Abaya: Abubakar Alkantamawy Nakowa ya rubuta gajeruwar waƙa mai taken "Jan Kunne" inda ya yi batu a kan sayen abaya.
Jan Kunne
Abubakar Alkantamawy Nakowa
08022581902
Kar ka yarda ka zam a baya, Garzaya ka sayo Abaya, Babu sabo ba sanayya, Hajiya bata zo da rangwame ba.
In kwa babu kudin sayen ta,
Jeka gun dangi ka ranta,
Don nufin ka sayo ka ba ta,
Zance ne ba abin musu ba!!
Wanga zancen gaskiya ne,
Na fada kowa ya gane,
Sa Abaya wajibi ne,
Kuma ba son zuciya na ke ba.
Duk macen da ta sa Abaya,
Za ta zanto me biyayya,
Gun mijinata ba kiyayya,
Tunda ta San ba rago bane ba!
Me gida maza jeka shago,
Gun Abaya ka yada zango,
Kar ka yarda a gan ka Raggo,
Ban zo da batu abin musu ba.
Saurayi kai ma ka dage,
In kana fatan ka burge,
Yankura damtse ka zage,
Raggo ba za ya Sha Zuma ba!
In ka so ka daramma kowa,
Sai Abaya ka bai budurwa,
Martabarka ta zan dagawa,
Ya zamo ba a kai ka daukaka ba.
In kwa har ka sake ka noke,
Naka aljihu ka damke,
To rijsta za a soke,
Maka ba wai sai da an jima ba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.