Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (5)
Na
AMINU MURTALA
BABI NA HUƊU
4.0
Takaitaccrn Tarihin Ƙasar
Kwatarkwashi
A shekara (1400) ne haddadiyar daular
Katsina ta fara mulkin garuruwan da ke ƙarƙashin daular Zamfara tun farkon mulkin daulolin ƙasar nan ta Hausa. Asalin
garuruwan da ke ƙarƙashin yankin ƙasar Katsina duk a shugabancin sarkin Katsina suke yawancin masu mulkin
garuruwan Katsinawa ne suka yaƙi ɓangaren wata ƙasa sauran kuwa ba yaƙi bane sai zaman lafiya a
tsakanin garuruwan da suke makwabtaka da su sanadiyar haka suke ƙarƙashin mulki ɗaya da garuruwa kamar haka:- Zurmi da Kiyawa da Ƙauran Namoda da Rawayya da
‘Yandoton-Daji da Maru da Bunguɗu da Magami da Dauran da sauransu. Garuruwan farko da ke ƙarƙashin Daular Katsina a can da
bayan masarautar Katsina ta basu wal-walar samun ‘yanci ga waɗannan garuruwan wasu kuma saboda jaruntaka suka
maida yankin ƙasa baya ga sauran garuwan da suke kuɓuta suna nan a matsayin gari-gari kowane ya ɗebi nashi yanki.
Bayan wannan ne aka samu garuruwa
kamar haka:- Tofa da Magami da ‘Yandoton-Daji da Bunguɗu da Rawayya da Ɗan-kurmi da Gada da Maru da sauransu. Wannan ya faru
tun ƙarni na (12-13) an samu ƙasashe da garuruwa a cikin ƙarni na (15-16), wannan kuwa ya faru tun kafin
Jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo waɗannan garuruwa suke a ƙasar Zamfara kuma sune tushen
Zamfara na farko.
Kwatarkwashi gari ne mai daɗaɗɗen tarihi asali da jarumtaka. An samu kafuwar ƙasar Kwatarkwashi a cikin ƙarni na (14) kimanin shekaru
(611) da suka wuce wato (1400) zuwa yau.
Sunan kwatarkwashi dutse da ganuwa in da Maiki ya shahara saboda yawan
duwatsun da Allah ya albarkaci wurin da su.
Garin kwatarkwashi ya yi iyaka da masarautar Mada daga gabas. A kudu maso
gabas kuwa garin ya yi iyaka da masarautar Tsafe. Ta arewa kuwa garin ya yi
iyaka da masarautar Ƙaurar Namoda. Harwa yau garin ya yi iyaka da Gusau babban Birnin Jahar
Zamfara daga yamma.
Sunan kwatarkwashi ta samu asali ne daga wanda ya kafa garin kwatarkwashi
tun farko mai suna Mangul.
Shi wannan mutumin ya yi ƙaura ne daga Katsina a bisa ga sana’arsa ta harbi lokacin sarkin Katsina
Kumayo. Sunan Mangul ya ɓata sanadiyar kyautatawa da
alhairin da yakan kaiwa sarkin Katsina a cikin wani baho da ake kira Kwatashi.
Bisa haka ne sarkin Katsina ya sa masa suna sarkin Kwatashi zuwa Kwatarkwashi.
Tun da aka kafa ƙasar Kwatarwashi ba a taɓa cinta da yaƙi ba, saboda jaruntaka al’ummar wannan gari suna da kyakkyawan jagoranci
da suka samu na shugabanni duk da yawan kawo hari da Namoda da Banaga dan
Bature na Morai suka kai mata. Hasalima dai lokacin mulkin mallaka, kwatarkwashi
ta yi fice sosai inda har ta kai ga ana jin tsoron auka mata ta hanyar hari da
tsangwama da faɗa ko ƙwace.
Cikin wannan halin ne a cikin watan Yuli na (1903) a ka yi arangama da
wasu sojojin turawan mulkin mallaka ƙarƙashin (Captain Wallace Wright) inda suka sha kashi, har daga baya aka ci
kwatarkwashi tarar fam (35). A kan wannan faɗa da nasara da kwatarkwashi ta yi.
4.1 Ƙasar Kwatarkwashi Gabanin Jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo
Ƙasar Kwatarkwashi an kafa ta ne tun ƙarni na (14-15) don ba wannan
zama ne na farko ba amma asalin waɗanda suka kafa garin an ce sun taso ne daga Katsina wato Katsinawa ne. A
farkon yadda zangonsu sun sauka ne a garin “Kofi” sun kuma da daɗe a nan don sun yi kimanin shekaru (560) a nan
yankin kusa da duwatsu. Daga nan ne suka taso zuwa gari na biyu mai suna “Unguwa”
nan ma sunyi kimanin shekaru (560) ne daga nan sai suka matsa a gari na uku mai
suna “Tungai” a nan ma sunyi shekaru (560) kuma shi ne zamansu na ƙarshe a kewayen duwatsu.
A duk inda suka kafa gari ya zama alƙarya kuma har yanzu waɗannan garuruwan da suka fara zama akwai mutane ciki sosai, kuma duk ɗiya da jikoki da tattaɓa kunne ne ke mulkin garuruwan da ƙasar baki ɗaya. Daga tashinsu a garin na uku sai suka matsa gaba a inda suka koma saman
Dutse sun kuma daɗe a can sama suna gudanar da
rayuwarsu yadda ya kamata don sun yi shekara da shekaru kafin su sauko saman
dutsen da gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullun. Shugabansu wanda ya
fara hawa saman duwatsun shi kaɗai ke sama bayan saukowarsu a ƙasa.
An ba garin suna ne daga sunan jagoransu a wannan garin shi ne “Kwatashi”
wai a hau Kwatashi shi ne haye dutse sama daga nan aka bashi suna Kwatashi a
matsayin shugabann garin wato Sarki kenan. Bayan sun sauko ne aka maida sunan
garin ana ce mashi kwatarkwashi har ta zama wani yankin ƙasa mai cin gashin kanta. A nan
ne duk Maguzawan ƙasar Zamfara ke zuwa “Bautar Tsafinsu na Magiro” a duk shekara a ke haɗuwa ranar kasuwar garin.
Wannan buki idan lokacin shi ya yi wato shekara ta zagayo kenan sai an
taru a wuri ɗaya sai a ɗunguma zuwa gidan Sarki don kai gaisuwa gare shi
kuma wannan hanya ita ce mafi sauƙin zuwa wurin Tsafin domin tanan ne a ke hawan Dutse
cikin sauki. Tun daga zuwansu na hawan duwatsun tare da saukowarsu a ƙasan dutsen har zuwa yanzu
masana tarihin ƙasa da nazari tare da bincike sun ce Kwatarkwashi a yanzu ta yi shekaru
(561). Lalle shi wannan garin na ƙarshe ya samu kafuwa ne tun kafin Jihadin Shehu
Usman Ɗanfodiyo a ƙasar Hausa baki ɗayanta.
4.2 Tarihin Mai Martaba Sarkin Kwatarkwashi na Yanzu
Mai Martaba Kwatarkwashi Alh.
Ahmad Umar Sarkin Kwatarkwashi na (28) a jerin sarakunan ƙasar Kwatarkwashi daga (1400)
zuwa yau. Ɗa ne ga Kwatarkwashi Ummaru na III jikan Dabo ne kuma tsatson Kwatashi ne
sarkin kwatarkwashi na farko daya cika shekaru (59) a bisa mulki ko sarautar ƙasar Kwatarkwashi, bugu da ƙari shi ne Emir na farko a
masarautar Kwatarkwashi.
An haifi mai Martaba a nan gidan Sarautar Kwatarkwashi kimanin shekara
(90), (1928). Mahaifin, mai Martaba Kwatarkwashi Ummaru III shi ne Sarkin
Kwatarkwashi kuma ya yi Sarautar Kwatarkwashi har na tsawon shekau (33).
Bisa tsarin tarbiyar Musulunci da al’adunmu na Hausawa mai Martaba ya yi
koyon karatunsa na Ƙur’ani tsakanin (1934-1941), ya fara ne da karatu a Makarantar Malam
Rabi’u a nan garin Kwatarkwashi.
Daga nan ya koma samawa, in da yayansa ke sarautar sarkin yaƙi ya kuma ci gaba da karatunsa
na Islamiya a Makarantar Malam Muhammadu Babba. Haka kuma mai Martaba ya yi
Islamiya a Ɗan Musa ta Jahar Katsina da garin Isa ta Jahar Sakkwato, mai Martaba ya
fara karatun koyon yaƙi da Jahilci a garin samawa wato (Adult Education) a shekarar
(1941) Malaminsa a lokacin shi ne Malam Hassan ya yaba da ƙwazon mai Martaba wajen
fahimtar dukkan darussan daya yi masa.
A shekarar (1942) mai Martaba ya samu zama Malam Hakimi (Ɓillage Head) na sarkin yaƙin samawa. Ya riƙi wannan matsayi har na tsawon
shekaru (18) cikin natsuwa da nasara da kuma mutuntawa ga al’umma.
A shekarar (1954) mai Martaba ya zama sarkin yaƙin samawa inda ya gaji yayansa
kwatarkwashi na lokacin, mai Martaba ya riƙe wannan matsayin cikin nasara da girmama al’umma da
kuma mutuntawa ga talakawansa.
A ranar (17 ga watan Maris 1961) Allah ya yi baiwa ga mai Martaba ta
Sarautar Kwatarkwashi inda ya zama Sarkin Kwatarkwashi na (28), wannan rana
tayi dai-dai da 29 ga watan Azumin Ramadana na wannan shekarar, mai Martaba ya
ga ji Mahaifinsa Kwatarkwashi Ummaru III da kakansa Kwatarkwashi Dabo Kwatashi
Jigo kuma Kwatarkwashi na farko.
A shekarar (1996) bayan an ƙirƙiro Jahar Zamfara kuma an ɗaga darajar Masarautar Gusau, an naɗa mai Martaba a matsayin ɗan Majalisar Sarkin Gusau kuma ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki.
A shekarar (2000) kuwa Allah mai iko yasa gwamnatin wannan lokaci ta ɗaga darajar Masarautar Kwatarkwashi zuwa Emir na
farko a wannan masarautar.
A shekara ta (2002) kuma Ɗan Ummaru Jikan Dabo sadauki ya zama sarki mai daraja ta biyu wato (2nd
Class Emir).
Mai Martaba Ahmadu yana da Ɗiya (35) da Jikoki (137) daga cikin manyan
‘ya’yansa akwai mai girma sarkin yamman Kwatarkwashi Alh. Bello Ahmad Umar
(wanda shi ne ya cika shekaru “57” da Haihuwa a Duniya).
Akwai kuma Alh. Garba Ahmad Umar wanda jami’I ne a
hukumar fadama da dai sauransu.
Mai Martaba Alh. Ahmad Umar mai Kwatarkwashi yana daga
cikin ɗiyan sarautar
masu tsaga ko Bille wato Gidan ya kasu kashi biyu (2) kamar yadda muka ambata a
baya, akwai ɓangaren masu
tsaga akwai kuma ɓangaren
maras tsaga. Amma shi mai martaba yana cikin masu tsaga ne.
4.3 Tsarin Sunayen Sarakunan Ƙasar Kwatarkwashi
Tun Daga Sarki Na Farko Har Zuwa Yanzu
1. |
Kwatashi |
1400-1429 |
29 Years |
2.
|
Gazara (Gungama) |
1430-1469 |
37 Years |
3.
|
Mai Yaƙi (Gemen Dodo) |
1470-1500 |
30 Years |
4.
|
Bita Da Ƙasari |
1500-1549 |
49 Years |
5.
|
Ummaru I |
1549-1550 |
20 Years |
6.
|
Abu |
1570-1600 |
30 Years |
7.
|
Gumgama |
1600-1640 |
40 Years |
8.
|
Ɗan
Magaji |
1640-1679 |
39 Years |
9.
|
Mai Datsi |
1680-1689 |
9 Years |
10.
|
Ummaru II |
1689-1700 |
20 Years |
11.
|
Kure |
1700-1728 |
29 Years |
12.
|
Dange |
1729-1749 |
20 Years |
13.
|
Farin Wake |
1750-1769 |
19 Years |
14.
|
Alu Dan Mai Ɗaki |
1770-1800 |
10 Years |
15.
|
Dabo |
1800-1830 |
30 Years |
16.
|
Aliyu II |
1830-1860 |
30 Years |
17.
|
Idi |
1860-1873 |
13 Years |
18.
|
Tsaidau |
1873-1893 |
13 Years |
19.
|
Mai Rabo |
1893-1900 |
10 Years |
20.
|
Haruna |
1900-1907 |
7 Years |
21.
|
Babba |
1907-1910 |
7 Years |
22.
|
Badakari |
1911-1912 |
2 Years |
23.
|
Kada |
1912-1920 |
8 Years |
24.
|
Ummaru III |
1921-1954 |
33 Years |
25.
|
Abdullahi |
1954-1954 |
1 Year |
26.
|
Alu Labba |
1954-1959 |
5 Years |
27.
|
Ibrahim |
1959-1960 |
1 Year |
28.
|
Alh. Ahmad Umar |
1961-2018 |
57 Years |
4.4 Bukin Hawan Dutse Don Ɗauko Maiki
Maiki wani tsuntsu ne wanda ke zama a kan dutse, yana da
fika-fikai guda biyu, sannan tsuntsu ne mai ƙarfi ba kamar sauran tsuntsaye yake ba.
Shi dai Maiki yana zama ne a Dutse wanda a Kwatarkwashi
ana tsafa shi a wancan lokacin domin yin amfani dashi a wurin gudanar da
rayuwarsu ta yau da kullum.
Ana amfani da Maiki a lokacin aure domin nuna bajintar a
kan aure, ana taruwa ne a ƙofar mai gari a ranar da kasuwar garin ke ci bayan an
taru mazansu da matansu da yara da manya tare da tsofaffi masu sauran ƙarfi waɗanda suka san yadda ake gudanar da bukin da
aka gada tun kaka da kakanni, sai jarumawan magajin tsafin Magiro suna gaba ana
biye da su ana tafe ana kaɗe-kaɗe da raye-raye da ihu! Tare kuma da guɗa ga kirarin da ake yiwa amsu son nuna gwaninta
a kan ɗauko
tsuntsun nan Maiki daga saman Dutse zuwa ƙasa tare da ɗana gashin Maikin a kafaɗa tungida don nuna cewa sune jaruman bana.
Bayan jaruman sun haye sai a basu umurni da cewa duk su
haye kan tsuntsu daga nan sai a ɗauko masu Maiki a bayansu, sannan a ce su koma ƙasan dutse.
Duk wanda ya kai ƙasan shi to shi ya isa aure kenan, wanda kuwa bai kai ƙasan ba to
sai wata shekara kuma. A wurin hawan kuwa ana samun mutane masu mutuwa ko su
kaririye idan sun faɗo daga saman
dutsen a wurin hawa ko sauka. Kafin a fara ana yanka wa tsafin na Magiron
Magaji baƙaƙen bunsurai ko ‘yan kuikuyo don ya sha jini ya shaida sai
a je da naman gida a dafa a ci.
Kuma yadda ake yi wurin Bautar haka za’a koma gida da
raye-raye da kaɗe-kaɗe da sauransu, har a cikin garin ‘yan kallo
duk su shaida abunda aka yi wurin ɗauko Maiki tsafin ya yarda wasu suyi aure. Wasu kuma bai
yarda su yi ba sai shekara ta dawo.
Daga wannan sai a sanya ranar baiko za’a raba goro ‘yan
uwa da makwabta da abokan arziki na unguwanni da ƙauyukan da na garuruwa su zo dan baikon auren
wane da wance, za’a raba goro a ranar za’a zo da tabarma daga iyayen ango da
garin rogo da hure da nono da gishiri. Ana zuwa da ɗan Akuya daga iyayen Ango da sauran kayan
ciye-ciye da shaye-shaye da makamantansu.
4.5 Bukin Wasan Baura
Wasan Baura ana gudanar da shi sau ɗaya a shekara a lokacin kaka bayan an cire
kayan gona an kawo gida ranar kasuwar garin ake gudanar da ita. Tana daga cikin
bukin wasanni na shekara da ake aiwatarwa na al’adun gargajiya da suka gada tun
kaka da kakanni a maguzance. A ƙofar Gidan Magajin garin a nan ne ake gudanar da ita
kamar yadda aka sa ba a maguzance, ƙasar kwatarkwashi a fili don ana yinta kamar
wasan Dambe sai a ɗau tafi kama
da wasan kokuwa wadda muka sani. Don ita wannan wasan Baura ana gudanar da ita
a share fili tare da an yi masa zobe da ‘yan kallo na ko ina, sun zo. Su kuwa a
bisa al’ada sai kowannensu ya je wurin Bautar tsafin Magiro na Magaji Dutse
domin neman sa’a. Sannan a shigo da guda-guda ana yi masa kuwa da kirari da ɗai-ɗansu, sai su watsa zobba masu bala’in kaifin gaske kamar reza,
da su ake bugun mutum a duk inda wani ya samu ko a fuska ko a kunne ko a kunci
da dai sauran sassan jiki a nan ake bugawa har a kai wani ƙasa kwance
galala a cikin jini baje-baje. Amma akwai maganin da suke sawa idan an bugi
mutum har fata ta yanke. Suna haɗa kashin shanu a kwaɓa da wani magani sai a shafa wurin shi kenan zai tsaya ya
kuma shafe kamar ba’a yi yankan ba.
Masu wasan da ‘yan kallo duk suna gaf ne da duwatsun
tsafin ta ƙasanshi inda ake bi a hau saman a nan kusa da wurin akwai
kogunan duwatsu daban-daban da manya da ƙanana ana ce masu “Kwama” ana haɗa waɗanda basu taɓa sanin juna ba wanda yake kowannensu ana ji da shi a
garinsu a kan jaruntakarsu ta wannan wasan Baura kwarai.
Akwai mutumin da ya fi fice kwarai a wannan wasan ta Baura
ana ce masa “Kalago” don shi ne magajin tsafin Magiro ya bashi Shugaban wasan
Baura na ƙasar Kwatarkwashi, don ya riƙe gudanar da
ita yadda ya kamata, kuma ga garuwa da suka fi fice kamar su. Hurjin giya da saɓawa da sankalawa sune manyan garuruwa. Ana
samun wani ɗan wasa ya
zo da makaɗansa don ya
yi zafin nama da jaruntaka tare da nuna kwazonsa a fili.
A wurin haduwarsu makaɗa suna faɗin haka a cikin kiɗa da kirarin ‘yan wasa.
Gaka nan tafe!
Gaka nan tafe baƙo!
Gaka nan tafe baƙo ba’a san halinka ba!
Duk suna ciccika suna hurji har sai an girada tsakaninsu,
sannan a san na kwarai wanda shi ne jarumi.
4.6 Naɗewa
Kamar yadda aka gani a cikin wannan babi mai bincike ya
yi Magana ne a kan takaitccen tarihin ƙasar kwatarkwashi inda yake cewa ƙasar kwatarkwashi
gari ne mai daɗaɗɗen tarihi, asali da jaruntaka. An samu
kafuwar garin kwatarkwashi a cikin ƙarni na (14) kimanin shekaru (611) da suka
wuce wato (1400) zuwa yau.
Sunan kwatarkwashi dutse da ganuwa inda maiki ya shahara
saboda yawan duwatsun da Allah ya albarkaci wurin da su.
A gaba kuma, mai bincike ya yi bayanin ƙasar
kwatarkwashi gabanin Jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo, inda yake cewa ƙasar
kwatarkwashi wannan ba zama ne na farko ba, amma asalin waɗanda suka kafa garin ance sun taso ne daga Katsina
wato Katsinawa ne.
A gaba kuma, mai bincike ya yi bayani a kan tarihin mai
martaba sarkin Kwatarkwashi ne yanzu inda har karatunsa har ya zuwa ga samun
malantar da ya yi har kuma karshe ya
zama sarki, tare da nuna irin cigaban daya samu.
A gaba kuma, mai Bincike ya yi bayani a kan tsarin
sunayen sarakunan ƙasar kwatarkwashi tun daga sarki na farko har ya zuwa ga
sarki mai ci yanzu tare kuma da kawo shekarun da kowannen ya yi a kan gadon
sarauta.
A gaba kuma, mai bincike ya yi bayani a kan bukin hawan
dutse dan ɗauko maiki,
mai bincike ya yi bayanin yadda ake ɗauko maiki daga saman dutse wanda ake duk ya ɗauko shi to ya isa aure kenan idan kuma mutum
bai ɗauko ba to
shi ya nuna bai isa aure ba sai wata shekara.
A karshe mai bincike ya yi bayanin ne game da bukin wasan
Baura a ƙasar kwatarkwashi a in da ya yi bayanin yadda ake wasan
Baura a ƙasar kwatarkwashi da kuma irin maganin da ake sanyawa
mutum idan ya ji ciwo wurin wasan Baura da kuma nuna lokacin da ake yin
wasan.
1 Comments
Yusif jafar gulu
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.