Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (2)

Na

AMINU MURTALA

 

Kwatarkwashi

BABI NA ƊAYA

1.0              Gabatarwa

Tarihi abu ne mai Muhimmanci da ke kawo abubuwan da suka gabata kuma ya fito da halin da ake ciki a yanzu da hasashen gaba. Tarihin masarautar kwatarkwashi mai bincike zai yi bayani ne kacukan a kan wannan masarautar tun daga yanayin ƙasar da yadda suke gudanar da harkokin sarautar su da abin daya shafi harkokin rayuwarsu na yau da kullun.

Binciken zai yi bayanin yadda ƙasar kwatarkwashi take tun gabanin jihadin Shehu Usman Danfodiyo da kawo tarihin mai martaba sarkin kwatarkwashi na yanzu, da kuma kawo sunayen sarakunan da suka riƙi ƙasar kwatarkwashi tun daga sarki na farko har zuwa sarki na yanzu wanda yake akan mulki. Haka nan kuma mai bincike zai yi bayanin yadda ake ɗauko maiki a kan dutse da wasar Baura da kuma yadda ake sauya sarakuna a ƙasar kwatarkwashi.   

 

1.1              Manufar Bincike

Manufar bincike shi ne a fito da abubuwan da yasa mai bincike ke so ya nuna wa mutane wanda ba’a sani ba musamman tarihin masarautar kwatarkwashi, duk da za’a samu kundayen da suka yi tsokaci a kan ƙasar kwatarkwashi ko wani abu daya shafi ƙasar kwatarkwashi, sai dai za’a samu cikakken bayani ba kamar yadda mai wannan bincike ya gudanar da wannan aiki, saboda shi ɓangare ne da yake Magana akan tarihin masarautar kwatarkwashi.

 

1.2              Dabarun Bincike

A wannan bincike, mai bincike ya bi hanyoyi da dama ta hanyar sa hikima da yin hira da mutane da ke da wani abin cewa game da wannan aiki na bincike.

Ya kuma samu ƙarin bayani daga fadar ƙasar ko garin a tsakanin Wazirin kwatarkwashi da Magatakarda da Turakin kwatarkwashi da kuma Fadawan sarkin kwatarkwashi.

Mai bincike ya bi Malamai don neman shawarwari a garesu da kuma samun ƙarin bayani a kan yadda mai bincike zai bi aikin tiryan-tiryan wato daki-daki a cikin tsari.

Haka kuma anyi amfani da kundaye waɗanda suka yi kama ko suke da alaƙa da irin aikin don zaƙalo muhimman abubuwan da suka dace da waɗanda masarauta ke da shi.  

 

1.3              Muhimmancin Bincike

A duk inda ka ga Ɗan Adam a doron ƙasa yana yin wani abu to Gaskiya zaka tarar cewa abin yana da matukar amfani da muhimmancin ƙwarai. Haka kuma wannan bincike da aka gudanar yana da amfani ga jama’a musamman ma masu nazarin harshen Nijeriya da al’adu.

A kan haka ne mai bincike ya zaɓi aiki a ɓangaren Tarihin Masarautar kwatarkwashi, don sanin yadda masarautar take tun gabanin Jihadin Shehu Usman Danfodiyo kamar yanayin zamantakewarsu da  sha’anin rayuwarsu da kuma abin da ya shafi aurensu, da yadda suke gudanar da bukukuwansu irin na ɗauko Maiki ko hawan Dutse don ɗauko Maiki da wasan Baura da yadda tsarin shugabancinsu yake da kuma sauye-sauyen da suke samu ga sarakunansu.

 

1.4              Farfajiyar Bincike

A wannan aiki na farfajiyar Bincike mai Bincike ya maida hankalinsa ne kacokan a kan tarihin masarautar kwatarkwashi, wato tun daga kafuwar ƙasar ko masarautar har zuwa yanzu.

Mai Bincike zai yi tsokaci a kan yadda masarautar kwatarkwashi take da yadda ta samu tun kamin Jihadin Shehu Usman Danfodiyo da kawo yadda ake ɗaukar Maiki akan dutse da yadda ake wasan Baura tare kuma da kawo sunayen sarakunan ƙasar kwatarkwashi tun daga sarki na farko har zuwa ga sarki na yanzu wato wanda ke kan karagar mulki kuma tarihi ya nuna mana cewa su Ashirin da ta Kwas ne (28). 

Ina fatar wannan aiki zai yi amfani ga manazarta a sashen harsunan Nijeriya, musamman masu karatun (B.A Hausa) a sashen harsunan da al’adu ga nazarin da suke yi mai kama da wannan na tarihin masarautar ko adabi ya ƙarfafa ga idon duniya sosai. Allah ya sa ya kasance mai amfani ga na bayanmu a tsakanin Ƙannenmu da Ɗiyanmu da ma Jikokinmu da su amfana da shi, amin.

Post a Comment

0 Comments