Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Amsa-Kama A Waƙoƙin Bakan
(5)
NA
SAMAILA ALIYU
BABI NA HUƊU
NAZARIN AMSA-KAMA A WAƘAR BAKA
4.0 Gabatarwa
Wannan babin zai
kalli amsa-kama a cikin waƙoƙin Alhaji Gambo da
Narambaɗa, da Salihu Jankiɗi, da sauran wasu
mawaƙan baka. Har wayau kuma zai kalli amsa-kama a cikin wasu
mawaƙan zamani irin su Adamu Kahuta Rarara da Ado Gwanja da
Kabiru Yahaya Kilasik. Da kuma amsa-kama cikin Jimlolin Hausa.
4.1 Amsa-Kama a Cikin
Waƙoƙin Alhaji Muhammadu Gambo
Kalmomin amsa-kama da
za a yi nazari a cikin waƙoƙin Muhammadu Gambo su
ne kamar haka;
a) Sharkat
b) Birdit
c) Kangai-rangai
d) Ar’!
e) Sakwankwan
f) Jangwam
g) Birjik
h) Kyar! Kyar!! Kyar!!!
Amsa-kama
a cikin waƙar Gambo inda yake cewa! “cikin” waƙar masu amfani da wuƙa:
Jagora:
Ko da yac ciri yuƙa yak kafa mat,
Taf fasa kuwwa tay yi jicce,
Yab bar su da gawa kwance sharkat!
A wata waƙa cikin tsakuren
Nassi ya ce:
Jagora: Sai da nay yi hawan manyan
hadissai
Nag ga wurin duk ba ɓarayi.
Kur’ani da nad daga haka,
Bakin amma zuwa sabbi,
Nag ga Jama’a ga su birdit
A cikin waƙar Tsoho Tudu cewa ya
yi:
Jagora: Rangai-rangai ni da
baba
Ana labari lahiya lau
Nic ce! “wallahi kana gane kurenka”
Sarrafa kalmomin sata
a waƙoƙin sata in da ya ke cewa:
Jagora: In ji maƙwabta na hwadin ar!
In ishe mata sun yi yakkwat
In ishe tsohi na hawaye
A waƙar Inuwa cewa ya yi:
Jagora: Ya yi shiru
Ya sad da kai ƙasa
Yay yi sakwankwan
Yay yi jangwan
Sannan Inuwa yay yi zonai
Yai babba sheda mijin nau,
A cikin waƙar layya in da ya ke
cewa:
Jagora: Don maganal layyata ta bara,
Ga salla na gurgusowa,
Amma bane juyi zan ragewa,
Don bana ba ni da kudɗi ban da rago,
Ba ni da hwashi layya Gambo,
Sai ran na san Jajibir muke,
Nay yi subahi nay yi yamma,
Bakin garka ko da ni ishe Dikko
_________________________
: Nar riƙe ɗan icce na darni
: Kamar wani tsoho yam mace min,
: Yac ce mis samu Gambo
: Mis sa kab ɓata ranka,
: Mataw wani kat taɓa
: Ko ɗiyaw wani?
: Nac ce ni kowa ban taɓa ba,
: Amma fa ina kunya karon ga
Nic ce don ka san yau jajibir muke,
Dikko ba ni da hwashi layya baba
Ga ni da mata yara-yara
Ga ni da barwa masu wasa
Ga ni da cikin manyan makwaɓta,
Ga ni da ‘ya ‘ya ga su birjik
A waƙar ‘yan boko cewa ya
yi:
Jagora: Satan biliyan ɗaya wa ka yin ta?
Mai rika raza ba shi yin ta
Mai tare hanya ba shi yin ta
Ko mai fasa banki ba shi yin ta
Don ko ya zo bai ishe su.
Satan biliyan ɗaya wa ko yin ta?
Mai rike biro ɗai ka yin ta
Ƙyar! ƙyar!! ƙyar!!! Ya rubuta
Ya sa hannu ya kashe su.
Waɗannan su ne wasu daga
cikin misalan amsa-kama da su ka fito cikin baitocin waƙoƙin Mahammadu Gambo.
4.2 Amsa-Kama Cikin Waƙoƙin
Ibrahim Narambaɗa
-
Tsombul
-
Fari
fes!
-
Kus!
Kus!! Kus!!!
-
Tinjim
-
Dukui-dukui
Misalan
su cikin baitocin waƙoƙin.
Gidan wakai: Danmalam ci kwallo Sarkin
Gudu
Na yarda da Danhilinge
Jagora:
Kai ko Alsan bai kai kamataiba,
Don ya samu jiki fari fes!
GINDIN Waƙa: Madogara na Malam
Iro Uban Bawa mai Gida Shinkafi
Jagora:
Mai kamakka Ibrahim,
Ka ga ya sha hura da nono tsumbul!
Ya ci tuwo da nama
Ga sutura, gas hi had da Doki ɗamre
Yab biye mutanen zamani
Sun ka kai shi ga hanyab banza,
Yara: Ga igiyara ruwa
sauka bas shi,
Yau ga ya nan da ragga tinjim!
Dole sai shi sha rummace.
Jagora: Dan sarkin da
yay yi doro,
Hay yay yi ɗan ƙusumbi abu dai duƙui-ɗukui
Yara: Fau-fau
Ba ka jin an na dai sarki
4.3 Amsa-Kama Cikin Wakar Sarkin Kotson Gusau Husaini, Ta
Sarkin Katsinan Gusau Kabir Dan Baba
Gindi Mamman jikan
sambo, sarkin Gusau Kabir Danbaba.
JAGORA: Dan
gahiyar ga mai bakar sata
Ya koma gida tas
Kayan ka, dai na laihi ne,
Ballai kayi man ras
4.4 Amsa-Kama Cikin Waƙar Ɗan
Gunduwa Kagara Morai Ta Sarkin Anka Attahiru Amadu.
JAGORA: Ɗan sarkin ga mai
kwadai,
Ba a gayyata tai liyafa
ba,
Amma naga ne shi can
yai,
Rashe-Rashe baki
nai natse-natse
4.5 Amsa-Kama Cikin Waƙoƙin
Zamani
Amsa-kama cikin waƙar Adamu Kahutu
Rarara
Gindi: masu gudu su gudu.
Inda yake cewa:
Jami’a gonar waƙa, in ka muna adalci
mu maka,
In ana maganar canji
APC sai ta karɓi duka
Mi ya kawo maganar
canji APC sai ta karɓi duka,
Mi ya kawo maganar
turmi, kowa yasan aikin shi daka,
Shi injin cakula, an
fi mashi lissafi da niƙa
Ita PDP tumbur
mu ka ce za’ayi kuma an yi haka
Mun hallaka PDP a
saman da ƙasa
Mu ne da duka
A wata rerawa cewa ya
yi:
Saura kuma zaɓen gwamnoni
Sai mun yiwa PDP Zigidir
4.6 Amsa- Kama Cikin Waƙar Ado Gwanja
Gindi Waƙa: Ɗakin bakuwa wa zai
leka Allah raba mu da halinki baƙar ashana
Jagora: Ɗakin bakuwa wa zai
leka?
Allah rabamu da halinki
bakar-ashana
Ɗakin bakuwa wa zai leƙa?
Allah rabamu da halinki
anti kunama
Yad da zaren yaz zo haka
kalar yadin,
Mai
neman sani jeka ga kundi,
Zo
da buƙur-bƙkur mugun siddi
Ra’ayin
rayuwa ba a yi da ni ba.
4.7 Amsa-Kama Cikin Waƙoƙin
Kabiru Yahaya Kilasik
Gindi Waƙa: Assalamu alaikum
Tambihi ne yaz zo na Gaskiya Allah ya ga ni P.D.P ciyaman sai Nasiru Ibrahim
Ammani
Jagora: Kuma ba shi da kilasimet
Ko dai don shi ba book
yay yi ba.
Amma kullum kai nai Sal-sal
Wai dakta ba a farga ba.
Kumatu yai wani tuli-tuli
Amma sauna bai farga ba.
Mai hannu baka hannu
akushi
Lalatacce baka tsira ba.
A wata rerawa cewa ya
yi:
Jagora: Nasiru yad dace Gusau fadamarmu ya
ɗauka ban ruwa.
Da wane ya
zan ciyaman Gusau, ai gara a yo
bannar ruwa.
Ɗandaudo kana da halin
mata wani mai
bakin shan
romuwa.
Gun faska yai wani gadan-gadan
Ya a za ban
ganik ke shi ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.