Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Amsa-Kama A Wakokin Bakan (3)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Nazarin Amsa-Kama A Waƙoƙin Bakan (3)

NA

SAMAILA ALIYU

Gurmi 

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

1.0              Gabatarwa

A wannan babin an yi bita ne a kan ayyukan masana magabata da marubuta da dama, sun yi bincike da nazarce-nazarce daban-daban a kan amsa-kama da kuma waƙoƙin baka, da suka gabaci wannan aikin. Wato masu nasaba ta kai tsaye ko kuma kai kai ce. Musamman waɗanda a ka buga su, suka zama littafai ko kuma kundayen digiri a matakai daban-daban da muƙalu da dai sauransu. Ga su kamar haka:

2.1       Galadanci

            Galadanci (1976:28), a cikin littafinsa main suna “ AN INTRODUCTION TO HAUSA GRAMMER” inda ya kawo kashe-kashen amsa-kama kamar haka

(A)

kasaƙe

zaƙo-zaƙo

firgigit

wuf

tuburan

kwaram

buguzun-buguzun

(B)

ƙaciɓis

fat

rak

sukutum

fil

tak

garandan

kwal

zir.

2.2       Bagari

            Bagari (1986), a cikin littafinsa “Bayanin Hausa Jagora ga Mai Koyon Ilimin Bayanin Harshe”. Ya kwatanta kalmomi ƙirgau amsa-kama da ajin sifa ta fuskar aiki. Don haka ya kira kalmomi da sifofi adadin masana irin su Bagari (1986), sun yarda da cewa kalmomi ƙirgau amsa-kama na iya zuwa kafin suna misali.

 tsibin kaya   biyar  

   

Ƙgak      Sn                 Ƙg kadina

A wannan misalin Kalmar ƙirgau amsa-kama ita ce “tsib:” ta suna kuma ‘kaya’ kuma Kalmar ƙirgau kadina ‘biyar’.

2.3       Amfani

Amfani (2010) a maƙalarsa mai take “Reɓisiting of the Categorization of Element in Hausa”. Ya bayyana cewa: “kalmomin ‘tak’ da ‘rak’ da ‘cur’ da ‘tal’ da ‘kadai’ kalmomin ƙirgau ne masu cin gashin kansu. A lura da kyau, kalmomin wannan nau’in na ƙirgau amsa-kama, suna da bukatar sake dubawa.

2.4       Umar Sa’idu

            Umar Sa’idu (1985), a kundin digirin sa a farko mai taken “Bishiyar Li’irabi A Cikin Nahawun Hausa.” Sashen Harsunan Nijeriya na Jami’ar Sakkwato. Inda ya yi bayanin amsa-kama a shafi na sha-tara (19) inda ya ce: “kalmomin da za a iya ɗaukarsu a matsayin amsa-kama” su ne kamar haka:

tsundun

fit

shar

wuf

makil

fil

tas da dai sauran su.

2.5       Inuwa Salisu Kankia da Umar Suleman Bello

            Inuwa Salisu Kankia da Umar Sulemam Bello (1987), a kundin digirin su na farko mai taken “Tubalan Ginin Kalma da Matsalolin su  a Cikin Nahawun Hausa.” A shafi na sha-biyar (15) ya kawo misalan amsa-kama kamar haka:

tiɓis

funjum

liɓis

tukuf

haiƙan

ainun

sosai

kwaram

2.6       Sama’ila Umar

            Sama’ila Umar (2012) a cikin kundin digirin sa na biyu, mai take “Matsayin ‘Yar Rakiya a Yankin Sun: a Tsokaci A Kan Ƙirgau.” A shafi na (117) ya kawo misalan ƙirgau kamar haka,

diris

firit

jingim

tsibi

sharkaf

kacal

rak

tal

kwai

birjik

galibi

tari

ɗinbi

tuli

daɓaɓa

kwatsatsa

kadai

Duk wadannan kalmomin masana sun bayyana su da cewa kalmomin ƙirgau amsa-kama ne.

Kasan cewar wannan aiki yana da alaƙa da waƙar baka, saboda haka an yi bitar wasu ayyukan da masana suka yi a kan waƙoƙin baka kamar haka.

2.7       Yahaya A.B

            Yahaya A.B (2001), a cikin muƙalarsa mai suna “Salo Asirin Waƙe,” wani ɓangare ne ko kuma sauyin salo a cikin rubutattun waƙoƙin Hausa na wa’azi a cikin wannan maƙalar marubucin ya yi ƙoƙarin tabbatar da cewa da suka keɓanta da shi.

2.8       Yahaya A.B

            Yahaya A.B (1997), a cikin littafinsa mai suna “Jigon Nazarin Waƙe” mawallafin ya kawo ma’anar waƙe daga masana da waɗanda ba masana ba, har ma da yadda su mawaƙan suka ɗauki waƙar.

2.9       Gusau

            Gusau (2003), a littafinsa mai suna “Jagoran Nazarin Waƙar Baka,” ya kawo bayanin waƙar baka da bunƙasar waƙar baka a ƙasar Hausa.

Waɗannan su ne wasu daga cikin ayyukan masana da magabata da aka yi bita dangane da amsa-kama da kuma waƙoƙin baka.

2.10     Nadewa

A binciken wannan aiki ba a ci karo da  wani aiki na kundin aikin N.C.E ko Difloma ko BA ko MA ko Phd da ya kebanta ga amsa-kama kawai. Don haka na ga babu wata tazara ta doguwar bita face in ambato fitattun ayyukan magabata na harshe da suka yi bayanin amsa-kama.

Post a Comment

0 Comments