Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (2)

Na

AMINU MURTALA

Kwatarkwashi 

BABI NA BIYU

1.0              Bitar Ayyukkan Da Suka Gabata

A cikin wannan babi wato bitare ayyukkan da suka gabata hakika mai bincike ya ci karo da ra ayoyi daban-daban na masana da kuma manazarta, har ma da malamai da kuma dalibbai ba a barsu a baya ba domin sunyi ayyukka masu dangantaka da irin wannan aiki.

 Bunza (2009) a cikin littafinsa mai suna Narambaɗa ya yi bayani a kan sarauta da masarauta da yadda ake nadin sarauta da kuma yadda sarauta take. A wannan bincike kuma ana Magana ne a kan tarihin masarauta kwatar-kwashi.

Sadi (1700-1995) a cikin littafinsa ya yi bayanin wasan Baura da yadda ake ɗaukar maiki a kan dutse. Wannan aiki yana da alaƙa da binciken da za’a gudanar ta fuskar shi ya yi Magana a kan wasan Baura da yadda ake ɗauko maiki a kan dutse shi kuma wannan bincike ana Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwatashi.

Abdullahi da Muh’d (2011) a cikin littafinsu sun yi bayani a kan ƙasar Kwatarkwashi dangantakar aikinsu da wannan bincike shi ne wannan bincike anyi shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Al-Hassan da Musa da Zaruk (1982) a cikin littafinsu sun yi bayanin ne a kan duniyar Hausawa da bayani a kan sarauta da kuma bayani a kan muƙamai waɗanda ke zagaye da masarauta. Dangantar wannan littafin da wannan aikin shi ne wannan bincike ana yinsa ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Dashi (2009) a kundinsa na Digirin Farko ya yi bayani a kan “Kan gida da ire-irensa a ƙasar Kwatarkwashi dangantakar aikinsa da wannan bincike shi ne wannan bincike ana yinsa ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi, shi a nashi yana Magana ne a kan Kan gida da ire-irensa a ƙasar Kwatarkwashi.

Bala (2012) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan tasirin zamani a auren maguzawan Kwatarkwashi. Dangantakar aikinsa da wannan aikin binciken shi ne a wannan ana bayani ne a kan tarihin Masarautar Kwatarkwashi a na shi kuwa ya yi bayani ne akan tasirin zamani a auren maguzawan Kwatarkwashi.

Sani Umar (2012) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan Gwagwarmayar Musulunci da gudumuwarsa a ƙasar Kwatarkwashi Bungudu Local Goɓernment a wannan bincike kuma ana Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Abdullahi (2008) a kudin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan Tsafe-tsafe a Bukukuwan maguzawan Kwatarkwashi. A wannan bincike kuma ana Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Mainasara (2001) a kudin Digirin Farko ya yi bayani ne a kan Bautar Magiro a ƙasar Zamfara. Dangantarkar aikinsa da wannan aiki na bincike shi ne ya yi bayani a kan ƙasar Kwatarkwashi da Magana a kan Masarautar Kwatarkwashi, wannan bincikr kuwa ya na bayani ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Mashi (2001) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani ne a kan Maguzanci. A wannan aiki kuwa a na Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Na’inna (2011) a wata muƙala ya yi bayani a kan taƙaitaccen tarihin ƙasar Kwatarkwashi, wannan bincike kuwa an gudanar da shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Turaki (2011) a wata muƙala ya yi bayani a kan tarihin mai Martaba Sarkin Kwatarkwashi, wannan binciken kuwa yana Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Birnin Magaji (2015) a wata muƙala ya yi bayanin taƙaitaccen Tarihin Kwatarkwashi. Dangantakar aikin sa da wannan bincike shi ne an gudanar da wannan binciken a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Joɗi (2011) a wata muƙala ya yi bayani a kan bukin mai Martaba Sarkin Kwatarkwashi ya kawo tarihin mai Martaba, wannan bincike kuwa anyi shi ne a kan Tarihin Masauratar Kwatarkwashi.

Musa (2016) a kundin Digirinsa na Biyu ya yi bayani a kan gudummar Musulunci ga korar al’adu da Tsafe-tsafe a ƙasar Kwatarkwashi, wannan bincike an gudanar da shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Millennium Target (2016) a littafinsu sun yi bayani a kan Kwatarkwashi a yau”, wannan bincike an gudanar da shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Hashimu (2015) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan Tarihin Liman Musa Kura, dangantarkar aikinsa da wannan bincike ya yi bayanin takaitaccen Tarihin Ƙasar Kwatarkwashi, wannan binciken kuwa yana bayani ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Rikiji (2014) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan ƙungiyar Izalah a ƙasar Kwatarkwashi, wannan binciken yana Magana a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Safana (2001) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan “Maguzawa Lezumawa”. Dangantakar aikinsa da wannan bincike ya yi bayanin wuraren Bautar Maguzawa a Kotorkoshi a wannan binciken kuwa yana bayani ne game da Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Maikano (2002) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayanin a kan Maguzawan Yari-bori dangatakar aikinsa da wannan binciken ya yi Magana a kan ƙasar Kwatarkwashi wannan binciken kuwa yana magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Abdullmumini (2014) a kudin Digirinsa na Farko ya yi bayanin  a kan Canje-canjen da Musulunci ya kawo a bangaren Bukukuwa a ƙasar Kwatarkwashi. Dangantakar aikin sa da wannan binciken shi ne ya yi tsokaci a kan ƙasar Kwatarkwashi, wannan binciken kuwa an yi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Basarakiya (2011) ta yi bayani ne a kan taƙaitaccen tarihin Masarautar Kwatarkwashi. Wannan binciken kuwa ya ta’allaƙa ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Basarakiya (2012) ta yi bayani ne a kan taƙaitaccen tarihin Masarautar Kwatarkwashi. Wannan binciken kuwa ya na magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

Basarakiya (2013) ta yi bayani ne a kan taƙaitaccen tarihin Masarautar Kwatarkwashi. Dangantakar ta da wannan binciken kuwa an gudanar da shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

 

1.1              NAƊEWA

Kamar yadda aka gani a cikin wannan babi mai bincike ya yi Magana ne a kan bitar ayyukkan da suka gabata in da mai bincike ya kawo ra’ayoyin Malamai da Ɗalibban daban-daban dangane da irin gudummuwar da suka bayar game da wannan bincike na Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

A farko mai bincike ya yi amfani da littafai daban-daban da kundaye na wasu Ɗalibbai da kuma Muƙalu da Jaridu da aka gabatar a wurare daban-daban.

A babi na gaba mai bincike zai yi Magana ko bayani ne a kan ma’anar sarauta da su waye masarauta da kuma tsarin siyasar sarautar ƙasar Kwatarkwashi da kuma abun da ke sa a sauya sarki.

A karshe sai mai bincike ya rufe babin da bayanin nadewa.

Post a Comment

0 Comments