Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (4)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (4)

Na

AMINU MURTALA

Kwatarkwashi

BABI NA UKU

1.0              Ma’anar Sarauta

Sarauta kalma ce babba mai ƙima da kwarjini da kuma mu’ujiza ga dukkan Jinsi na al’ummar duniya. Abin lura a nan shi ne, dama sarauta ce ake nema a zama sarki. Haka kuma it ace ake nema domin in ba sarauta ba za’a samu masarauta ba, balle Gidan sarauta, har a samu sarki da fadawa.

Jigon sarauta ya ƙunshi manya-manyan abubuwa da al’adun Bahaushe ke kallon sarauta das u. daga cikin abubuwan da ke shika-shikan ƙarƙashin sarauta akwai:-

i.                    Samuwar Sarauta

ii.                  Faɗuwar Sarauta

iii.                Yadda ake neman Sarauta

iv.                Waɗanda suka cancanci Sarauta

v.                  Waɗanda basu cancanci Sarauta ba

vi.                Yadda Sarauta take

vii.              Kokuwar neman Sarauta

viii.            Naɗin Sarauta

ix.                Daɗin Sarauta

x.                  Wuyar Sarauta

xi.                Shimfiɗar gadon Sarauta / Hawa gadon Sarauta

1.1              Su Wane ne Masarauta

Mutum ba zai yi sarauta ba sai ya gajeta, haka kuma ba zai gajeta ba inn ba Gidan sarauta ya fito ba ga asalinsa. Don haka ashe masarauta da Gidan sarauta sun fi sarki muhimmanci, domin da su sarki ke tinƙaho ba su ke tinƙaho da sarki ba. Kuma su suka yi sarki, ba sarki ya yi su ba, samun irin wannan tsari ya sa makaɗan fada kan keɓe jigo na musamman domin fito da wannan bayani ga sarakai da jama’arsu.

Ba dole don mawaƙi na yiwa fada waƙa ba, ace ba zai yiwa wata fada waƙar ba.

 

1.2              Tsarin Siyasar  Ƙasar Kwatarkwashi

Ga al’ada ba bu abin day a kai naɗin sarauta didima da annashuwa da farin ciki da buki da cashewa. Haka kuma nadin da za a yiwa sarki shi zai tabbatar da zaɓen da aka yimasa.

A ranar naɗin sarauta ne sarki zai yi bayani ga jama’a ya yi godiya gare su da neman goyon bayansu. A ranar ne wani babban sarki na ƙasar zai yiwa jama’a jawabi game da wanda aka zaɓa masu da kuma neman goyon bayansu ga sabon sarki. 

 

 

Narambaɗa Ya Fito da Wannan Jigo  Fili  a Waƙarsa Ta Fadar Mai mar taba Sarkin Kwatarkwashi Yana Cewa:- 

Yai halin mazan jiya ɗan sanda mai kwatarkwashi

                                                    Waɗan su sun sarauta sun sani ban tahoba

Da anka ce Alu assarkin gidanga gani na taho

                                      Waɗan su sun shekara goma sarki basui abinda kayiba

Sarki kamin kyautar Doki gami da kwakwata, in kai hakanga ka biya     

           


 

1.3              Tsarin Shugabancin Ƙasar Kwatarkwashi

Ga al’adun Maguzawa za muga cewa ana fara shugabanci tun cikin gidajensu za’a samu wanda shi ke faɗa aji a Gidan, don shi ne babba. Idan wani abu ya faru shi za a nufa don ya kashe wutar ko ya bada shawara akan a bun da ke faruwa ko ake so ayi. Haka kuma wadda ke uwargida ita ke gudanar da komi don itace yaya a Gidan kuma itace mai cewa ayi ko a bari, tana samun umurni da shawarwarin abun daya shafi Gidan ne daga kakansu uwayen Gidan mazansu da matansu idan yafi kowa shekaru a gidan.

Idan kuwa namiji shi ne yafi kowa shekaru a Gidan to shi ne zai riƙa ba da umurni gaba ɗaya. Ga al’adarsu suna ba da shugabanci tun daga gidajensu zuwa ga unguwanninsu da ƙauyukkansu zuwa garururwansu har ƙasar baki ɗayanta saboda nuna kwazonsu da jarumtarsu da juriya tareda kwarjininsu da kula da dangantakar zumuncin jama a. Ana bada shugabanci a sassan fannoni al’adun na sana’o’I da suka gada tun asali.

Ga tsarin shugabancin kamar haka:-

a.      Masarautar Kwatarkwashi na daTsarin Uwayen ƙasa Kamar Haka:-

1-      Sarkin Yamman Kwatarkwashi

2-      Uban Ƙasar Sankalawa

3-      Uban Ƙasar Samawa

4-      Uban Ƙasar Tofa

5-      Uban Ƙasar Gulubba

b.      Tsarin Muƙaman Sarautar Ƙasar Kwatarkwashi:-

1.      Wazirin Kwatarkwashi

2.      Magajin Kwatarkwashi

3.      Makaman Kwatarkwashi

4.      Garkuwan Kwatarkwashi

5.      Turakin Kwatarkwashi

6.      Wamban Kwatarkwashi

7.      Marafan Kwatarkwashi

8.      Ubandoman Kwatarkwashi

9.      Baraden Kwatarkwashi

10.     Tafidan Kwatarkwashi

11.     Walin Kwatarkwashi

12.     Yariman Kwatarkwashi

13.     Chiroman Kwatarkwashi

14.     Iyan Kwatarkwashi

15.     Ɗan Iyan Kwatarkwashi

16.     Talban Kwatarkwashi

17.     Sardaunan Kwatarkwashi

18.     Jarman Kwatarkwashi

19.     Tambarin Kwatarkwashi

20.     Katukan Kwatarkwashi

21.     Kogunan Kwatarkwashi

22.     Marafan Samawa

c.       Tsarin Shugabancin akan sana’o’i:-

Ƙasar Kwatarkwashi a matsayin ƙananan sarauta na al’ada ana bayar da su ne ga wanda ya nuna jaruntakarsu da kwarjininsa ga sana’arsa a fili ga inda yafi shahara kwarai a kan sana’arsa.

Ga kuma nasu tsarin kamar haka:-

1.      Sarkin Noma

2.      Sarkin Fada

3.      Sarkin Aski

4.      Sarkin Baushi

5.      Sarkin Ƙira  

 

1.4              Sauye-Sauyen Sarakunan Ƙasar Kwatarkwashi

Gabanin zuwan Shehu Usman Ɗanfodiyo Ƙasar Kwatarkwashi suna naɗa sarakunansu ne ta hanya kamar haka:-

Mutanen garin ko ƙasar Kwatarkwashi suna haɗuwa a wuri guda gaba ɗayansu su zauna su yi shawara a kan wanda ya kamatasu zaɓa a mastayin sarkinsu. Suna duba jaruntakar mutum mutuncinsa da irin yadda yake hulɗa da mutane wato suna zaɓen mutum mai nagarta mutumen kirki. Sai su zaɓe shi a matsayin sarki haka za’a naɗa shi a bashi sarauta.

Yanda kuma suke sauya shi, shi ne idan sarki ya yi masu wani laifi ko ya yi wani abu marar kyau ko abun kunya to sai mutanen gari su sake taruwa suje fada su fito da shi su fita ta ƙofar baya wadda a yau ake kira ƙofar bai zasu raka shi har ƙarshen gari wato gaba da Gulubba. A kan hanyarsu ta dawo wa duk wanda suka gamu da shi to shi ne Sarkin da zasu sake zaɓa a matsayin Sarkinsu.

Bayan zuwan Shehu Usman Ɗanfodiyo shi ne yanayin sarautar ya canza domin a wannan lokacin su na la’akari da wanda yak e Musulmi kuma mai riƙon Addini sannan kuma ana ba da sarauta ne idan mutum ya gaji sarautar wato idan mutum ɗan Gidan sarautar ne, ya gajeta ga mahaifinsa ko kakansa. Ba’a kuma ba wanda ya gaji sarauta ga mahaifiyarsu wato wanda yak e ɗan mace baya gadon sarautar wannan garin. Dole sai ɗan namiji wanda ya gajeta ga mahaifinsa ko kakansa. 


 

1.5              Naɗewa

Kamar yadda aka gani a cikin wannan babi an yi Magana a kan Ma’anar Sarauta in da mai bincike ya kawo ra’ayin wasu masan daban-daban dangane da ma’anar sarauta, wannan ya nuna mana cewa, a taƙaice sarauta kalma ce babba mai ƙima da kwarjini da kuma mu’ujiza ga dukkan jinsi na al’ummar duniya.

A gaba kuma, mai bincike ya fayyace ko su wane ne masarauta a cikin wannan babi wanda ya nuna mana cewa masarauta sune mutane da suka gaji sarauta ga iyayensu kuma wanda bai gajeta ba, ba zai zama cikin masarauta ba.

A gaba kuma, mai bincike ya yi bayani a kan Tsarin siyasar sarautar Ƙasar Kwatarkwashi. A in da mai bincike ya nuna yadda tsarin sarautar Ƙasar Kwatarkwashi ya ke, da kuma kawo yadda tsarin uwayen ƙasar kwatarkwashi yak e daga ƙarshe kuma a ka kawo yadda tsarin shugabanci a kan sana’o’in ƙasar kwatarkwashi ya ke.

A ƙarshe, mai bincike ya tattauna a kan sauye-sauyen sarakunan ƙasar kwatarkwashi tun gabanin zuwan Shehu Usman Ɗanfodiyo har zuwansa.

Wato mai bincike ya yi bayani a cikin wannan babi na yadda ake naɗa sarki da kuma yadda ake sauya shi.    

Post a Comment

0 Comments