Ticker

6/recent/ticker-posts

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (2)

NA

ABDULRAHMAN BALA

 

Barkwanci

BABI NA ƊAYA

SHINFIƊA

1.0 GABATARWA

Ƙasar Hausa wuri ne inda jama’ar Hausawa suke zaune, kuma tana shimfiɗe ne a Arewacin Nijeriya da kudancin Jamhuriyyar Nijar. (Adam 1978). Harshen Hausa shi ne mazauna wannan yankin na asali, da shi suke amfani wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum. Kamar hulɗoɗin kasuwanci da na auratayya da sauran al’amurran rayuwa.

 

Hausawa suna kewaye da maƙwabta daban-daban waɗanda ba Hausawa ba da kuma suke da nasu Harshe da al’adunsu da suke gudanar da harkokinsu. Amma mafi yawan lokacin sukan cuɗanya da Hausawa domin yin wasu hulɗoɗi. Wannan ne kan haifar da shaƙuwa da fahimtar juna har wani lokaci auratayya ta kasance tsakaninsu. A nan ne sukan koyi harshen Hausa da kuma al’adunsu.

 

Hausawa dai kamar yadda aka san su, mutane ne masu yaƙini ga duk abin da suka sa a gabansu da sauƙin kai, sannan an san su da rashin nuna wariya ko ƙyama ga kowa da kowa. Hakan ya sa suka shiga cikin mabambantan al’ummomi su yi mamaya sosai ga abokan hulɗoɗinsu da ba Hausawaba. (Idris: 1946).

 

Hausawa sun bai wa harshensu da al’adunsu muhimmanci matuƙa, addininsu kaɗai sukan fifita a kan harshensu da al’adunsu.

Zamfarawa mutane ne kuma Hausawa, ma’ana su ma wani yanki ne na wata al’umma daga cikin ƙasar Hausa. Kuma ba su da wani harshen da yafi harshen Hausa, a wurinsu. Domin da shi suke sadarwa, da kasuwanci da sauran hulɗoɗinsu da sauran ƙabilu daban-daban.

 

Zamfarawa suna maƙwabtaka da al’ummomi daban – daban waɗanda ba Hausawa ba. Daga cikinsu, akwai Fulani, Barebari, da kuma dakkarawa. Sai dai a nan za mu yi bayani ne a kan wata ‘yar alaƙa da ke tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa, wato “TAUBASANTAKAR BAZAMFARE DA BADAKKARE.

 

Dakkarawa dai kamar yadda aka sani wata al’umma ce waɗanda suke ba Hausawa ba. Ma’ana suna da nasu harshe da suke sadarwa da shi, kuma suke gudanar da al’amurran rayuwarsuta yau-da-kullum. Waɗannan mutane a halin yanzu suna zaune ne a cikin jihar Kebbi a ƙaramar hukumar mulkin Zuru. Sai dai nan gaba kaɗan a cikin wannan bincike za mu gano asalinsu, da kuma wurin da suka fara zama, kafin su kasance a inda suke a yau.

 

Dakkarawa kamar yadda muka yi bayani a baya, su ma suna cikin maƙwabtan Zamfarawa, kuma suna tafiyar da hulɗoɗinsu da dama tare da Zamfarawa. Hasali ma sun cuɗanya sosai da Zamfarawa har ta kasance waɗansu, (Dakarkarin) sukan baro wurin zamansu na gado su dawo ƙasar Zamfara su zauna domin gudanar da sana’o’insu. Ko kuma a sanadiyar wani dalili sai wasu su yi ƙaura zuwa Zamfara, haka kuma auratayya kan kasance a tsakaninsu da Zamfarwa. Dalilin haka ta sanya wasu al’adu da ɗabi’un waɗannan al’ummomi suka cuɗanya dana juna. Sai dai na Zamfarawa su suka fi rinjaye domin kuwa wasu daga cikin Dakarkarin sukan bar nasu ne su ɗauki na Hausawa, kamar aure, Dakarkaru sun bar al’adarsu ta noma kafin ka auri mace, inda suka ɗauki ta Hausawa kawai sadaki ake biya ba sai an yi noma ba.

 

Shi wannan bincike ya yi ƙoƙari ne ya binciko yadda taubasantaka ta samo asali ko tushe a tsakanin Bazamfare da Badakkare (Zamfarawa da Dakkarawa), ta yadda za a fito da komai fili, ta hanyar bayyana duk wata hanya da taubasantakar ta afku a tsakanin waɗannan al’ummomi guda biyu. Haka kuma wannan bincike zai bai wa manazarta dammar dubawa tare da aunawa don tabbatar da duk wani hasashe da aka yi a kan wani abu da wataƙila zamani ne ya kawo shi, ta yadda har wannan taubasantaka ta yi tasiri a tsakanin Bazamfare da Badakkare.

 

1.1 MANUFAR BINCIKE

Wannan bincike na nufin nazarin dalilan da suka haddasa taubasantakar da ke tsakanin waɗannan al’ummomi guda biyu, wato Zamfarawa da Dakarkari.

 

Hausa na cewa “ruwa ba ya tsami banza” ko kuma su ce “Ba banza ba kuɗa kabin walki”. Ma’ana ba haka ƙaddam, al’ummomi suke zama taubasan juna ba, a a dole sai da wasu dalilai ko faruwar wani abu a tsakanin waɗannan jinsunan al’ummomin guda biyu, sannan a samu taubasantakar a tsakaninsu.

 

Wannan bincike ya ɗauki aniyar yin nitso a cikin waɗannan al’ummomi domin yin farautar gano asalin taubasantakar da ke tsakaninsu. Don haka aikin zai dubi wasu muhimman abubuwa, kamar asalin kowace al’umma a cikinsu da alaƙar da ke tsakaninsu. Sai kuma asalin taubasantakarsu, wato inda ta samo asali. Sannan a kawo cikakken bayanin tasirin taubasantakar Bazamfare da Badakkare ga raya al’adun Hausawa da harshensu.

 

Daga nan sai binciken ya samar da abubuwan amfani kamar su shawarwarin da ke wanzar da haɗin kan ƙasa, wato a tsakanin ƙabilu daban-daban na Najeriya.

 

1.2 DALILIN BINCIKE

Dalilin gudanar da wannan bincike shi ne, domin mu gano ko mu zaƙulo asalin yadda Bazamfare da Badakkare suka zama taubasan juna, wato musan asalinta da kuma dalili ko dalilan da suka haifar da taubasantakar. Domin kuwa ita taubasantakar tana matuƙar yin tasiri a tsakanin al’ummomin da suke taubasan juna. Saboda duk irin yadda taubashi yake cikin tsananin baƙin ciki, ko damuwa ko yake cikin yanayin fushi da zarar yaga taubashinsa dole ya yi ƙoƙarin ɓoye wannan yanayin da yake ciki, tare da sakin fuska don taƙaita zolayar da za ya yi mashi.

 

Haka zalika taubasantaka tana ƙara ɗanƙon zumunci a tsakanin taubasai, da kuma cusa musu soyayyar juna. Don haka yana da kyau matuƙa jama’a su fahimci taubasantakar da ke tsakanin waɗannan al’ummomi guda biyu.

 

Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa na yi tunanen aiwatar da aikin binciken domin jama’a su fahimci yadda Zamfarawa suka zama taubasan Dakarkari.

 

1.3 FARFAJIYAR BINCIKE

Wannan bincike zai taƙaita ne a kan taubasantakar da ke tsakanin Zamfarawa da Dakarkari. Ma’ana dai za a kalli al’ummar Dakarkari tun daga inda suka samo asali tun fil’azal da kuma yadda suka haɗu da zamfarawa, ta fuskar zamantakewa da junansu.

 

Haka kuma suma maƙwabbtansu Zamfarawa, za a dubi nasu asalin da kuma gano irin abubuwan da suka yi tasiri ko suka faru a tsakaninsu da taubasansu, ko ince maƙwabtansu (Dakarkari), da kuma zaƙulo abin da da ya haifar da taubasantakar da ke tsakaninsu. Sannan kuma musan yanayin ko yadda ƙasar Zamfara take tun wancan lokacin har zuwa yau.

Lokacin da wannan bincike zai ɗauka shi ne mafi a’ala domin a wannan tsakani ne ingantattun bayanai kan samu ko dai a rubuce ko ta hanyar samun wani mutum wanda ya san tarihin abubuwa ko ma wanda yak e da haƙiƙanin yadda al’amarin yake faruwa a ƙasar Zuru. Misali yankin wasagu da Fakai waɗanda suke wurare ne da Dakarkari suka mamaye ko suke zaune. Wato a nan ne ake tsammanin a sami cikakken tarihin Dakarkari domin aiki da shi. Daga nan kuma sai a fito da asali ko dalilin yadda taubasantaka ta samu a tsakanin Bazamfare da Badakkare.

 

Haka kuma su ma maƙwabtansu, wato Zamfarawa za a iya samun tarihinsu a rubuce ko kuma a sami wani mutum masanin tarihi sosai, musamman wanda yake zaune a ƙasar Bukkuyum ta cikin ƙaramar hukumar mulki ta Bukkuyum a jihar Zamfara. Ko kuma a samu mutumin da ya san tarihin abubuwan da suka wakana, wanda ya ke zaune a ƙasar Zurmi, ta jihar Zamfara. A haka ne za a iya samun damar sanin asalin taubasantakar da ke tsakaninsu.

 

Dalilin da ya sa na kawo ƙasar Bukkuyum da Zurmi na Jihar Zamfara, shi ne, wasu masana ko ince manazarta, suna ganin cewa can ne asalin Dakkarawa ya fito. Binciken zai taƙaita a waɗannan yankuna na jihar Kebbi da Zamfara domin a nan ne waɗannan al’ummomi suke zaune.

1.4 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Domin ganin haƙa ta cimma ruwa, wato mu ga cewa wannan bincike ya tabbata, kuma da ganin cewa ya samu karɓuwa a wurin manazarta ko makaranta, za a yi amfani ne da wasu dabaru don gudanar da wannan bincike har a ga an tabatar da cewa, an kammalashi.

 

Da farko dai za a duba bugaggun littattafai da mutane da dama suka rubuta masu alaƙa da aikin. Sannan za a nemi kundayen bincike na neman digirin farko wato (B.A) da na biyu (MA) da kuma na uku (PhD) don a sami nasarar kammalawa wannan bincike cikin sauƙi.

 

A lokacin da ake gudanar da wannan bincike, za a ƙara himma wajen halartar ɗakunan karatu daban-daban, na jami’o’i da na kwalejojin ilimi da makamantansu.

 

Haka zalika da mujallu da takardun da aka gabatar na ƙara wa juna sani a tarurukan ƙarawa juna sani daban-daban da suka shafi tarihi da al’adu na al’ummomi, musamman Hausawa. Haka kuma za a kai ziyara wasu garuruwa da ake sa ran can ne asalin wurin da ƙabilun Zamfarawa da Dakarkari suka fara zama ko ɗaya daga cikin ƙabilun suka fara zama, domin ana sa ran cewa ba za a rasa waɗansu alamomi ko waɗansu mutane waɗanda suka yi zamani tare da su ba. Idan har aka samu irin waɗannan mutanen to za a yi fira da su don a sami wasu muhimman bayanai, waɗanda za su iya zama ginshiƙai na tattara bayanai a wannan bincike.

 

Biyar waɗannan hanyoyi da na zayyana a baya, wajen gudanar da wannan bincike, za su taimaka matuƙar gaske wajen kafa hujjoji gamsassu, waɗanda za su taimaka don binciken ya samu karɓuwa a wurin manazarta da masana tarihi.

 

1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE

Duk wani abu da ake bincike ko ake gudanar da bincike a kansa, to tabbas wannan abun yana da matuƙar muhimmanci. Domin kuwa ana yin bincike ne don a gano, ko don a zaƙulo wani abu da ba a san shi ba. Kuma ana da buƙatar a san shi, domin muhimmancinsa ko tasirinsa ga al’umma.

 

Shi ma wannan bincike da ake gudanarwa, yana da irin nashi muhimmanci ga al’umma, musamman ɗaliban ilimi, dalilina na faɗar haka shi ne, muddin aka samu damar kammala wannan bincike, kuma aka cimma abin da ake so, to ina sa ran binciken zai iya zama wata yar fitilar haskawa ga duk wani ɗalibin ilimi da zai gudanar da bincikensa a wani fanni mai alaƙa da wannan aiki ko makusancin wannan fanni.

 

Wannan bincike yana da muhimmancin gaske, kuma zai taimaka sosai wajen sanin asalin tarihin waɗannan al’ummomi guda biyu wato Zamfarawa da Dakkarawa dangane da abin da ya shafi taubasantakar da ke tsakaninsu.

 

Yana da kyau a ce an san muhimmancin kalmar taubasantaka, da kuma irin abubuwan da ta ƙunsa ba wai dole sai wannan taubasantakar da ke tsakanin waɗannan ƙabilun guda biyu (Bazamfare da Badakkare) ba.

 

Saboda haka wannan bincike ya ɗauri aniyar yin nitso a cikin waɗannan al’ummomi guda biyu domin ya gano waɗansu abubuwa masu muhimmanci waɗanda ya kamata a ce an sansu, kuma an san asalinsu da abin da ya assasa alaƙarsu kamar irin tarihinsu da yadda alaƙa ta ƙullu a tsakaninsu. Haka kuma da sanin abin da shi ne musabbabin yin wannan bincike, wato “Taubasantakar da ke tsakanin Bazamfare da Badakkare.

 

1.6 HUJJAR CIGABA DA BINCIKE

Hujjar cigaba da gudanar da wannan bincike shi ne domin zaƙulo asali ko tarihin yadda taubasantakar Bazamfare da Badakkare ta samo asali da kuma sanin silar abin da ya haifar da taubasantakar a tsakanin waɗannan al’ummmi guda biyu (2) (wato Zamfarawa da Dakkarawa). Dole sai an bi ta hanyar yin amfani da tarihin waɗannan al’ummomi ne guda biyu, sannan za a iya gano tushe ko asalin yadda taubasantakar ta samu a tsakaninsu. Saboda shi tarihi wani muhimmin abu ne wanda yake ƙunshe da abubuwa mabambanta game da al’ummomi tun daga asalinsu da yadda suke gudanar da rayuwarsu da bukukuwansu, da suturarsu. Hakan zai tabbatar mana da cewa duk wata al’umma ta duniya wadda ta isa, kuma ta ke ji da kanta, to idan aka bincika za a ci karo da tarihinta, ya sami canje-canje daga nan zuwa can.

 

Zamfarawa da Dakarkari ba a ɓoye suke ba a wannan ƙasa tamu Nijeriya, amma rubuce-rubuce a kan waɗannan al’ummomi guda biyu ba su yawaita ba sosai kamar yadda ya kamata. Wannan shi ne hujjar da ya sa zan cigaba da wannan bincike. Saboda a ɗan wannan tsakanin ne in gantattun bayanai za su samu. Wato za a samu bayanan ne ko dai a rubuce ko kuma ta hanyar samun wani mutum wanda ya san tarihin abubuwa ko ma a samu mutumin da ya san haƙiƙanin yadda al’amura suka faru a ƙasar Zamfara da Kebbi; misalin yankin Bukuyum da Zurmi, nan ne ake sa ran asalin Zamfarawa waɗanda suka zauna tare da Dakarkari suka fito, sannan sai a samu wani wanda yake da haƙiƙanin tarihin al’amarin da ya faru a ƙasar Zuru. Misali, yankin Wasagu da fakai domin wurare ne da Dakarkari suka mamaye. Don haka waɗannan wurare da aka ambata ake tsammani a sami cikakken tarihin waɗannn al’ummomi guda biyu, wato Zamfarawa da Dakkarawa. Daga nan kuma sai a taɓo inda taubasantakar ta su ta samo asali, tare da gano ko sanin abin da ya haifar da ita. Babbar hujjar da ya sa za a yi aiki tuƙuru wajen sanin ko gano tarihin kowace al’umma a cikin waɗannan al’ummomi guda biyu, shi ne, saboda kasancewarsu al’ummomi ne masu matuƙar muhimmanci a tarihin ƙasar Hausa. Don haka yana da kyau matuƙa jama’a su fahimci ko su san tarihinsu da kuma abin da ya haifar da taubasantaka a tsakaninsu. Kamar yadda aka san waɗansu abubuwa dangane da sauran al’ummomi irinsu yarbawa da al’ummar Ibo da Fulani da sauran ire-irensu. Saboda haka wannan bincike zai mayar da hankalinsa wajen fito da asalin taubasantaka dake tsakaninsu.

 

1.7 BITAR AYYUKKAN DA SUKA GABATA

Gano ko binciko ko bayyana wani abu da ke tsakanin al’umma daban-daban ba wani sabon abu ba ne domin masana da manazarta da dama sun daɗe suna aiwatar da ayyuka wajen binciko wani abu da suke son tabbatarwa akan wasu al’ummomi.

 

Masana da dama sun yi rubuce-rubuce masu yawa a kan kowace al’umma, daga cikin waɗannan al’ummomi guda biyu (Zamfarawa da Dakkarawa); misali. Adam (1978) “Asalin Dakarawa da Dukkawa iri ɗaya ne da na al’ummar muryam”, saboda suna ganin cewa al’ummomin Dakarawa da Dukkawa sun faru ne a lokacin da waɗansu suka yi ƙaura daga ƙasar Hausa, suka zauna a wani wuri da babu kowa, a tsakanin Yawuri da Zamfara, suka rasa harshensu na Hausa suka ƙirƙiri wani sabon harshen da hanyoyin gudanar da rayuwarsu.

Shi kuma Robins (1967) cewa ya yi a kan tarihin dangantakar harsuna ko ƙabilu da suke ‘yan tushe ɗaya da marubutan turai suka yi, ya fara ne daga Dante (1265 – 1321).

 

Mainasara S. (2001) Bautar Magiro a Zamfara; daga ciki akwai inda ya ɗan yi tsokaci a kan Zamfarawan asali ya ce “Zamfarawan Asali sun fito ne daga Dutsi a ƙaramar hukumar mulki ta Zurmi, kuma su ‘ya’ya ne ga Dakka (mai yawon farauta). Don haka Dakka mahaifi ne ga Zamfarawa.”

 

Shi ma Umar Muhammad (2010), ya yi rubutu ko bincike a kan “Tau basantakar wamakko da Yabo,” a kundin digirinsa na farko (BA), in da ya bayyana waɗansu muhimman dalilan da suke haifar da taubasantaka a tsakanin al’ummomi, ya ce: Daga cikin abubuwan da suke haifar da taubasantaka akwai, zumunci. Misali a samu wa da ƙanwa ‘yan ɗaki ɗaya, idan suka yi aure suka haifi ‘ya’ya, to ya’yan nan nasu za su zama taubasan juna saboda kasancewar su ‘yan wa da ‘yan ƙanwa. Irin wannan taubasantaka al’ada ta haifar da ita.

 

Ya ƙara da cewa akwai wasa ta taubasantaka tsakani jika da kaka. Irin wannan wasan ba a cikin gida kawai take tsayawa ba, wani lokaci takan zama silar haɗa al’ummomi su zama taubasan juna.

 

Abdullahi M. (2002) ya yi aiki a kan tasirin magungunan Gargajiya na Hausa a kan na Dakarkarin ƙasar Zuru, ya yi taƙaitaccen bayani a kan Dakarkarin kasar Zuru. Ya ce “anihin Dakarkarin ƙasar Zuru hijira suka yo daga ƙasar Katsina, har ana kiransu da wani suna “Mutanen Riɓah” dalilin kiransu da wannan suna shi ne, lokacin da suka baro Katsina, sun zauna ne a wani gari ko ƙauye mai suna Ribe, a arewacin Zamfara. Don haka ba a rasa wata alaƙa tsakaninsu da Zamfarawa.

 

Muhammad (1982) a cikin wata takarda da ya gabatar a jami’ar Bayero da ke Kano, ya yi magana a kan “Haɗuwar Dakarkari da Hausawa,” ya ce Huɗɗar kasuwanci ita ce ta haɗa alaƙa tsakanin Dakarkari da Hausawa, musamman Katsina da Zamfara da ƙasar NUPE. Ya ƙara da cewa, Katsinawan Laka sun fara zama a kongon wasagu daga nan suka zarce zuwa Wasagu kai tsaye.

 

Su kuma P.G. da Harris (1938) sun ce “Zamfarawan Dutsi a gundumar Zurmi ‘yan uwan Dakarkari ne, su kuma Dakarkarin jikoki ne ga Dakka, wato mai yawon farautar nan da aka faɗi a ƙasar Bukuyum.

 

Bugaji (1985); cewa ya yi “Asalin Dakarkari ya fito ne daga ƙasar Bukkuyum.” Inda ya ƙara da cewa, a wancan lokacin Dabai daji ne, wanda ya ke cike da itatuwa da kuma namun daji. To sai mafarauta suka fara zuwa suna shiga don yin farauta. Lokacin da wannan mutumin ya zauna sai wurin ya zama gari. Bugaje ya cigaba da cewa, har zuwa farkon ƙarni na goma sha tara, sarkin Bukuyum shi ke naɗa hakimi da Dabai wanda daga baya aka fi sani da suna marafan Dalai (Kasancewar asalinsu Bukkuyum ne).

 

Haris (1938) ya ce su Dakarkari sukan yi wa yaransu maza tsage bayan wata uku da haihuwa, mata kuma shekara huɗu. Amma ko a cikin Hausawa, wani lokaci sai bayan mutum ya girma ne akan yi masa tsaga. Amma an fi yin haka lokacin da mutum yake jinjiri domin ya fi sauƙi, kuma an tabbatar ya fi saurin warkewa.

 

Idrisu (1946) ya ce “akwai auratayya a tsakanin Zamfarawa da Dakarkari tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, har ma daga cikin iyalan Sarkin Zuru da na Dabai akwai Hausawa. Ya yi wannan bayani ne a wurin taron ƙara ma juna sani a jami’ar Usmanu Ɗanfodio da ke Sokoto.

 

Nadama G. (1986) ya yi aiki a kan “yanayin ƙasar Zamfara” a kundin neman digirinsa na uku (Ph.D) a jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ya ce “ƙasar Zamfara ƙasa ce mai faɗin gaske,, wadda take ƙunshe da al’ummomi daban-daban gami da dajujjuka da kuma tsaunuka, ga kuma itatuwa iri iri a cikinta. Sannan kuma ƙasar Zamfara tana da gulabe, kuma ƙasa ce mai daɗin noma, ya cigaba da cewa ƙasar Zamfara tana maƙwabtaka da garuruwa mabambanta misali Sokoto da Katsina da Kabi da sauran su. 

Sani (1986) “Dakarkari sun haɗu da Zamfarawa tun lokacin da Zamfarawa ba Hausa ce harshensu ba, wanda suke amfani da shi na asali. Ya ci gaba da cewa sun sami harshen Hausa ne a matsayin harshen kasuwanci domin kasancewar Zamfara cibiyar kasuwanci ce kafin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo a ƙarni na goma sha tara a ƙasar Hausa.

 

Gujiya, M. (1987) ya ce “Ƙidayar jama’a da aka yi a can baya a ƙasar nan ta nuna cewa, Dakarkari (wato Lele) sun fi yawa a wuraren da suka kama tun daga peni da senchi zuwa garin zuru har Dabai da Wasagu. Amma garin wasagu ba ya ciki. Ya cigaba da cewa” daga arewa zuwa kudu, ana samun Dakarkari tun daga kyabo har zuwa Tadurga da bedi”.

 

Sakaba (1988) “Farko zuwan maganar Alh. A ƙasar Dakarkari a Zuru an fara ɗora tubalin Kira ga al’umma da su shiga addinin Kirista tun shekarar 1925. Kafin wannan lokacin Dakarkari ba su da wani addini sai ‘yan tsafe - tsafe.

 

Kabiru (1988) “Tarihin ƙasar Zamfara da albarkatunta a kundin neman digirin farko a jami’ar Usmanuu Ɗanfodiyo da ke Sokoto.” Ya ce, “ƙasar Zamfara ƙasa ce mai ɗimbin tarihi, ga kuma tarin albarkatun ƙasa a cikinta. Haka kuma ƙasa ce mai hulɗar kasuwanci da ƙabilu daban-daban misali tarihi ya nuna cewa Zamfarawa sun yi huɗɗar kasuwanci da ƙabilar Dakarkari tun kafin ƙasar Zamfara ta samu ‘yancin kanta na zama (jaha).

 

Isma’ila (1989) “Sana’o’in Zamfarawa jiya da yau, a cikin wannan bincike da ya yi, ya yi ɗan tsokaci a kan asalin Zamfarawa, inda ya ce “asalin Zamfara sun fito ne daga ƙasar Bukuyum, kuma suna da alaƙa mai ƙarfi tsakaninsu da Dakarkari. Domin bincike ya nuna cewa asalin Zamfarawa kakanni ne ga Dakarkarin asali, domin tarihi ya nuna cewa jikan “Dakka” ne asalin Dakarkari”.

 

Haruna (2002) “Tasirin al’adun Hausawa aan na Dakarari” a kundin neman digiri na biyu (MA) a jami’ar Bayaro da ke Kano. “Ya yi bayani sosai kan ƙabilar Dakarkari mazauna ƙasar Zuru, kamar yadda ya ce “Mafi yawan Dakarkari mazauna ƙasar Zuru, masu tsawo (Dogaye) ne waɗanda ba su faye ƙiba ba. Suna da babban kai da haƙora masu kaifi da tsini. Ya cigaba da cewa mafi yawancin Dakarkarin manya da ƙanana, maza da matansu ba su da ƙyuya ko kasawa ga dukkan al’amura. Sannan ya ce; “Dakarkari musamman mazauna ƙauyuka mutane ne marasa tsafta ga jiki da kuma ta gidaje. Ba su da girman kai mutane ne masu ladabi da biyayya.

 

Ni kuma a wannan aiki nawa, zan yi shi ne a kan taubasantakar da ke tsakanin Bazamfare da Badakkare, domin kamar yadda bayanan masana tarihi suka gabata, ya nuna cewa taubasantakar da ke tsakanin waɗannan jinsuna guda biyu ta fi rinjaye ne a kan jikoki da kakanni (jika da kaka) ma’ana Zamfarawa su ne kakannin Dakarkari, kamar yadda nan gaba za a tabbatar da hakan a cikin wnanan bincike.

 

1.8 NAƊEWA

Babban abin buri ga kowane bincike shi ne samun nasara, haka nike fata in ga cewa na samu nasarar kammala wannan bincike, duk da cewa, yanzu aka fara sa hannu. Amma Hausawa sun ce “sannu – sannu kwana nesa.

 

Binciken ya ƙunshi babi biyar ne waɗanda a cikinsu ne manufofin gudanar da aikin suka fito har “haƙa ta cimma ruwa.” Wannan Babi shi ne na farko da ya ƙunshi bayanan ayyukan da suka gabata, bayan an kawo kyakkyawar shimfiɗa don gudanar da aikin, sai hujjar cigaba da bincike da bayanan muhimmancin bincike. Sai farfajiyar bincike da kuma dalilin bincike.  Haka kuma da manufar bincike da hanyoyin bincike, waɗannan su ne abubuwan da aka tattauna a wannan babi.

Post a Comment

0 Comments