna akwai aikace-aikace masu ɗimbin yawa da aka gudanar kan adabi a cikin kowane reshe na adabin Hausa, musamman waƙa. Amma ba a sami wani aiki da ya yi daidai da irin wannan aikin da aka sanya gaba ba, wato kan Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai. Ayyukan da wannan bincike ya nazarta sun haɗa da:

          Bello, (1976) a muƙalarsa mai taken: “Yabo da zuga da zambo a waƙoƙin sarauta.” Marubucin ya yi bayanin matsayin kiɗa da waƙa da yadda waƙa ke shiga cikin jinin ɗan Adam. Haka kuma ya kawo dangantakar makaɗan sarauta kuma, maƙalar ta bayyana abubuwa uku waɗanda suka haɗa da yabo da zuga da zambo, ya kawo ma’anoninsu da misalansu daga waƙoƙin da aka yi wa sarakuna. Daga nan sai ya naɗe aikinsa.

          Wannan aiki yana da nasaba da wannan bincike ta fuskar zambo. Sai dai maƙalar ta keɓanga ne kawai a waƙoƙin faɗa. Shi kuma wannan aikin bincike bai keɓance kowane ɓangare ba, yana magana ne a kan kowace irin waƙa amma ta Alhaji Musa Ɗanba’u.

          Safiya, (1984) ta rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello mai taken: “Habaici.” A cikin wannan aiki ta yi bayanin habaici da nau’o’insa da yadda ake amfani da shi. Wannan aiki ba ɗaya ne da nawa ba, sai dai habaici wani yanki ne a cikin nawa bincike domin za a fito da habaici a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u. Amma duk da haka aikin zai ba da gudummuwa ta hanyar samun nasarar wannan binciken.

          Yahya, (1985) ya rubuta takarda mai taken “Hikimar mawaƙa.” Wannan maƙalar ta haska min hanya da zan bi cikin hikima wajen nazarin gano hikimar da Ɗanba’u ke bi wajen gina zambo da habaici acikin waƙoƙinsa, amma ba ɗaya ce da nawa aikin bin cike ba.

          Mazawaje, (1985) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya mai taken: “Zambo da Habaici a Waƙar Fada.” Ya kasa aikinsa zuwa babi biyar. A babi na biyar ya tsunduma a cikin aikinsa inda ya kawo bambanci tsakanin zambo da habaici, sannan ya kawo zambo da habaici a tsakanin mawaƙan fada.

          Idan aka yi la’akari da wannan bincike za a ga yana da alaƙa da wannan aiki. Sai dai, shi yana magana ne a kan zambo da habaici a cikin waƙoƙin fada inda wannan bincike ya keɓanta ga makaɗi ɗaya kuma aka faɗaɗa aikin a kan kowace irin waƙa. Sai dai duk da haka ya ƙara share wa wannan aiki hanya domin samun nasarar wannan aikin bincike.

          Alkali, (1989) ya rubuta kundin neman digiri na biyu a Jami’ar Bayero, Kano mai taken: “Cuɗeɗeniyar Adabi: Tasirin Adabin Baka a Kan Rubutattun Waƙoƙin Hausawa Dangane da Habaici da Zambo Da Karin Magana.” Wannan aikin ya bambanta da nawa aikin bincike domin aikin ya duba cuɗeɗeniyar da ake samu tsakanin zambo da habaici a ƙarƙashin adabin baka da rubutacce. Shi kuwa wannan bincike zai yi nazari ne a kan zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u.

          Modibbo, (1989) ya rubuta kundin neman digiri na farko a jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo mai taken: “Nazari da Sharhi Kan Yabo da Zambo na Waƙoƙin Musa Ɗankwairo na Fada.” Wannan aikin ya yi nazari da sharhin yabo da zambo a cikin wasu waƙoƙin Ɗanƙwairo na fada tare da kawo misalai a cikin wasu ɗiyan waƙa. Wannan aiki ba ɗaya ne da nawa ba, domin ya yi nazari ne a kan yabo da zambo a cikin waƙoƙin fada na Musa Ɗanƙwairo. Inda nawa aikin zai yi nazarin ne a kan zambo da habaici a cikin kowace irin waƙa ta Musa Ɗanba’u. sai dai zai ƙara min haske wajen samun nasaran nawa aikin bincike.

          Waya, (1990) ya rubuta kundin neman digiri na farko a jami’ar Bayero, Kano mai taken: “Habaici, Zambo da Karin Magana: Matsayinsu da Tasirinsu.” Wannan aiki ba daidai yake da nawa bincike ba, domin ya yi nazari ne a kan matsayinsu da tsasirinsu, inda nawa bincike zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u.

          Bala da wasu (1993) sun rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo mai taken: “Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai Da Waƙoƙinsa.” Sun kasa aikinsu gida biyar. A babi na biyu sun kawo tarihin mawaƙi, a babi na uku sun tattauna a kan ma’anar waƙa da nau’o’inta. A babi na huɗu sun yi sharhin waƙoƙi biyu, ta Magajin Rafin Sakkwato da waƙar Sarkin Daura Muhammadu Bashar ta fuskar jigo da salo. Wannan aiki bai da alaƙa da nawa bincike sai dai binciken namu ya keɓanta ne a kan Alhaji Musa Ɗanba’u. ma’ana mun yi tarayya wurin nazarin waƙoƙinsa kawai. Sai dai kowannenmu abin da yake nazari daban. Su sun yi sharhin wasu waƙoƙi kan jigo da salo. Ni kuma nawa aikin ya keɓanta ne kawai a kan zambo da habaici.

          Safara’u, (1994) ta rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya mai taken: “Habaici da Matsayinsa ga Al’ummar Hausawa.” Wannan aiki ya kawo ma’anar habaici da matsayinsa ga al’ummar Hasuawa. Shi kuma nawa aikin bincike zai fito ne da zambo da habaici a cikin waƙoƙin Ɗanba’u Gidan Buwai. Wannan aikin ba ɗaya ne da nawa ba.

          Abdullahi, (1995) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato mai taken: “Dangantakar Waƙar Baka da Rubutatta ta Fuskar Zambo da Habaici.” Ya kasa aikinsa zuwa gida huɗu. A babinsa na uku ne ya zube zuciyar aikinsa, ma’ana dangantakar waƙar baka da rubutacciyar waƙa. Ni kuma nawa aikin zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Ɗanba’u. wannan aikin ba ɗaya ne da nawa ba, amma zai ƙara mini haske sosai wajen samun nasarar nawa aikin.

          Yahya, (1997) ya rubuta wani littafi mai suna: “Jigon Nazarin Waƙa.” Wannan littafi ya taimaka min wajen sanin yadda ake nazarin waƙa kuma ya ba ni haske sosai ta yadda zan gudanar da wannan aiki.

          Zaruk da wasu (1997) sun rubuta wani littafi mai taken: “Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare.” A cikin wannan littafi sun yi bayani a kan abubuwa da dama cikinsu har da adabi. Daga cikin adabi sun yi tsokaci a kan waƙa kuma sun yi bayanin zambo da habaici ta fuskar ma’ana. Wannan littafi bai tunkari irin matsalar da wannan aikin bincike ya tunkara ba amma zai ba da haske ta yadda za a iya samun nasarar gudanar da wannan aikin bincike.

          Garba, (1998) ya rubuta kundin digiri na biyu a Jami’ar Bayero, Kano mai taken: “Azancin Magana A Waƙoƙin Makaɗan Baka.” Wannan aiki ba guda ne da nawa aikin bincike ba sai dai zan samu haske na cigaba da nawa bincike.

          Shinkafi, (1998) ya rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo mai taken: “Shahararrun Waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali (1975-1960).” Wannan aiki ya yi bayani a kan waƙoƙin Narambaɗa musamman waƙoƙin sarauta inda ya yi bayanin abubuwa da dama har da zambo da habaici. Wannan aikin ba ɗaya ne da nawa aikin ba. Sai dai zai ƙara min haske wajen samun nasaran nawa bincike.

          Maidubu, (1999) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Bayero, Kano mai taken: “Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai Rayuwarsa da Ayyukansa.” Wannan aiki ba ɗaya ne da wannan aikin bincike ba domin wannan aikin ya kawo tarihin rayuwarsa da ayyukansa da kuma bayanin wasu waƙoƙi. Ni kuma nawa aikin zai keɓanta ne a kan zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Ɗanba’u, duk da haka za a sami hasken da zai haska ga wannan aikin bincike.

          Halima, (2000) ta rubuta kundin neman digiri na farko a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo mai taken: “Dabarun Zambo A Cikin Waƙoƙin Sani Aliyu Ɗandawo.” Wannan aiki ya bayyana dabarun da makaɗin ke amfani da su wajen yin zambo a cikin waƙoƙinsa. wannan aikin ba iri ɗaya ne da nawa bincike ba domin nawa bincike zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.

          Yahya, (2002) ya rubuta maƙala mai taken: “Siffantawa Bazar Mawaƙa: Wani Shaƙo Cikin Nazarin Waƙa.” Wannan maƙala za ta taimaka min ƙwarai ta hanyar fito da siffar zambo da habaici a sauƙaƙe a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.

          Ɗalhat, (2002) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo mai taken: “Habaici Da Dangantakarsa Ga Al’ummar Hausawa.” Wannan aiki, ba fuska ɗaya suka duba da wannan bincike ba. Sai dai ya yi maganar habaici kuma habaici wani yanki ne a cikin wannan aikin bincike. Sai dai shi ya yi nazarin habaici da dangantakarsa da Hausawa, shi kuwa wannan aikin bincike zai yi nazarin zambo da habaici ne a cikin wasu waƙoƙin Ɗanba’u.

          Dunfawa, (2005) ya rubuta maƙala mai taken: “Zambo da Habaici A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Addini.” Duk da yake wannan maƙala ta yi nazari ne a kan rubutattun waƙoƙin addini, shi kuma wannan aikin bincike zai yi nazari ne a kan waƙoƙin baka na Alhaji Musa Ɗanba’u za a ga hanyar jirgi daban da ta mota sai dai dukansu sun yi tarayya ne a wajen nazarin zambo da habaici, amma za ta haskaka min ƙwarai da gaske wajen samun nasarar gudanar da wannan aikin bincike.

          Yahaya da wasu (2006) sun rubuta wani littafi mai suna: “Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare.” Wannan littafi ya yi bayanai a kan abubuwa da dama. Daga cikin abubuwan da suka tattauna har da ɓangaren adabi. A ɓangaren adabi kuma sun tattauna a kan zambo da habaici. Wannan littafin zai taimaka wajen samun nasarar wannan aiki, amma ba su da wata doguwar alaƙa, kowane cin gashin kansa yake.

          Mujallar Makrantar Hausa, (2007) ta yi rubutu a kan wasu waƙoƙin Ɗandago tun daga tarihin rayuwarsa da yadda yake tsara waƙa har zuwa kan  yadda yake yabo da zambo da habaici. Mujallar da wannan bincike kowane zaman kansa yake, amma duk da haka, za ta ƙara ba da haske wajen samun nasarar binciken.

          Dangambo, (2007) ya rubuta littafinsa mai suna: “Gadon Feɗe Waƙa.” Wannan littafi ya yi bayanin waƙa ciki da wajenta tun daga jigo, salo da zubi da tsari. Wannan littafi ba ɗaya ne da nawa aiki ba sai dai yana da amfani ƙwarai ga wannan aikin bincike.

          Bunza, (2009) ya rubuta littafi wanda ya raɗa wa suna: “Narambaɗa.” A cikin wannan littafi a babi na shida da ya kira ‘keɓaɓɓo Kananan Jigogin Sarauta’ inda a ciki ya kawo zambo da habaici ya yi bayaninsu a dunƙule. Kuma ya kawo misali a cikin wasu ɗiyan waƙoƙin sarauta. Littafin ba ɗaya ne da wannan aikin bincike ba domin ya yi magana ne a kan waƙoƙin Narambaɗa kawai. Inda wannan aikin bincike zai yi magana a kan zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Ɗanba’u. Sai dai ya zama min hanya ta sanin yadda ake gane zambo da habaici a cikin waƙoƙi da yadda ake sharhin zambo da habaici a cikin ɗiyan waƙa.

          Usman, (2009) ya rubuta maƙalarsa mai taken: “Zari: Kiɗa Sana’ar Ƙira Don Zuga Maƙera.” Cikin wannan maƙalar ya fito da zambo da habaici a cikin wasu ɗiyan waƙa. Wannan aikin ba ɗaya ne da wannan aikin bincike ba, sai dai zai yi ƙarin haske dangane da wannan bincike.

          Shagari, (2011) ya rubuta kundin digirinsa na farko a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato mai taken: “Waƙoƙin Jam’iyyar P.D.P Na Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.” Wannan aikin ya keɓanta ne a cikin wasu waƙoƙi biyu kacal na siyasa kuma na jami’iyyar P.D.P. don haka aikin ya bambanta da nawa. Alaƙarsu kawai ita ce an yi su a kan makaɗi ɗaya.

          Muhammad, (2013) ya rubuta maƙalarsa mai taken: “Habaici A Adabin Al’ummar Hausawa.” Wannan aikin ya yi nazarin habaici tare da bayyana hikimarsa ga al’ummar Hausawa. Wannan aiki ya bambanta da nawa domin nawa aikin zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u.

          Atuwo da Bunza, (2014) sun rubuta maƙalarsu mai taken: “Sulhun Tankiya a Cikin Waƙoƙin Baka da Rubutattu na Hausa.” Inda suka yi amfani da waƙoƙin baka da rubutattu daga cikinsu har da waƙar Ɗanba’u ta haɗin kan Nijeriya, inda suka yi amfani da waƙar suka yi sulhun tankiyar a cikin hikima. Wannan maƙalar da nawa bincike kowane zaman kansa yake. Alaƙarsu kawai ita ce sun yi tarayya a wurin nazarin waƙoƙin mutum ɗaya.

          Gusau, (2014) ya rubuta littafi mai suna: “Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Biyu.” Wannan littafi ya kawo zubin waƙoƙin makaɗan baka cikinsu har da waƙoƙin Ɗanba’u waɗanda suka haɗa da waƙar Magajin Rafin Sakkwato Alhaji Shehu da ta Isa Ɗunɗaye da ta Isiyan Ɗanba’u da ta Janjunan Gidan Buwai da ta Sarkin Arewan Sakwkato da waƙar haɗin kan ‘yan Nijeriya. Aikin ya bambanta da wannan bincike sai dai kawai dukkansu sun yi tarayya a cikin waƙoƙin mutum ɗaya.

          Yahya, da wasu (2015) sun rubuta littafi wanda suka raɗa wa suna: “Sai Alu: Sharhi Kan Waƙoƙin Da Aka Yi Wa Dr Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sakkwato.” Wannan littafi ya kawo zubin waƙoƙin na mawaƙa daban-daban kuma an yi sharhinsu sannan an yi bayani kan jigo/turken zambo da habaici a ciki amma duk da haka ya bambanta da aikina domin an yi amfani da waƙoƙin baka da rubutattu da ba za a rasa waƙar Musa a ciki ba.

          Bagudu, (2015) ta rubuta maƙalarta mai taken: “Gyara Hali da Tarbiya: Nazarin Waƙoƙin Daka Na Mata A Garin Sakkwato.” Wannan maƙala ta fito da hanyoyin gyara halaye da tarbiya a cikin waƙoƙin daka na mata, haka kuma ta fito da turken (jigo) habaici a cikin ɗiyan waƙoƙi da dama. Wannan aiki ba fuska ɗaya suka duba da nawa aikin bincike ba, sai dai ta fito da habaici a cikin waƙoƙin daka na mata, habaici wani yanki ne a cikin nawa aikin bincike sai dai za a fito da shi ne a cikin wasu waƙoƙin Musa Ɗanba’u.

          Junaidu da ‘Yar’aduwa, (2015) sun rubuta littafinsu mai suna: “Harshe da Adabin Hausa a Kammale.” Wannan littafi ya yi bayanin abubuwa da dama da suka shafi harshe da adabi a cikin adabi ya kawo habaici. Wannan littafi ba ɗaya ne da nawa aikin ba, domin nawa aikin zai fito ne da zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Ɗanba’u.

          Yahya, (2016) ya rubuta wani littafi mai taken: “Salo Asirin Waƙa.” Wannan littafi ya yi bayanin salo tun daga ma’anarsa da nau’o’insa da yadda yake zuwa a cikin waƙa. Wannan littafi yana da bambanci da wannan aikin bincike sai dai zai taimaka min ta hanyar sanin yadda Ɗanba’u ke amfani da salo wajen yin zambo da habaici a cikin waƙoƙinsa.

          Yahya, da wasu (2016) sun rubuta wani littafi wanda suka kira: “Alun Nan Dai: Sharhi Kan Waƙoƙin Da Aka Yi Wa Alhaji (Dr) Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sakkwato).” Wannan littafi ya kawo waƙoƙi masu yawan gaske kuma sun ɗauke su ɗaya bayan ɗaya sun yi sharhin kowace daga cikinsu ta hanyar fito da jigogi/turaku manya da ƙanana tare da bayyana salailan da ke cikin waƙoƙin. A gaskiya wannan aikin ya ba ni haske sosai ta hanyar da zan gudanar da nawa bincike cikin sauƙi.

          Gusau, (2016) ya rubuta wani littafi mai suna: “Makaɗa da Mawaƙan Hausa.” Wannan littafi ya ba da tarihin mawaƙa ne, da makaɗan baka a taƙaice cikin mawaƙan da ya kawo har da Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai. Wannan littafi ya fitar da ni wani ruɗu da manazarta suka sa min na rashin samun daidaituwa a kan tsayayyar shekarar da aka haifi Alhaji Musa Ɗanba’u. bayan hira da na yi da wazirinsa Alhaji Shehu waziri ya sheda min shekara da aka haife shi wadda kuma ta bambanta da sauran shekarun da manazarta suka bayyana a cikin ayyukansu. Sai na sami wannan littafi wanda ya ƙara tabbatar min da abin da wazirin Alhaji Musa Ɗanba’u ya sheda min. Na ji daɗi ƙwarai da gaske da ya walwale mini wannan ruɗu da nike fama da shi. Amma duk da irin namijin ƙoƙarin da wannan littafi ya yi min wajen walwale sarƙaƙiyar da ni shiga sun bambanta domin Gusau ya yi aikinsa na littafi kan makaɗa  da mawaƙa da yawa. Aikina kuwa Ɗanba’u kaɗai zai taɓo da waƙoƙinsa da ke ɗauke da zambo da habaici.

1.2 Hujjar Ci Gaba Da Bincike

        Hujjar ci gaba da wannan bincike ita ce a iya inda Allah ya kai ganina, kuma ya ba hannu damar taɓawa domin yin bitar ayyukan da suka gabata wajen nemo wani bincike wanda ya yi canjaras, ma’ana ya yi daidai da irin wannan aiki a matsayin wani littafi ko kundi ko maƙala ko mujalla da za a iya nazari a ilmance ta wannan ɓangaren ba a samu ba. Wannan dalilin shi ya  tilasta ni cike wannan giɓin da aka bari.

          Kasancewar irin shaharar da Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai ya yi a fagen gina zambo da habaici a cikin waƙoƙinsa, wanda ake hasashen kafin rasuwarsa babu wani mawaƙin baka da ya yi fice a ƙasar Sakkwato da ya kai shi a wannan ɓangare ma’ana mai yawan amfani da zambo da habaici a acikin waƙoƙinsa, wasu waƙoƙinsa kusan kashi saba’in cikin ɗari (70%) duk zambo ne da habaici musamman waƙoƙin siyasa da na sarauta, amma kuma babu wani bincike da aka gudanar a kansa. Wannan ya ƙara min ƙwarin guiwar fitowa da wannan a matsayin nazari a cikin adabin Hausa ta ɓangaren waƙar baka domin muhimmancinsa.

1.3 Hanyoyin Gudanar Da Bincike

          A duk lokacin da za a gudanar da bincike dole ne a samu hanyoyi na ilimi da za a bi domin gudanar da shi. Saboda haka, a ƙoƙarin gudanar da wannan aikin bincike za a bi duk hanyar ilimi da ta dace domin gudanar da binciken kamar ɗakunan karatu manya da ƙanana domin samun littattafai da muƙalu da kundayen da za su ba da haske wurin gudanar da binciken. Haka kuma za a kusanci manyan masana da malamai musamman na wannan fanni domin samun ƙarin haske da shawarwari domin a samu nasarar gudanar da binciken.

          A ɓangaren waƙa ita ma za a sanya waƙoƙi waɗanda za a sami zambo da habaici ƙarara ta hanyar kawo hoton yadda mai nazari zai fahimci abin cikin sauƙi. Haka kuma hira da yaran Musa da waɗanda suka san shi da kuma sauran na kusa da shi da kuma sauran abokan hulɗa saboda samun bayanai a kansa da kuma walwale zare da abawar wasu dunƙulallun maganganu da ke cikin waƙoƙinsa. idan an bi waɗannan hanyoyi babu shakka za a samu nasarar gudanar da wannan aikin bincike.

1.4 Muhallin Bincike

          Muhallin wannan bincike shi ne waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai da adabin baka. Harshen Hausa na da rassa guda uku da suka haɗa da Adabi da Harshe da Al’ada. Wannan aikin bincike zai keɓanta ne a fagen adabi. Shi ma adabi an kasa shi gida biyu, wato:

1.     Adabin baka/gargajiya

2.     Rubutaccen adabi/na zamani

Wannan aikin zai keɓanta ne a kan adabin baka. Adabin baka yana da rassa guda uku kamar haka:

1.     Zube

2.     Waƙa

3.     Wasan kwaikwayo

Wannan bincike zai keɓanta ne a akan waƙar

Waƙa ta kasu gida biyu:

1.     Waƙar baka

2.     Rubutacciyar waƙa

Wannan bincike zai keɓanta ne a kan waƙar baka ta Alhaji Musa Ɗanba’u, haka kuma ko a cikin waƙoƙinsa, za a yi nazarin waɗanda ke ɗauke da zambo da habaici kawai.

1.5 Muhimmancin Bincike

          Muhimmancin wannan aikin bincike shi ne domin samun takardar shedar kammala digirin farko a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Ba tare da rubuta aikin ba, wanda yake yana daga cikin sharuɗɗan da ba a kammala digiri sai da shi, ya zan dole a yi shi. Yin sa ke sanya a karɓi digirin, rashin yin sa kuma, kan sanya a rasa digiri. Ƙaruwar ilimi ga mai gudanar da aikin bincike. Fitowa da basirar da Allah ya yi wa Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.

1.6 Matsalolin Bincike

        Babu shakka manazarta masu bincike sukan haɗu da matsaloli daban-daban idan ba a sa haƙuri ba, sai a kasa kai ga nasara, ko kuma ana iya kammala binciken amma babu ƙaruwa da aka samu. Daga cikin matsalolin bincike akwai:

1.     Rashin kuɗi: Da yawa mai bincike zai samu littafi da zai taimaka masa wajen gudanar da bincike, amma ba ya da zarafin sayen shi. Kuma babu shi a ɗakunan karatu, kuma mai shi ba zai ba da aro na tsawon lokaci ba. Wani lokaci duk da kuɗin da za a gurza maka ba ka da. Wani lokaci kuma ko aron ba za a ba ka ba. Haka kuma masu irin wannan bincike, sau da yawa sukan haɗu da matsalolin yankewar guzuri a lokacin da suke bincike ta hanyar zuwa wajen ganawa da waɗanda binciken ya shafa, ko ake bincike a kansu, da su kansu kuɗin da ake buga aikin da su, wani lokaci a neme su ruwa a jallo a rasa.

2.     Mai bincike yakan ci karo da matsaloli ta hanyar dokokin da ake aza masa a ɗakunan karatu manya da ƙanana, wani lokaci za ka tashi daga Sakkwato har Zariya ko Kano tare da takardar neman ba ka dama ka yi bincike amma a gindaya ma wasu sharuɗɗa waɗanda matsawar ba ka yi haƙuri ba sai ka kasa samun abin da kake nema. A ɗakunan karatu na makarantar da kake karatu kakan nemi wata alfarma a hana ka.

3.     Wata matsala da mai bincike ke haɗuwa da ita, ita ce zai ci karo da ayyuka masu magana a kan mutum ko abu ɗaya amma bayanin kowane ya bambanta da na wani kuma kowane ya ce ya samo shi ne daga tushe.

4.     Haka kuma masu riin wannan bincike na waƙa sukan ci karo da matsaloli wurin ganawa da mawaƙa ko kuma yaransu da suka gaje su. Kasancewar ba su zama wuri ɗaya, a yi ta nemansu abin ya ci tura wani lokaci har mai bincike ya ji kamar a canza mai wani taken bincike.

5.     Wata matsalar bincike ga masu nazarin waƙa ita ce, ta hanyar neman waƙoƙin da tattara su da rubuta su musamman waƙar baka. Yana da matuƙar wahala hasali ma wata waƙa za ta ƙawata ma aikinka ka tashi gari da gari ka je inda wanda anka yi wa waƙar bai da ita. Haka kuma ka je wajen mawaƙin shi ma bai da ita. Haka za ka yi ta yin wahala wani lokaci ka samo wani lokaci kuma ka rasa.

1.7 Naɗewa

          A wannan babi an tattauna manya-manyan muhimman tubalai na gina kowane bincike da manazarci zai gudanar a kowane ɓangare na ilimi a ciki ne zai kawo hoton yadda binciken zai gudana daga farkon babi na ɗaya har zuwa ƙarshe a matsayin gabatarwa da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike tare da kawo hanyoyin da ake bi wajen gudanar da bincike da kuma bayyana inda muhallin bincike zai keɓanta. Haka kuma an bayyana muhimmancin bincike da irin taimakawa da yake yi wurin cigaban ilimi. Haka kuma an kawo matsalolin da aka haɗu da su wurin gudanar da bincike.

Kayan kidan hausawa


Post a Comment

0 Comments