Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Amsa-Kama A Waƙoƙin Bakan
(6)
NA
SAMAILA ALIYU
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 Kammalawa
A babi na ɗaya an nuna yadda
tsarin binciken ya gudana. Babin ya fara ne da gabatarwa sannan aka kawo
manufar bincike. An bayyana cewa a lokacin da ake ƙoƙarin karance-karancen
don samar wa binciken gindin zama, ba’a ci karo da wani bincike da aka yi irin
wannan binciken ba. An ambaci cewa farfajiyar binciken ta tsaya ne kan ayyukan
da aka gudanar waɗanda suka shafi
amsa-kama a waƙoƙin baka. An bayyana muhimmancin wannan bincike da cewa an
aiwatar da shi ne domin a magance ire-iren matsalolin da ake cin karo da su
wajen fahimtar amsa-kama cikin waƙoƙin baka. Aikin ya
gudana ne ta hanyoyin tattaro bayanai daga littafai da aka wallafa da kundayen
da bitar ayyukkan da suka gabaci wannan aiki waɗanda suke da nasaba da shi. An gudanar
da aikin bitar ayyukan ne kan muhimman ayukka daban-daban da aka gudanar kan
amsa-kama; ayyukan su ne Murphy (1980), da depereze (1991), da Stephen (2012),
da Amfani (1996), da cole (1995), da Galadanci (1976), da Newman (1977).
Babi na hudu bayan gabatarwa, aikin
ya tattaro amsa-kama daga mawaka daban-daban na Hausa. Aikin ya kawo ire-iren
amsa-kama cikin waƙoƙin baka.
5.1 Shawarwari
Dangane da bincike da
aka gudanar, a lokacin da ake ƙoƙarin kammala wannan
aikin, an fahimci cewa akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata masana su maida
hankalinsu game da su. Abubuwan sune:
(a)
Ya
kamata masana nahawun harshen hausa, su ƙara ƙoƙari, don a samar da ƙarin ƙamusun Ingilish zuwa
Hausa.
Saboda ba wani ƙamus mai irin wannan
tsari baya gana Rozna ma Newman, wanda ta wallafa a shekarar 1997.
samar da kamusu irin wannan zai taimaka wa
masu nazari don samun sauƙin fassara wasu kalmomi na ilimin kimiyar harshe a
lokacin da suke gudanar da nazarin wani fannin nahawu daga littafan Ingilishi.
(b)
Masana
ilimin kimiyar harshe da suke gudanar da ayukkansu a kan harshen Hausa ya
kamata su lura da ire-iren sababbin kalmomi da suke shigowa na zamani zuwa
cikin harshen Hausa. Rashin lura da ire-iren wadannan kalmomi na iya haifar da
matsala na samun ɓacewar kalmomi na asali.
(c)
Gudanar
da nazarin waɗannan kalmomi zai
taimaka wajen adana kalmomin Hausa na asali ba tare da sun ɓacce ba.
Sannan kuma za’a sami ƙarin wasu kalmomi da
za su dace da zamanin da ake ciki.
5.2 Manazarta
Tuntuɓi masu gudanarwa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.