Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Amsa-Kama A Waƙoƙin Bakan
(4)
NA
SAMAILA ALIYU
BABI NA UKU
AMSA-KAMA A WAƘAR BAKA
1.0
Gabatarwa
Wannan babi ya kalli
ma’anar amsa-kama da rabe-rabe amsa-kama da mahimmancinta. Sannan kuma ya kalli
ma’anar waƙar baka, da tasirin waƙar baka, sai muka
nade babin da takaita zancen da babin ya kunsa.
(Amfani 1996), akwai
miskila a Hausa dangane da cewa shin ajin kalmomi na amsa-kama ake da shi ko
kuwa ajin bayanau? Idan muka duba.
Ƙamusan Bargery
(1934), za mu ga sam babu wani ajin kalmomi na amsa-kama duk kalmomi da yau ake
kira amsa-kama a waɗannan ƙamus guda
biyu,bayanau (Adɓerb) ne. To amma
Galadanci (1976), da Newman (1977), da sauran ayyuka na yau, duk sun bambanta
tsakanin amsa-kama da bayanau. Dalilin wannana miskila bai rasa alaƙa da cewa a ilimin
kimiyar harshe, Kalmar amsa-kama (idiophone) sabuwar kalma ce da aka ƙirƙiro a tsakiyar ƙarni na ashirin. Don
haka, sa’ad da aka rubuta ƙamus Bargery da na Abraham, babu
wannan kalma ta ‘amsa-kama’ wannan shi ya sa ba su yi amfani da ita ba. Yanzu
abin da ya rage shi ne a tabbata akwai ƙwararan hujjoji da
za’a yi amfani da su wajen tantancewa tsakanin amsa-kama da bayanau saboda haka
bari muji abun da masana ke cewa game da
ma’anar, bayanau da amsa-kama, wanda wannan ne zai tabbata mana da cewa waɗannan azuzuwan
kalmomi ne mabambanta, kuma masu cin gashin kansu. Abin lura a nan shi ne, ajin
bayanau ƙarin bayani yake yi game da aiki. Ya yin da amsa-kama ke
nuna yadda ake yin wani aiki.
3.1 Ma’anar Amsa-Kama
(Cole, 1955),
Amsa-kama kamancen sautuka ne, ko launi ko ƙamshi, ko na yanayi
abu, ko abin da ake iya aikatawa, ko nuna tsananin kyawon wani abu. Misali zane
ko hotuna ko kuma abubuwa masu wakiltar ido wajen kallo, ko saurare da wasu
fannoni masu ba mutum damar fahimta ko lura da abu, ko kuma kalmomi masu nuna
gogewa da yadda ake aiki da hankali.
Paul da Roɗana Newman (2002), Su
ma a ganinsu amsa-kama kalmomi ne da ke fayyace yanayin sauti, da launi, da
bayanin sigar sura da kuma yanayi ko halin da abu yake ciki (aikatau).
(Sa’id, 2006), ya
bayyana amsa-kama a matsayin kalma mai siffanata abin da ake magana a kai. Abin
nufi a nan shi ne amsa-kama na aikin fayyace yadda aiki ke aukuwa a cikin
Magana.
Misali Audu ya tsaya
cik. A nan kalmar cik ita ce amsa-kama domin tana nuna yadda aka tsayau ko
yadda tsayuwa ta kasance. (Wikipedia, the free encyclopedia)
Amsa-kama kalmomi ne
waɗanda mai magana ke
amfani da su domin bayyana abubuwa da ake iya ji ko tantancewa ta hanyar taɓawa, ko waɗanda ake iya gani a
kuma fahimta. Misali kamshi da launi da girman abu. Da sauti, da abin da
motsuwa. Misali daga nan zuwa can.
Amsa-kama dai,
kalmomi ne waɗanda ke ƙarin bayani a kan
aikatau, ko siffanta yadda aikin aikatau yake gudana a cikin jimla. Sai dai
kalmomin amsa-kama suna da ɓirɓishin jawo hankali da
haifar da motsawar rai.
3.2
Rabe-Raben Amsa-Kama
Wannan
suna dai an samo shi ne daga yadda kalmomi ke amfani ta hanyoyi iri-iri don ƙarfafa ma’anonin wasu
kalmomi. A taikace dai kowace kalma daga cikin waɗannan aka yi wa laƙabi da amsa-kama tana
daɗa nuna tsananin
ma’anar kalmar da ake so a ɗaukaka. Yawancin kalmomin da suke zuwa da amsa-kama duk
sunaye ne kuma su amsa-kama ɗin suna iya zuwa bayan sunayen kalmar yadda za mu gani
idan mun zo wurin ba da misalai nan gaba.
Kuma dangane da irin ma’anonin da
amsa-kama kan ƙara ƙarfafawa sun ƙunshi fannoni irin na
abubuwa da suka shafi launi, ko sifa ko ƙirar jiki, ko wani
irin hali da mutum ko wani abu ke ciki da dai sauran irin waɗannan fannoni. Alal
misali kamar in an zo maganar ƙirar jiki sai ka ga an yi amfani da
wata kalma wadda take amsa irin kalmar da ake son jaddadawa muna iya duba
wannan jimlar:
“ Na ga wata mace ɗibgegiya na nemanka”
To da jin wannan
jimlar nan da nan wanda kake gaya ma (da
ma wasu masu saurare ne kawai) zai fahimci irin matar da kake nufi dangane da ƙirarta ko sifarta
saboda amfani da amsa-kama da kayi watau “ɗibgegiya”.
Kuma ko ba a faɗa ba kai ka san
wannan matar tana da tsananin girma wanda ya haɗa da kauri da ma tsawo. Akwai mu da
amsa-kama fal a Hausa, amma yanzu mu yi magana kan wasu daga ciki musamman ma
dangane da yadda muke sarafa su a jimloli daban-daban don ma’anoni iri-iri.
3.3
Amsa-kama masu nuna
tsananin girman jiki ko abu.
a) Ɓulɓu; An kawo wa Baba
wata saniya ɓulɓul da ita
b) ruƙuu-ruƙuu; Ya sami goro ruƙuu-ruƙuu zai kai wa
bazawararsa.
c) Gungurun; Ta samo
wani rake gungurun da shi.
3.4
Amsa-kama masu nuna wani irin halin da
mutum ko wani abu ke ciki
a) laƙaƙai-laƙaƙai; Haba ai Abdu yana
tafiya laƙaƙai-laƙaƙai shi ya sa ba ya
dawowa.
b) saɗa-saɗaf; Binta ta tafiya
saɗaf-saɗaf don kar Baba ya ji
c) buguzun-buguzun; Dubi
yadda take kaiwa da kawowa buguzun-buguzun kamar ta sha ƙwaya.
d) tukuf; Abdu ya tsufa
tukuf
e) tuburan; Okonko
mahaukaci ne tuburan
f) sanƙanƙan; Karime na tafiya
sanƙanƙan kamar ta haɗiyi taɓarya
g) birjik; Kai yau na ga
mutane birjik a filin sukuwa
h) ma’aƙil; Ai yau kasuwa ta
cika maƙil har ba masaka tsinke
3.5
Amsa-kama masu nuna ga jiya ko wata irin
kama
a) tiɓis; Sa’adatu ta gaji
tiɓis don tsananin aikin
niƙa.
b) zugun; Shehu ya yi
zugum yana tunanin duniya.
c) gaalaalaa; Dubi yadda
juma ta yi wani galala da baki don sakarci.
3.6
Amsa-kama masu nuna
tsananin launi
a) sol; Na ga mai kudi
ya sa wata riga fara sol ya nufi makaranta.
b) ƙirin; Don Allah dubi
yadda ta daura wani zane baƙi ƙirin da shi!
c) wuluk; Fuskar ishaku
baka ce wuluk har tna shaƙi.
d) jawur: mis. Idanun
Aminu sun yi ja-jawur don tsananin shangiya.
e) shar; Ganyayen
bishiyoyi sukan yi kore shar da damina.
3.7
Amsa-kama masu nuna
tsananin tsafta
a) tas; Sai da ta wanke
fuskarta tas sannan ta fara kwalliya
b) fes; Yan makaranta
sukan fito fes duk ranar litanin.
c) garau; Don Allah
rowan nan garau da shi!
Wadanan
su ne wasu daga rabe-rabe da mu yin a amsa-kama dangane da irin ma’anonin da
suka bayarwa idan sun zo a jimloli iri-iri kasan cewarsu a jimloli watau
ka’idar aukuwarsu za mu ga cewa duk cikinsu suna kama da siffofin ne kamar
yadda muka tattauna a baya tuni.
Suna kama da sifofi
ta hanyoyi biyu. Na farko ta hanyar kara bayyana sunaye, sai dai su amsa-kama
suna kara karfafa ma’anonin sunaye ne. Na biyu kuma su ma amsa-kama sukan zo ne
da sunaye wani lokaci kafin sunayen su zo.
Harila yau muna da
nau’o’in daban-daban na waɗannan amsa-kama watau wasu ana sarrafa su dangane da
yadda abin da ake son karfafawa yake ko “namiji” ne ko “mace” ce sai a yi
amfani da amsa-kama yadda zai dace. Idan kuma jam’ i ne ma haka.
Bugu da kari kuma
wasu daga cikin amsa-kama din kamar fes, sadaf,-sadaf da sauransu ba sa taran
nau’in abin da ake Magana kai watau ko “namiji” ne ko “mace” ce ko kuma
“jam’i” ne duk za a iya amfani da su.
3.8
Ma’anar Waƙar Baka
Waƙar baka dadaddiya ce
wadda aka fara ta tun lokaci daɗaɗɗe mai nisan gaske.
Akwai wasu matakai, wato kalmomi muhimmai da za a iya amfani da su wajen fito
da ma’anar waƙar baka, su ne kuwa
ü Rerawa
ü Hawa da saukar murya
ü Azanci
ü Naƙaltar harshe
ü Hikima da fasaha
ü Kida
ü Karɓi ko amshi
ü Gaɗa da tafi
ü Saƙo
Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya bayyana wasu
hanyoyi da ake bi ta kansu a shirya waƙar baka. A takaice
kalmomi da ake haɗa su, suzama zance
ciki yanayin waɗa. Ga abin da ya
cewa.
Duk makaɗan da at tsahe na
shahe,
Hab baƙi har yan gidan su
duka,
Babu mai shirya waka kamar tawa,
Duk makaɗan da at tsahe nai
jam’i,
Hab baƙi har yan gidan su
duka,
Babu mai ƙulla waƙa kamar tawa,
Ga makiɗi ya ƙulla waƙa tai
Sai a amsa mashi ba a
ƙara
mai,
In na ƙulla waƙa a ƙara man,
Mu haɗu duk azanci gare mu,
Shin a’a mutun guda
za ya yarde mu,
Gindi: shirya kayan
faɗa mai gida tsahe
Ali ɗaniro baka dauki raini
ba.
Kalmomi ‘shirya’ da ƙulla da ‘amsa’ da ‘ƙara’ da ‘azanci’ su
ne suke bayyana yadda Ɗankwairo yake kallon waƙar baka da cewa zance
ne shiryayye mai hikima da ake ƙullawa cikin azanci tare da yi masa
kari da karɓi. A she kenan
tsararriyar waƙa baka gamsasshiya da za a iya ƙara waƙa ita ce wadda ta ƙunshi waɗannan abubuwa
Ø Saƙo
Ø Fasaha/azanci/hikima
Ø Tsari/shiri
Ø Saƙa/ƙulla
Ø Zaɓi
Ø Sautin murya/rauji
Ø Raurawa
Duk waɗannan tubalai ne na
gina waƙa waɗanda idan aka rasa su, to sai dai wani abu, amma ba waƙa ba. Rashin
wasu daga cikinsu kuma kan raunana waƙa ta zama lami tamkar
miya ba gishiri.
Yanzu
kuma za mu duba mu ga yadda masana adabin Hausa suke kallon ma’anar waƙa daɗa ta baka ce ko
rubutacciya.
Yahaya (1976:1), a gabatarwa da ya
yi wa littafin waƙar haɗa kan Afirika cewa ya yi:
“waƙa magana ce ta fasaha
a cure wuri ɗaya a cikin tsari na
musamman”
Yahaya (1984:2-3), ma
ga yadda ya kalli waƙa:
“waƙa maganar hikima ce
da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke
da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma
zaunannu.”
Ɗangambo (Laccar Aji:
16/11/1982) ya bayana waƙa kamar haka:
waƙa wani furuci ne wato
lafazi ko saƙo
cikin azanci da ake
aiwatarwa ta hanyar
rerawa da daidaita
kalmomi cikin tsari
ko ƙa’ida da kuma yin
amfani da dabaru kan salon amshi!
Amma ma’anar da za a
iya ba waƙar baka ta kai tsaye ba tare da gwamata da waƙar rubutacciya ba,
ita ce? Dangambo 1982
Waƙar baka, wani zance
ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaba-gaba bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa
a rere cikin sautin murya da amsa-amo
kari da kida da amshi. Daidaitawar da ake yi wa layukan waƙa, ya sa ba ta zuwa a
shimfiɗe ko kuma ta zo gaba ɗaya a’a tana zuwa ne
gutsure-gutsure tare da maimaita gindinta a tsakaninsu. Kusan kowace gutsure
kammalalle ne ga kansa, sai dai wani lokaci ma’anar takan cika ta tumbatsa ta
tsallaka zuwa ga gutsure da ke biye. Gutsuren nan da ake magana shi ne jagoran
waƙa
ya kan fara furtawa kafin yan amshinsu su karɓa, yakan rere layi ko wasu layuka daga
cikinsa, daga nan ‘yan amshinsa su isar da sauran layukan. Amma a waƙoƙin da suke da kadaita
kawai, kadaitan ne shi kaɗai yake furta layuka
a ɗiyan waƙarsa.
A nan ya kamata mu tuna cewa, akwai
waƙoƙi iri biyu
rubutacciyna waƙa da waƙar baka wato waƙar makaɗa. Shin me ce ce waƙa? Sau da yawa mutane
sukan yi wannan Tambaya, mahawara ta harƙe. Ko da yake ba nufi
na ba ne in kawo wannan mahawara a nan, to amma ina ganin ya wajaba. Domin kuwa
fahimtar abin da ake nufi da “waƙa” ita ce ginshiƙin fahimtar nazarin
waƙa.
Domin kuwa sai an fahimci abin da ake nufi da waƙa ne za a iya gane
abin da waƙa ta ƙunsa, da inda ta nufa da kuma yadda za
a iya yanke hukunci a kan kyaunta ko
rashin kyaunta.
Muna iya cewa waƙa wani saƙo ne da ake gina shi
kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, dango, rerawa kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙa’idoji da suka shafi
daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su
cikin sigogin da ba lalle ne haka suke maganar baka. Dangambo 1982
3.9 Nadewa
Babbban sakamakon da
aka samu game da ma’anar amsa-kama da rabe-raben sa da mahimmancinsa. da kuma
ma’anar waƙar baka da tasirin ta ga Hausawa. Duk wannan sakamakon ya
sa mu ne daga masana daban-daban, kumar su Bunza (2006), da Galadanci (1976), da Newman (1977), da Ƙamus Bargery (1934),
da Cole (1955) da Paul da Roɗana Newman (2002), da
Sa’id (2006), da Wikipedia the free encyclopedia.
Zari’a (1978) Gusau
(2003) Yahaya (1984) Ɗangambo (1982) Aminu (1978). Har wa yau masana irin su
Murphy (1980) da Depereze (1991) Stephen (2012) sun yarda cewa amsa-kama na
amfani da Kalmar da amonta ke bayyana
ma’anar watau Kalmar ta kwaikwayon amo ne.
0 Comments
Post your comment or ask a question.