Tambaya: Malama Ina da tambaya. Wai shin me yake hana sha’awar iyali shekararmu biyar da matata amma daga baya sai na ji sam ba na sha’awarta.
BILKISU YUSUF ALI
Rashin kwanciyar hankali:
Duk lokacin da ya kasance babu kwanciyar hankali tsakanin ma’aurata ba yadda za a yi sha’awa ta gitta. Rashin kwanciyar hankalin nan, ko dai ta ita matar da mijin ko mijin da iyayenta ko da yanayin gari ko matsugunni da dai duk wani nau’in rashin kwanciyar hankalin da zai janyo rashin nutsuwa da fargaba ko zulumi. Hatta a wurin aiki in har namiji yana fama da fargaba da rashin nutsuwa to tabbas zai iya neman sha’awa ya rasa. Sannan ga macen da take da yawan Æ™orafi da daddare sawa’un matsalarta ko ta kishiya ko ta ‘ya’yan miji a lokacin da namiji ya zo da buÆ™atarsa ita ma kan haifar masa rashin kwanciyar hankali wanda duk wannan yana iya janyo rashin sha’awar Maigida ga iyalinsa.
Talauci:
Talauci ko rashin abin hannu shi ma babban makami ne da ke yanke sha’awa. Duk lokacin da samun mutum ya yi Æ™asa kuma buÆ™latunsa suka ninka har ya shiga saÆ™e-saÆ™en mafita to fa zai yi wuya duk maganin da zai sha ya yi masa tasiri kan wannan matsalar, dole makarin matsalar shi ne a samu abin da ake buÆ™ata. Hatta rashin muhalli mai kyau da nutsuwa shi ma kan zama barazana ga sha’awa tsakanin iyali.
Roƙo:
Akan samu mata masu roÆ™e-roÆ™e ga maigida kuma sukan riÆ™e makamin roÆ™onsu shi ne lokacin da maigida yake da buÆ™atar kasancewa da su. Daga lokacin da wannan ya zame wa mace al’ada kuma miji ya tsani hakan to yana iya zama wani sanadari na kashe masa sha’awar maiÉ—akinsa.
Ƙazanta:
Duk lokacin da Maigida zai kalli abin da ba ya son idonsa ya kalla, ko ya shaÆ™i abin da ba ya son hancinsa ya shaÆ™a, ko ya taÉ“a abin da ba ya son ya taÉ“a, to tabbas a sannu Uwargida za ta gusar masa da dukkan sha’awarsa. Don haka tsafta tana da matuÆ™ar tasiri wajen Æ™arfafa sha’awar Maigida. Haka Æ™amshi na cikin sinadaran da ke Æ™arfafa sha’awa.
Biyayya:
Duk lokacin da mace ta zama ba ta biyayya ga mijinta , kullum tana cikin É“ata masa rai nan ma zai yi wuya yake sha’awarta. Ita irn wannan biyayyar ba sai iya kansa ba hatta iyayensa in ya lura ba ta mutuntawa ko darajjantawa to tana iya fita a ransa.
Rashin ni’ima ga mace:
Akan samu mata marassa ni’ima da iya sarrafa maigida yayin mu’amalar aure wannan nau’ikan matsalolin sukan shafi zamantakewa da kuma sha’awa tsakanin iyali. Haka ma idan namiji ya fuskanci cewa matar ba ta sha’awarsa ko ma ba ta son kasancewa tare da shi, irin wannan matsalar kan kawo matsalar.
Ha’inci da Æ™arya da cutar da abokin zama ko ’ya’yansa:
WaÉ—annan dalilan kan sa mace ta fita a zuciyar namiji har ya ji ba ya son ko ganinta bare sha’awarsa ta kai gare ta.
Akwai dalilai da dama wanda na zamantakewa ne ke kawo wannan matsalar ba wai rashin lafiya ba.Za mu É—ora daga inda muka tsaya a mako na gaba in sha Allah.
Ga mai neman ƙarin bayani ko tambaya kan wani abu day a shafi lafiyar iyali yana iya aiko da tambayarsa ta hanyar wannan lambar 08039475191 ko ta Page ɗina Ilham Special care and treatment ko a Facebook account ɗina Bilkisu Yusuf Ali.
Credit to: Manhaja Blueprint
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.