Ticker

6/recent/ticker-posts

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (1)

NA

ABDULRAHMAN BALA

Taubasantaka

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki ga mahaifina Alh. Bala Garba B.G Tsafe da fatar Allah saka masa da alkhairi, da kuma mahaifiyata Hajiya Zulfa’u Sani Tambaya Tsafe da kuma kakana Alh. Sani Tambaya Tsafe da Sauran ‘yan uwa da abokan arziki.

GODIYA

Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai da ya ba ni ikon kammala wannan bincike cikin nasara, tare da yabo ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da Sahabbansa, da kuma mabiyansa har zuwa ranar ƙarshe.

Ina godiya tare da girmamawa ga Malamina Malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi wanda ya taimaka matuƙa wajen gudanar da gyare-gyare na wannan bincike da ba da shawarwari da kuma haƙuri tare da ba da gudummuwa ta ɓangoriri mabambanta, Allah ya saka masa da mafificin alkhairi amin.

 

Haka kuma ina miƙa godiya ga shugaban sashe Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, Dr. Nazir Abbas Ibrahim, da sauran Malaman Sashe kamar Farfesa Balarabe Abdullahi, Farfesa Muhammad Lawal Amin, Farfesa Magaji Tsoho Yakawada, da Malam Musa Abdullahi da Malam Isah S. Fada da sauransu, da fatar Allah ya saka musu da alkhairi.

 

Daga ƙarshe ina miƙa godiya ga Nasiru Hassan, da Ahmad Muhammad Kabir, da Bashar Isyaka, da Aliyu S Ibrahim, da Mustapha Sa’idu, da Abubakar Hassan, da Nura Sani, da Hisbullah Ɗanlami, da Amina Abubakar, da Ɗayyaba Mustapha, da Hassan Galadima, da kuma Abdulrashid S/Pawa.

 

Har wa yau ina mika godiya ta musamman ga Abbati Muhammad da ya buga wannan aiki cikin na’ura mai ƙwaƙwalwa har ya zuwa kammala wannan bincike. Shi ma Allah ya saka masa da alheri, amen.

Post a Comment

0 Comments