Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (1)
Na
AMINU MURTALA
SADAUKARWA
Ni Aminu Murtala, na Sadaukar da wannan
littafin kundin digirin farko da na yi a sashen Harsunan Nigeriya a jami’ar
Tarayya Gusau.
Na sadaukar da shi ga Ɗa na shi ne
Al-Ameen Aminu Murtala da Babata da Mahaifina su ne Hajiya Habiba Muhammad
Kwatarkwasi da Alhaji Murtala Salisu Kurah, Kwatarkwasi wanda shi ne ya ɗauki nauyin karatuna tun daga furamari zuwa
sakandare har in da Allah ya kai ni a yanzu. Don haka ina mai roƙon Allah
dare da rana da cewa Allah ya saka masu da mafificin Alkhairi ya kuma sa su
gama lafiya da duniya ya sa su Aljannar Firdausi ce makomarsu, Amin.
A kan haka ne na sadaukar da shi zuwa ga
matata da yannena da ƙanne na tare da ‘yan uwa da abokan arziki da na nesa da
na kusa, da ma dattijai da samari da ɗiyan yanne na da na ƙanne na da waɗanda suka taimaka mani wurin nazarin da binciken a kan
hirar da nayi da su daban-daban da wanda shi ne magatakardan masarautar
kwatarkwashi ya taimaka mani wurin haɗa mani wasu kayan da suka taimaka mani don rubutu wannan
kundin digirin farko a sashen Nazarin Harsunan Nijeriya (B.A Hausa) Jami’ar
Tarayya Gusau.
GODIYA
Ina mai godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki Mai kowa mai komi mai Rahama mai jinƙai zuwa ga
bayinsa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu (S.A.W) da
sahabbansa da zuriyarsa da dukkan wanda ya bishi zuwa ranar sakamako, Amin.
Bayan haka, ina mai nuna farin cikin godiya ta ga malamai
na na sashen nazarin harsunan Nijeriya tare da irin gudummuwar da suka bani
taimakawarsu har Allah ya kawoni wannan lokacin da nike haɗa kundin digirin farko a bisa ga haka ne nake
ƙara yiwa
Allah Maɗaukakin
Sarki godiya a kan wannan baiwar da ya bani ALHAMDULILLAH godiya ta tabbata ga
Allah.
Ina mai nuna godiya ta musamman ga Shugaban sashen
nazarin harsunan Najeriya wanda ya bani shawarwari a kan yadda za a wannan
binciken cikin tsanaki tare da ban sha’awa ƙwarai shi ne Prof. Aliyu Muhammad Bunza, da
sauran Malaman sashen nazarin da suka taimaka wurin aikin littafin ya gudana
kamar su Malam Rabi’u Ɗan gulbi da Malan Musa Fadama da Malan Isah S. Fada da Malan S. Gulbi da Mallan
Yakawada da Malan S. Gubir da Malan Balarabe da Mallan Imrana da dai sauran
Malaman da ke sashen nazarin harsunan Nijeriya ina mai godiya a garesu bisa ga
gaggarumin gudummawar sa suka bani Allah Maɗaukakin Sarki ya saka masu da alkhairinsa ya kaisu
makomar Aljannar Firdausi.
Godiya ta musamman ga Malamina wato Malan Musa Abdullahi
wanda shi ne ya yi ta ɗawainiyar
duba wannan aiki tare da ba ni shawara ba bu gazawa dare da rana, kuma babu
fushi ko nuna gajiya a duk lokacin da na sameshi, Allah Maɗaukakin Sarki ya saka masa da mafificin
alkhairinsa ya kuma saka masa da Gidan Aljannar Firdausi, amin.
Daga ƙarshe, ina miƙa godiya ta ga abokaina waɗanda muke karatu tare kamar Jafar Usman da
Mukhtar Abbakar da Sama’ila Aliyu da Bashar Haruna da Bilya Umar da Umar Yahaya
Dogara da Abdulrahman Lawal da Sadiya Kabiru da kuma Shafa’atu Salihu Labbo da
ma waɗanda suke
abokai ne na gida, musamman Abubakar Muhammad da Nafi’u Ibrahim da Yusha’u
Ibrahim da Murtala Lawal da Nafi’u Bello da Shafi’u Sulaiman da Aminu Totti da
dai sauransu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.