Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), marubuci ne kuma mawaƙin Hausa na zamani ne wanda ya shahara sosai a fagen waƙoƙin fiyano. Sai dai kafin shaharar tasa a fagen waƙoƙi ya kasance marubucin littattafan labarin Hausa na Adabin Kasuwar Kano. Amma duk da irin wannan gudummawa da ya bayar a fagen rubutaccen labari, manazarta ba su mayar da hankali wajen nazartar littattafansa na labari kamar waƙoƙinsa ba. Shi ya sa wannan maƙala ta ɗinke wannan giɓi, ta nazarci gudummawar Aminu Alan Waƙa a fagen rubutaccen labarin Hausa. An tattauna matsayinsa na marubucin labari kafin mawaƙin zamani, sai kuma sharhin littattafansa da saƙonnin da suka ƙunsa. An yi nazarin ayyukansa da Tarihin rayuwarsa, an gano cewa saƙonnin da suke ɗamfare da littattafan da ya rubuta suna da kamanci da irin saƙonnin da yake tsarmawa a waƙoƙinsa na faɗakarwa da hannunka-mai-sanda da bayyana halin da ƙasa ke ciki da makamantansu. Sa’annan littattafansa suna ƙunshe da saƙonni na gyaran halaye da ɗabi’u kyawawa da kuma riƙo da addini bisa tafarki nagari.
Aminu Alan Waƙa a Fagen Rubutattun Ƙagaggun Labarai na Hausa
Na
Abdullahi Mujaheed
Sashen Harsunan Nijeriya
Da Kimiyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna
mujaheedabdullahi@gmail.com
+2348069299109, +2348156747550
1.0 Gabatarwa
Bahaushe kan ce a san
mutum a kan cinikinsa. Da zarar an ce Aminu Ladan Abubakar (ALA), abin da
galibi jama’a suka sani ALA ɗaya ne daga cikin mawaƙan zamani da suka shahara a
wannan ƙarnin. Shi ya sa ma laƙabinsa Alan Waƙa. Nazarce-nazarce da dama (Dikko,
2010; Giɗaɗo, 2012; Rogo, 2013; Shehu, 2011; Yakasai, 2012 da sauransu) duk sun
taɓo mabambantan batutuwa game da adabin ALA ta fuskar waƙa, sai dai ayyukansa
na rubutaccen labari ba su sami tagomashi ta fuskar nazari da sharhi ba; ba su
ma sanu sosai kamar waƙoƙinsa ba. Duk da cewa aikin Shehu, (2011), ya zayyano
ayyukan ALA da suka shafi waƙa da wasan kwaikwayo da rubutaccen labari, sai dai
bai yi sharhi ko nazarin ƙumshiyar littattafan nasa ba. Da yake Bahaushe kan ce
sanin asali shi ke sa kare cin alli, wannan maƙala ta lalubo cewa ALA ya fara
noma rubutaccen labari ne a gonar adabin Hausa, wato ya fara baje-kolin
fasaharsa ne a fagen rubutaccen labarin Hausa na zamani, kafin ya sauya akala
zuwa waƙa. Sai dai a fagen waƙar ne aka fi sanin sa, domin a nan ne ya shahara.
Shi da kansa ya faɗa a waƙarsa cewa, shahararsa a rubutaccen labari ba ta kai
ta waƙoƙi ba, shi ya sa ma ba a ji ɗuriyarsa ba a fagen rubutaccen labarin
Hausa, ballantana rubuce-rubucen nasa:
Na tuno farkon ɗagawa,
Da ina ɗan ƙanƙanina.
Nai firamare garinmu,
Da sakandire sanina.
Na zamo alkatibin nan,
Marubucin so da ƙauna.
Ba domin ban iya ba,
Shahara ta hana sanina,
Babu wanda ya san da
ALA,
To bare aikin wurina.
(ALA: Waƙar Shahara ta 1)
Saboda haka, duk da cewa ALA bai shahara a fagen rubutaccen
labarin Hausa ba, ba za a rasa abin tsinta ba ta fuskar nazari cikin
littattafan da ya rubuta. Shi ya sa wannan maƙalar ta lalubo wasu daga cikin
littattafan nasa ta nazarce su, musamman ƙunshiyar saƙonninsu.
2.0 Marubuci Kafin Mawaƙi
Nazarce-nazarce da dama (Dikko, 2010; Giɗaɗo, 2012; Rogo, 2013;
Yakasai, 2012 da sauransu) duk sun yi rubdugu kan tarihin rayuwar ALA da
ayyukansa na waƙa. Saboda haka abin da za mu yi a nan ba batun haihuwarsa da
ilimi da gwagwagwarmayar rayuwarsa ba ne, illa ƙyallaro abin da ya shafi
kasancewarsa marubucin labarin Hausa kafin zama mawaƙi.
Batutuwan da suka shafi ilimi da tattalin arziƙi sun yi katutu a
ƙasar Hausa a farkon shekarun 1980[1].Waɗannan batutuwa sun yi
tasiri wajen samuwa da bunƙasar rubutaccen labarin Hausa na zamani, fasalin da
ya haifar da Adabin Kasuwar Kano (AKK). ALA ya faɗo cikin rukunin marubuta irin
wannan nau’in adabi na AKK. Kuma kamar yadda ya bayyana a wasu waƙoƙinsa, ALA
ya yi karatun addini da na zamani, kuma ya sha fafutikar neman abin yi domin
riƙe kansa da iyalansa amma abin ya faskara. Saboda haka sai ya jefa kansa
cikin harkar rubuce-rubuce[2] daga bisani kuma ya
koma waƙa. Domin jaddada wannan batu, ga abin da ALA ya ce:
Ba kurum nake wai na ƙi sanna’a ba,
Har karatun Arabic fa ban ƙi nai ba,
Har karatun boko fa ban ƙi nai ba,
Nashinal difiloma na yi duba.
Da takardu na zaga ofisoshi,
Bambaɗanci na yi shi har na ƙoshi,
Kamfanoni na bi su ofisoshi,
Babu aiki ba hanyarsa garan ba.
Ga iyalai ga matata da yara,
Babu natsuwa in koma in taƙara,
Cigaban boko ba tsimi dabara,
Mafakata ubangijinmu Rabba.
Babu aiki na dogaro na kaina,
A rubutu na fara jefa kaina,
Yau a waƙa kuma na tsinci kaina,
Faɗakarwa ba watsa tarbiya ba.
(Aminu ALA: Waƙar Kurkuku)
Hada-hadar bugawa da sayarwa na littattafan ALA, duk sun kasance a
kasuwa ne kamar duk wani adabin kasuwa. A cikin waƙoƙinsa, ALA ya jaddada
rubuce-rubucensa suna cikin rukunin Adabin Kasuwar Kano (AKK) ne. Misali a
waƙar Shahara ta 1, ya ce:
Da ina alkatibi na,
Marubucin so da ƙauna[3].
In na wallafa ɗab’ina,
Sai in sanya wayar
kirana.
A jikin bangon kitabu,
Manufata ai kira na.
In da mai gyara ya ba
ni,
Ko ko sukar ƙallamina.
In da mai ƙarin bayani,
Ko gani na ko yabo na.
Ko ko aiki ne a ba ni,
Ga wayar tarhon gidana.
(ALA: Waƙar Shahara ta 2)
Abin ban sha’awa shi ne, marubucin yana maraba da suka ko gyara in
an ga kura-kurai cikin rubutunsa, shi ya sa ma yake sanya lambar wayarsa. Sai
dai ALA bai jima a harkar rubutaccen labari ba, ya watsar ya koma waƙoƙin
fiyano, inda a nan ya fi shahara, a nan aka san shi, kuma a nan ya huda ya ga
jini har ya samu gindin zama. Amma duk da haka, ai tushiya mafarin dawa; ALA
marubuci ne kafin ya juya akalar fasaharsa zuwa waƙoƙin zamani a shekarar 2003,
kamar yadda ya sha faɗin haka da bakinsa.
A hirar da aka yi da shi a Sashen Harsuna da Al’adun Afirka na
Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ranar 31/07/2018, ALA ya bayyana:
‘Na fara rubutu a shekarar 1992, amma ya fara bayyana a hannun
mutane a shekarar 1999. Na fara rubuta littafi mai suna Jirgi Ɗaya Shi
Ke Ɗauke Da Mu. Littafina na ƙarshe wanda hukumar A Daidaita Sahu ta yi
ɗab’insa shi ne Ceto Ko Cuta? Na yi littattafai aƙalla guda tara,
waɗanda ake kira Adabin Kasuwar Kano in ji wani Farfesa, masu karantawa kuma
suka ce littattafan soyayya. Ni dai na ɗauke su a matsayin littattafan
faɗakarwa.’ ALA.
Ke nan, ALA ya kasance marubucin labarin Hausa tun daga 1992
ko1999. Sai kuma ya zama mawaƙi daga shekarar 2003 zuwa yau, duk da ya cigaba
da rubutun labari har 2005. Bugu da ƙari, har yanzu yana amsa sunansa a
matsayin marubuci, kuma yana tutiya da kasancewarsa marubucin. Alal, misali, a
waƙar Kyauta, ALA ya jaddada shi fa komai-da-ruwansa ne a harkar
waƙa da rubutu da nazari:
Idan aka ce ALA mawaƙi ni
ne,
In aka ce alkatibi ma ni
ne,
In manazarci anka ce muku ni ne,
Fulani ki san wannan fa farilla ne.
(ALA: Waƙar Kyauta).
3.0 Rubutu a Tunanin ALA
Mallakar iya rubutu kowane iri ne, kafa ce ta mayar da tunani ko
harshe a cikin takarda. Shi ya sa labarin da kowace al’umma ke badawa bayani ne
game da rayuwa da yadda ta gudana ko take gudana ko za ta iya gudana, sa’annan
yana tafe ne bisa matakai biyu na rayuwar, ko dai a shirya shi a ƙwaƙwalwa a
wanzar da shi ta baki ko kuma a rubuta shi daidai da zamanin da ya samar da
shi, (Malumfashi, 2018: Sh. 1-2). Aminu ALA ya bayyana cewa tsintar baiwar
rubutu ya yi a tare da shi kawai, don haka ya zama wajibi ya yi rubutu. Sai
kuma ya kawo wasu ƙananan dalilai da suka zama musabbabin yin rubutun gare shi,
inda ya bayyana cewa fitar da abin da ke cikin zuciya da faɗakarwa da tallar
harshe da kuma neman kuɗi su ne suka jefa shi cikin harkar rubutun zube,
musammam na labarin Hausa, (Gidan Dabino, 2018)[4]. Abin lura a nan shi ne, ALA
bai ɓoye batutuwan da suka shafi neman kuɗi a matsayin dalilinsa na shiga
harkar rubutu ba, sai dai abin da ke da muhimmanci shi ne ya sanya tallata
harshe da kuma faɗakarwa a gaba, shi ya sa ma ya ɗauka cewa tun da fa Allah
(SWT) ya hore masa baiwar rubutun, to fa rubutun ya zama ‘wajibi’ a gare shi,
ko ba komai ya sami kafa ta furzar da abin da ke cikin zuciyarsa. Bugu da ƙari,
fasihin ya sake jaddada wannan batu a cikin waƙarsa ta Shahara,
inda ya ce:
Yin rubutu gare ni,
Wajibi ne a wajena.
Ba batun samun muƙami,
Ko kuɗi daula sanina.
(ALA: Waƙar Shahara ta 1)
Duk da a wannan misali
da aka tsakuro daga waƙarsa, yana da’awar wajibi ne ya yi rubutu don ya isar da
saƙon faɗakarwarsa ga al’umma, amma dai amfanin zunubi romo. Shi ma ALA kamar
kowane ɗan’Adam yana buƙatar abin masarufi. Don haka ne ya bayyana cewa shi da
sauran marubuta ‘yan’uwansa suna buƙatar goyon bayan hukuma da mazhabobin
ilimi, (Gidan Dabino, 2018). Hakan shi zai sa a martaba ayyukansu har su sami
karɓuwa cikin al’umma, karɓuwar nan kuwa ita za ta kai shi ga samun muƙami da
kuɗi har ma da daular.
4.0 Rubutaccen Labarin
ALA
ALA ya rubuta
littattafai na ƙagaggen labarin Hausa guda takwas (8). Littattafan su ne Cin
Zarafi 1da 2 da Jirgi Ɗaya waɗanda suka fito a
shekarar 2001. Sai a shekarar 2002 ya fitar da Baƙar Aniya 1 da 2,
sai Tarzoma a shekarar 2003 . Sai kuma Sawaba da Cin
Fuska na 1 da 2 da kuma Jirwaye, duk a shekarar 2005. Sai
kuma littafin Ceto Ko Cuta[5]. Duk littattafan da
suka zo hannu sun dace da siffofi na Adabin Kasuwar Kano (AKK), domin kuwa
littattafai ne na yayi, kuma har ma sun yi yayinsu sun ƙare. Sa’annan ba su da
yawan shafuka, alal misali, littafin Sawaba yana da shafuka 64,
yayin da Tarzoma ke ƙunshe da shafuka 48, shi kuwa
labarin Baƙar Aniya 1 an tsara shi ne cikin shafuka 40,
sai Jirwaye… mai shafuka 56, Cin Fuska kuwa,
shafukansa 53 ne, da sauransu.
BAƘAR ANIYA 1 labari
ne a kan rayuwar masoya biyu Hauwa da Auwalu, waɗanda suna gab da aure Auwalu
ya yi haɗari a hanyarsa ta dawowa Kano daga Jigawa. Haɗarin ya yi sanadiyyar
samun ciwo a ƙwaƙwalwarsa, wanda sai da aka fitar da shi ƙasar Indiya ya yi
wata 6, bayan jinya ta tsawon wata 4 a Nijeriya. Gab da za a fitar da shi kuma
sai ciki ya bayyana a jikin Hauwa’u duk da ba a ɗaura masu aure ba. Lamarin da
mahaifinta ya danganta da Auwalu, amma ita ta yi musu ta kuma tabbatar da ba ta
taɓa yin zina ba. Ƙullin labarin ya nuna za a iya ɗora lamarin ga Abbas abokin
Auwal wanda Hawwa’u ta je gidansa gaishe da matarsa ta tarar ba ta nan, ya fita
aikawa a kira ta, ya dawo ya tarar ta yi bacci ya haike mata.
Wannan ƙulli shi aka cigaba da warwarewa cikin labarin CIN
FUSKA wanda ya kasance labari kan rayuwar Abbas ɗan da Hawwa’u ta
haifa, wanda ya taso a matsayin malamin sunna kuma ya sha gwagwarmaya da
malaman ɗariku wanda hakan ta yi sanadiyyar fallasa wani sirri game da
rayuwarsa wanda bai sani ba, cewa an haife shi ne ba ta hanyar aure ba. Har ila
yau, bambancin aƙida ta sanya mahaifin Abida ya warware alƙawarin aura wa Abbas
ɗin ɗiyarsa har ya sa katangar ƙarfe tsakaninsu.
Labarin Abbas ya cigaba a littafin SAWABA inda
aka nuna sakamakon takura da tsanani na ruɗanin al’umma, Abbas ya yi hijira da
nufin ƙaro ilimin aƙida a ƙasashen Yemen da Sudan. A kan hanyarsa, ya ya
sda zango a ƙasar Nijar kuma ya sami karɓuwa wajen mutanen garin da ya sauka,
saboda suna jin daɗin da’awarsa. Daidai lokacin da jama’ar garin suka tanadi
fili da zummar gina masa makaranta da zai rinƙa koyar da su ilimin addini. Shi
kuma Alhajin da Abbas ya sauka a gidansa ya ƙudiri aniyar aura masa ɗiyarsa
Ramla, sai Abbas ɗin ya bijiro da uzurin ci gaba da tafiya don isa inda ya
ɗauro niyya tun daga gida wato zuwa ƙasar Yemen ko Sudan. A nan ne Abbas ya ba
Alhaji cikakken labarinsa, ya kuma yi alƙawarin in ya je zai dawo, daga baya a
yi auren. Abbas da Ramla suka yi bankwana tare da ɗaukar alƙawarin riƙe amanar
juna. Marubucin ya ƙare labarinsa da cewa sai a littafinsa na gaba mai
suna MASLAHA za a ji ƙarshen wannan labari na Abbas.
Labarin TARZOMA an gina shi ne kan rayuwar Ayuba
wanda ya kasance Bahaushe Musulmi ɗan asalin Sakkwato ta ƙasar Hausa, mazaunin
Kudancin Nijeriya. Daga bisani, ya komo Kano da zama, ya ci gaba da fuskantar
ƙalubale da tarzomar rayuwa, abin da ya kai shi ga rayuwa a garuruwa irin su
Anambra da Ikko da Kaduna, har ya haura ƙasashen Libya da Spain. Ayuba mahauci
ne wanda sana’ar fawa ita ta kai iyayensa har suka zauna a Anambra, bayan
rikicin ƙabilanci ya yi sanadiyyar kashe iyayen nasa, ita kuma ƙanwarsa Asiya
ta bi tawagar ‘yan gudun hijira zuwa ƙasar Libya. Ƙarshe dai sun haɗu da ƙanwar
tasa a Libya suka dawo Kano inda a nan ne ta gamu da ajalinta, shi ma daga
bisani ya mutu bayan taƙaitaccen lokaci na zamansa a Kano.
Shi kuwa labarin JIRWAYE an gina shi ne kan irin
ta’annati da badaƙalar da ake aikatawa a bayan fage a masana’antar shirya
fina-finai wadda ta shafi lalata da mata kafin shigar da su harkar da wasu
ɓata-gari ke yi (kan-ta-waye). A cikin labarin Nismatu ta kasance suna
zaune da mijinta Assadiƙ a garin Yamai a ƙasar Nijar. Sai dai ba ta daraja shi
duk da yana ƙoƙarin kyautata mata, ita a nata ɓangaren tana la’akari da irin
rayuwar da take kallo a fina-finan Hausa. Hakan ya sanya ta gudu daga gidan
mijinta ta tafi Kano domin shiga harkar fim.
A karon farko ta faɗa hannu nagari, inda ta kai kanta wajen wasu
furudusoshi biyu, suka ƙi amsar ta kai-tsaye. Suka ce sai ta zo da mahaifinta
ko wakilinta da sauran wasu ƙa’idoji da suka gindaya mata. Daga bisani sai ta
afka hannun wasu gurɓatattun furodusoshi, suka yi lalata da ita suka fara saka
ta a fim. Wannan ya buɗe mata ƙofar yin fice a harkar yadda ta fito a
matsayin jaruma a fina-finai uku cikin watanni uku da kwana tara. Daga bisani
dai bayan ta sami matsala da iyayen barikinta Dasal da Akwanga, sai ta yi
fargar jaji, ta fara nadamar wulaƙanta kanta da ta yi, ta baro ɗakin aurenta,
ta shigo harkar da ta mayar da ita gulbi makamfatar kowa. Sai dai lokaci ya
ƙure mata, domin iyayenta sun cire rai da dawowarta, tun da ba-amo-ba-labari,
sai suka aura wa Assadiƙ ƙanwarta Yasmin. Bayan auren ne, wata rana Yasmin da
mijinta Assadiƙ da ƙaninta Nasir suna kallon wani fim mai suna BULAYI,
sai suka yi kaciɓis da fuskar Nismatu cikin taurarin fim ɗin. A daidai nan
marubucin ya gintse labarinsa inda ya nuna sai a littafinsa na gaba mai
suna ƘYANƘYASA zai cigaba da labarin domin kawo
hannunka-mai-sanda kan gyare-gyaren da harkar fim ke buƙata, ko kuma nuna
gyaran da aka samu in an samu.Ya kuma yi albishir zai baddalar da littafin zuwa
fim.
An lura cewa, yawancin littattafan ALA yakan gintse labari, ya
cigaba a wani sabon littafin. Misali;
1. Baƙar Aniyaà Cin Fuskaà Sawaba
2. Jirwaye àƘyanƙyasa.
5.0 Abubuwan Da Aka Binciko
Abubuwan da aka binciko sun ta’allaƙa ne kan saƙonnin da suke
ɗamfare cikin rubutattun littattafan ƙagaggun labarai na ALA. Saƙonnin da aka
ci karo da su kamar a waƙoƙinsa ne, wato galibi faɗakarwa ce a ɓangarorin
zamantakewar rayuwar yau da kullum. Saƙonnin sun haɗa da nuna muhimmancin
haƙuri da riƙo da addini da taka-tsantsan a soyayya da sauran makamantansu.
Saboda haka, abin da za mu yi a wannan gaɓar shi ne fasalta saƙo a cikin
littattafan rubutattun ƙagaggun labarai na ALA.
5.1 Saƙo a Rubutaccen Labarin ALA
Rubutun ALA ya fara shiga hannun mutane daga shekarar 1999 kuma ya
ci kasuwarsa ta rubutu har zuwa shekarun 2003-2005. Saboda haka, kafin nazarin
saƙo a rubutaccen labarin ALA, yana da muhimmanci a yi bitar zangon da
marubucin ya faɗo cikin tarihin adabin Hausa. Kenan idan aka yi la’akari da
zangunan rayuwar Adabin Kasuwar Kano (AKK), littattafan ALA sun faɗo
cikin zanguna uku mabambanta, wato zangon ‘Balaga’(1990-1995) da kuma zangon
‘Tsufa da Hayayyafa’(1996-2001) sai kuma zangon ‘Ya’ya da Jikoki’(2002-2008).
Galibi littattafan da aka samu a waɗannan zanguna, sun zo da
fasalin ni na rubuta, ni na gyara, ni na kai inda za a buga mini, ni kuma
ke sayarwa da kaina (Sabe, 2011). Abin mamaki, galibi nazarce-nazarcen da aka
gudanar kan AKK (in ma ba a ce duka ba) ba su taɓo littattafan Aminu Alan Waƙa
ba[6].
Ta fuskar saƙo kuwa, marubutan AKK na farkon-farko yawanci,
saƙonnin soyayya suka tanada a cikin littattafansu, sai kuma batutuwan da suka
shafi zamantakewa da rayuwar aure da sauran saƙonnin da suka haɗa da rikici da
kishi da sauransu (Sabe, 2011). Idan muka dawo kan littattafan ALA na
rubutaccen labari muka yi masu fyaɗar kaɗanya, za mu tarar saƙonnin da suke
karakaina cikin littattafan nasa galibi saƙonni ne na faɗakawa. Faɗakarwa ita
ce nuna halin ɗa’a wanda zai kasance tsayayyiyar hanya ɗauke da ma’aunin
halayyar ɗan’adam na zahiri da son rai kuma ya kasance a kawar da aiwatar da
wata halayya mara kyau da mai kyau, (Encyclopaedia Britanica, 1943-1973:11).
Kenan faɗakarwa na nufin gargaɗi wanda ya ƙunshi tunasarwa kan ‘yi’ ko ‘bari’
da yi wa mutum hannunka-mai-sanda cikin nusarwa da tsoratarwa da amfani da
sauran hanyoyin gyaran zama ko kan gyaran rayuwa. Daga nazarin da aka gudanar,
saƙonnin faɗakarwa cikin labaran ALA sun fito da fasalce-fasalce da dama da
suka haɗa da:
5.1.1 Nuna Muhimmancin Haƙuri
Haƙuri na nufin juriya ga wani abu na ɓacin rai ko masifa, (CNHN,
2006:190). Haƙuri yana da matuƙar muhimmanci a rayuwa. Sanin haka ne ma ya sa
Bahaushe yake da karin magana irin su ‘haƙuri maganin zaman duniya’; ‘mai
haƙuri yakan dafa dutse har ya sha romonsa’ da sauransu. A cikin
labarin Sawaba, bayan an idar da sallah a masallacin da yake sallah
a garin da ya sauka, Abbas ya yi nasiha tare da nuna muhimmancin haƙuri a
rayuwa, inda ya ce:
Mu ɗauki haƙuri, mu kau da dogon buri, mu zuba jari ga
Allah, ta hanyar aiwatar da aiki nagari domin mu riski sakamako irin na masu
haƙuri ranar tashin alƙiyama. (Sawaba, shafi na 26).
A nan, marubucin ya nuna muhimmancin haƙuri a rayuwar duniya, inda
ya nuna shi haƙuri tamkar jari ne wanda ribarsa ba ma a duniya ba ne, har da
ƙiyama.
5.1.2 Taka-tsantsan a Soyayya
An lura cewa wajen gina rayuwar soyayya cikin labaransa, ALA
yana aika saƙonni ga masu karatu cewa a kiyaye ƙa’idar al’ada da ta addini
yayin da ake soyayya. Alal misali, a labarin Cin Fuska, marubucin
ya nuna lokacin da Abida ta ziyarci Abbas a gidansu, mahaifiyar Abbas ɗin ta
jawo hankalin Abida a kan ta kiyaye ƙa’ida a mu’amalarsu, inda ta ce:
Abbas na ɗaki yana karatu, ba na jin ya fita. Amma Abida kar ki
sake kuskura ki ƙara yin haka daga yau, da zarar an tashe ku daga makaranta ki
rinƙa zuwa gida iyayenki su gan ki tukun, kuma ma in dai ba gurina kika zo ba,
to kada in ƙara jin cewa kin zo wurin Abbas, wannan ba mutuncinki ba ne kina
‘ya mace, duk da kuwa na san cewa haɗuwarku alkhairi ne tun da karatu yake koya
miki, to in ba kin zo karatun ba ko kin zo gurina kar ki rinƙa zuwa gurinsa
kai-tsaye. Kin ji ko Abida? (Cin Fuska, shafi na 5).
Wannan ya jaddada yadda Bahaushe yake taka-tsantsan a kan batun
keɓancewar mace da namiji, ko da kuwa suna soyayya ne, domin gudun kauce wa
ƙa’ida da aikata ɓarna. Har ila yau, a hirarsu da Ayuba cikin litttafin Tarzoma,
Aminuddeen ya tambayi Ayuba cewa:
Ko da dai ka ce ba ka da ilimin addini amma dai duk da haka na san
ba za ka fasa sanin illar zaman dadiro ba a addinance, don ko addinin
Kiristoci ya yarda da aure ko? (Tarzoma, shafi na 16).
Wannan ya tabbatar da cewa a al’adance, Bahaushe yana ƙyamar zaman
dadiro da duk wani nau’i na fasiƙanci, tun kafin ya rungumi addinin Musulunci
ko na Kiristanci. Shi ya sa marubucin ya saƙa wannan saƙo domin faɗakarwa ga
al’umma. Bugu da ƙari, da yake an ce ‘abincin wani gubar wani’, abin da
yake daidai a tsarin rayuwar wata al’ummar kan iya zama baibai ga wata
al’ummar. Alal misali, a yayin da wata al’ummar ta amince da saurayi da budurwa
su rungumi juna yayin da suke soyayya, Bahaushe bai yarda da haka ba a
al’adarsa. Ba kamar sauran AKK ba, Aminu ALA yana cusa ƙyama ga irin wannan
ɗabi’a cikin rubuce-rubucensa. Misali, a littafin Baƙar Aniya 1,
muryar mai bayar da labarin ta nuna cewa Hauwa’u da Auwalu:
Suna ƙaunar junansu kamar su haɗiye junansu don soyayya, amma
daidai da second ko minti ba su taɓa haura iyaka ba, a fagen
soyayya, hannunsa bai taɓa saɓanin ya gogi nata ba ko da wasa, saboda kawaici
da tsantseni gami da tsoron Allah na kowannensu…. (Baƙar Aniya, shafi na
11).
Wannan ya jaddada yadda marubucin ke tsarma saƙonnin faɗakarwa
game da taka-tsantsan a harkar soyayya domin tabbatar da al’umma tagari.
5.1.3 Nuna Muhimmancin Riƙo da Asali
Asali shi ne mafari ko tushe ko salsala (CNHN, 2006: Sh.
20). Asali abin tutiya ne a wajen Bahaushe, shi ya sa kowa ke tinƙaho da
asalinsa. Muhimmancin riƙo da asali ya sanya Bahaushe yake da karin magana irin
su ‘kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi’; ‘kowa ya bar gida, gida ya
bar shi’, da sauransu. A littafin Tarzoma, ALA ya faɗakar da
al’umma kan muhimmancin riƙo da asali a lokacin da Ayuba yake bayar da labarin
rayuwarsa a Ikko, inda ya ce:
Sai a lokacin ne na gane kuskuren mahaifina, na kuma ci gyaran
kaina da kaina, a sa’ilin da na tuno, sau biyu kaɗai mahaifina ya taɓa kai ni
yankin Sakkwato ganin gida, duk kuma a lokacin da ba ni cikin hankalina na sake
tuna lokacin da ya rinƙa gaya mini cewa ya kamata in fara shirin zuwa gida zai
mini kwatance, ko domin in hutar da shi ya rage tafiye-tafiye, saboda matsalar
basur da ke addabarsa. Na yi takaici mai tsanani a lokacin da ƙarairayin da na
rinƙa yi suka faɗo min, a inda na rinƙa togaciya da karatu ina zuzzuƙewa, kuma
a zahirin gaskiya ba ni ko sha’awar zama garin da Bahaushe yake a wannan
lokaci. (Tarzoma, shafi na 11-12).
A nan, marubucin ya nuna duk matsalolin da Ayuba ya fuskanta a
rayuwarsa ta rashin makoma da faɗawa tarkon rikice-rikicen ƙabilanci duk sun
faru ne sakamakon shi da mahaifinsa ba su ba asalinsu muhimmanci ba. Domin kuwa
da ya san asalinsa, kai-tsaye daga Anambra can zai koma zama cikin ‘yan’uwansa
bayan da aka kashe iyayensa. Amma da yake bai san ina zai dosa ba, sai ya sake
nausawa duniya.
5.1.4 Nuni da Kyawawan Ɗabi’u
A cikin littattafansa, ALA yana ƙoƙarin faɗakar da al’umma kan
kyawawan ɗabi’u. Misali, a labarin Tarzoma, tauraron labarin wato
Ayuba a zamansa na Kaduna, ya bayar da labarin yadda rabuwarsu da Sarkin Fawan
da ya zauna a wajensa a kasuwa ta kasance cikin kewar juna, sakamakon kyawawan
ɗabi’unsa:
Sannu a hankali muka sanya ranar tafiya, a lokacin ne kuma na je
na yi bankwana da Sarkin Fawa, ina kuka yana tausar zuciyata tare da shi mini
albarka, Sarkin Fawa ya ji ɗadin zama da ni matuƙa saboda biyayyata da riƙo da
sallah ga ganin girman na gaba, kuma har ya zuwa lokacin barina ba ni da abokin
sa-in-sa, balle faɗa.” (Tarzoma, shafi na 23).
A nan ALA ya nuna muhimmancin riƙo da kyawawan ɗabi’u irin su
biyayya da girmama na gaba da zaman lafiya da riƙo da addini, waɗanda su ne
ƙashin bayan zama lafiyar da Ayuba ya yi da Sarkin Fawa a Kaduna har suka rabu
cikin kewar juna.
5.1.5 Nuna Damuwa da Halin da Ƙasa Take Ciki
Ko a waƙoƙinsa, ALA ya shahara wajen damuwa da halin da ƙasa take
ciki, musamman sha’anin mulki da siyasa da tattalin arziƙi da tsaro. An lura
cewa a rubutaccen labarinsa ma haka batun yake, yana tsarma irin waɗannan
saƙonni domin faɗakar da al’umma muhimmancin kishin ƙasa. Misali, a
littafin Baƙar Aniya 1, a tattaunawar Auwalu da Hawwa’u,
Auwalun ya nuna damuwa da irin halin da ƙasar Nijeriya take ciki, inda ya ce:
Yau a duniya mun makara,
mun zama koma baya, a harkar ƙere-ƙere (technology). Bayan kuma Allah ya
albarkace mu da komai na mu tafi kafaɗa-da-kafaɗa da sauran ƙasashen duniya.
Ƙasashen da suka zama (super powers) ƙashin bayan arziƙinsu a yau (Technology).
Da akwai ƙasar da ba su da isasshiyar rana, Nijeriya muna da ikon ƙere-ƙere, ta
(sun light) akwai ƙasar da ba ta noma, akwai ƙasar da ba su da ruwa,
akwai ƙasar da ba su da ma’adinai na ƙarƙashin ƙasa, ke hatta fatar dabbobin
Nijeriya ta fi ta sauran ƙasashen duniya nagarta, babu abin da Allah ya rage mu
da shi, face mu muka tauye kanmu, muka tare a ɓangare ɗaya, a ɓangare ɗayan ma
shugabanninmu kansu suka sani da ‘ya’yansu.
(Baƙar Aniya 1, shafi na 6-7).
Daɗin daɗawa, a littafin Tarzoma marubucin ya
kawo irin wannan saƙon faɗakarwa kan halin da ƙasa take ciki. Misali, yayin da
Ayuba yake ba Aminuddeen labarin rayuwarsa cewa ya yi:
Zan ba ka cikakken labarina Aminuddeeen, ko domin ka yi amfani da
damar da Allah ya ba ka ta rubutu, ka isar da saƙon gurin al’umma, wala’alla
yin haka zai iya zame wa mutanen arewacin Nijeriya darasin da zai sa su
fuskanci tsari da mulki da mu’amalar da ta cancanci rayuwarsu. Rayuwata kacokan
tana ɗauke ne da saƙonni masu fa’ida, ga shugabanni da talakawa na ƙasarmu baki
ɗaya. (Tarzoma, shafi na 8).
Ire-iren waɗannan saƙonni suna jaddada yadda ALA ya damu da halin
da ƙasa take ciki, domin haka yake faɗakar da al’umma cikin rubuce-rubucensa na
labarin Hausa.
6.0 Kammalawa
Alƙiblar wannan takarda ita ce nazarin ayyukan ALA na rubutattun
ƙagaggun labarai, duk da cewa an fi sanin sa a fagen waƙa. Da yake masu
iya magana sun ce ‘tushiya mafarin dawa’, shi ya sa wannan maƙala ta yi
nazarin rawar da Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya taka a fagen kiɗan rubutaccen
labarin Hausa. An nazarci yadda ALA ya kasance marubuci kafin mawaƙi,
tare da bayyana gurbinsa cikin marubutan Hausa. An kuma kawo sharhin rubutaccen
labarinsa da saƙonnin da suka yi karakaina a cikin littattafansa. An bi diddigi
an fito da gudummawarsa fili a fagen rubutaccen labarin Hausa, inda a nan ne ya
fara baje-kolin fasaharsa a adabance kafin waƙa. Nazarin ya tabbatar cewa akwai
auratayya tsakanin saƙonnin da suke kimshe cikin littattafan ƙagaggun labaran
da ALA ya rubuta da kuma waƙoƙinsa.
Manazarta
Abubakar, A. L. (2002). Baƙar Aniya. U.P. Printers and
Publishers.
Abubakar,
A. L. (2002). Baƙar Aniya 2. U.P. Printers
and Publishers.
Abubakar,
A. L. (2003). Tarzoma. Assabir
Publication.
Abubakar,
A. L. (2005). Sawaba. Iya Ruwa Publishers.
Abubakar,
A. L. (2005). Cin fuska. Iya Ruwa
Publishers.
Abubakar,
A. L. (2005). Cin fuska 2. Iya Ruwa
Publishers.
Abubakar,
A. L. (2005). Jirwaye. Assabir
Publication.
Barista,
M. L. (2011). Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar Alan
Waƙa: Littafi na ɗaya. Iya Ruwa Publishers.
Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya. (2006). Ƙamusun
Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.
Dikko,
S. S. (2010). Uwa a Bahaushiyar al’ada: Nazarin
mu’amalar uwa da ɗa cikin waƙar Ummina ta Aminu Ala (Kundin digiri na
ɗaya). Jami’ar Usumanu Ɗanfodiyo.
Encyclopaedia Britannica. (1943–1973).
Giɗaɗo,
H. A. (2012). Tasirin zamananci kan al’adun
Hausawa: Nazarin mu’amalar aure tsakanin mata da miji cikin waƙar Gizo-gizo ta
Ala da Fati Nijar (Kundin digiri na ɗaya). Jami’ar Jihar Kaduna.
Isah,
Z. (2014). Jiga-jigan Hausa a bakin mawaƙin Hausa: Waiwaye a kan waƙoƙin ALA na
Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau. In S. M. Gusau et
al. (Eds.), Garkuwan adabin Hausa: A
festschrift in tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Ahmadu Bello University
Press Limited.
Malumfashi,
I. (Ed.). (2019). Labarin Hausa a rubuce:
1927–2018. Ahmadu Bello University Press Limited.
Mujaheed,
A. (2019). Bugun gaba a waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). In B.
Zulyadaini (Ed.), Yobe Journal of Language,
Literature and Culture (YOJOLLAC) (Vol. 7). Yobe State University.
Mukhtar,
I. (2004). Jagoran nazarin ƙagaggun labarai.
Adamu Joji Publishers.
Rogo,
M. S. (2013). Kiɗa da waƙar Hausa jiya da
yau: Kamanci da bambanci tsakanin waƙar Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta Alhaji
Mamman Shata Katsina da ta Aminu Ladan Abubakar Ala (Kundin digirin
farko). Jami’ar Jihar Kaduna.
Sabe,
B. A. (2011). Adabin kasuwar Kano: Nazari da
sharhi game da ƙagaggun labaran Hausa, 1984–2008 (Kundin digiri na biyu).
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Shehu,
I. (2011). Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) a
tsakanin sha’irci da ƙagaggen labari (Departmental seminar paper). Kaduna
State University.
Yakasai,
S. A. (2012). Some major themes of Hausa
responsorial songs in Aminu ALA’s performance (Conference paper). Bayero
University Kano.
Yakasai,
S. A. (2014). Nazarin harshen farfaganda cikin siyasar Kudanci da Arewacin
Nijeriya cikin waƙar ALA ta Rajista. In S. M. Gusau et al. (Eds.), Garkuwan adabin Hausa: A festschrift in tribute
to Abdulƙadir Ɗangambo. Ahmadu Bello University Press Limited.
[1] A daidai wannan zangon rayuwa ne ɗaliban
UPE, shirin Gwamnatin Tarayya da aka soma daga 1976 domin ba kowane yaro damar
samun ilimin furamare kyauta, suka fara shiga kasuwar rubutu da karatu da
rububin abubuwan karantawa, domin ɗaliban farko na wannan shiri sun baro
firamare a shekarar 1982, daga wannan lokaci har zuwa 1984, an yaye dalibai har
kashi hudu. Saboda haka an samar da sababbin makaranta da suke buƙatar abin
karantawa.
Haka wannan zango ya zo
daidai da lokacin da babban kamfanin wallafa da dab’i a ƙasar Hausa wato NNPC
ya soma shiga tasku, ya soma sukurkucewa da neman durƙushewa. A daidai wannan
lokaci kamfanin NNPC ya daina buga littattafan hira da nishaɗi, bayan kuma ga
dubban matasa da aka yaye daga shirin na UPE sun antayo cike da shauƙin
irin wadannan littattafai da babu su.(Abu Sabe, 2008; 2018).
[2] Wato rubuce-rubucen littattafan Adabin Kasuwar Kano (AKK)
[3] Wasu manazartan suna bayyana Adabin Kasuwar Kano (AKK) da
sunan littattafan soyayya la’akari da cewa soyayya ce ta mamaye kaso mafi tsoka
na jigogin littattafan. Saboda haka, idan ALA ya bayyana cewa ya kasance
marubucin so da ƙauna, kenan ya jaddada cewa shi marubucin AKK ne.
[4] A duba tattaunarwar ALA da marubuci Ado Ahmad
Gidan Dabino ta hanyar saƙon wayar salula, ranar 10/11/2012 da misalin
ƙarfe 11:26 na dare. Kamar yadda Gidan Dabino ya kawo a cikin (Malumfashi,
2018).
[5] Har zuwa lokacin da aka kammala wannan takarda
littafin Ceto Ko Cuta bai zo hannu ba, ballantana a
fayyace shekarar bugunsa da abin da ya ƙunsa.
[6] Hakan ba ya rasa nasaba da cewa bai daɗe ana damawa da shi a fagen rubutaccen labari ba, kuma an fi jin ɗuriyarsa a fagen waƙa, sa’annan littattafan nasa ba su shahara kamar waƙoƙinsa ba.
.jpeg)
1 Comments
Allah ya kara basira.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.