Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (6)

Na

AMINU MURTALA

 

Tarihin Hausawa

BABI NA BIYAR

Kammalawa

 Kamar yadda mai bincike ya yi bincike a kan rubuta wannan littafin wato kundin digirin farko kan abun daya shafi tarihin masarautar kwatarkwashi yadda shi kanshi garin yake da yadda ya samu a kan haka mai bincike ya raba aikinsa zuwa babi-babi tun daga na ɗaya har zuwa na biyar.

A babi na ɗaya mai bincike ya yi Magana kan gabatarwa da godiya da manufar bincike da dabarun bincike da muhimmanci bincike da akan yi bayaninsa cikin rubutun wannan littafin.

A babi na biyu mai bincike ya yi bayani kan bitar ayyukan da suka gabata.

A babi na uku mai bincike ya yi rubutu kan ma’anar sarauta dasu waye masarauta da sauye sauyen sa kuma da nadawa duk mai binike ya yi bayaninsu a cikin wannan littafin.

A babi na hudu mai bincike ya yi rubutu kan takaitaccen tarihin kasar kwatarkwashi gabanin jihadin shehu danfodiyo da takaitaccen tarihin mai martaba sarkin kwatarkwashi da tsarin sunayen sarakunan ƙasar kwatarkwashi da bukin hawan dutse da bukin wasan baura da nadewa ƙanda duk suna cikin wannan littafi.

Waddannan abubuwa da littafin kundin digirin farko na (B.A Hausa) ya kunshi tarihin masarautar kwatarkwashi.

Manazarta

Tuntuɓi masu gudanarwa.

Post a Comment

0 Comments