Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Amsa-Kama A Waƙoƙin Baka (1)
NA
SAMAILA ALIYU
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan aiki nawa ga iyayena,
da iyalaina. Da fatar Allah ya ƙara masu lafiya amin.
GODIYA
Yabo da godiya, sun
tabbata ga Allah mai kowa mai komi. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga
fiyayyen halitta cikamakin Annabawa, Annabi Muhammada Ɗan Abdullahi (S.A.W)
da iyalansa da sahabbansa. Har ya zuwa ranar sakamako.
Ina mika godiyata
zuwa ga babban malamina wanda ya jure da yanayin rayuwata, ya bani shawarwari,
kuma ya ɗauki nauyin dubawa da
gyara wannan aiki. Wannan malami shi ne farfesa Aliyu Muhammad Bunza. Allah ya
saka masa da alheri ya gafatarwa mahaifansa yasa aljanna ta zama makomarsu, shi
da zuri’arsa.
Haka kuma ina mika
godiyata ga malamaina da suka taimaka mani wajen ganin wannan aiki ya samu
nasarar kammalawa.
Gasu kamar haka:
Farfesa Halliru
Amfani, Farfesa Atiku Ahmad Dumfawa, Farfesa Abdulhamid Ɗantumbishi, Mal. Musa
Abdullahi, Mal. Adamu Ibrahim Malumfashi, Mal. Isah S. Fada, Mal. Aliyu
Dangulbi, Farfesa Magaji Tsoho Yakawada, Farfesa Balarabe Abdullahi, Dr. Yakubu
Gobir.
Ganin wannan shafi taƙaitacce, naga ya
kamata in miƙa godiya ga dukkan malamaina na sashen Harsuna da Al’adu
da sauran malaman tsangaya gaba ɗaya Allah ya saka wa kowa da alherinsa.
Ina miƙa godiya ga Mariya
Lawal bisa ga shawarwari na gode. Godiya ga yaya na Kabiru Garba (Unity) da
Isah Aliyu, da Haruna Abdullahi, da
Mustapha Lawali Jega, da Yusufa Kafu, da Sanusi Garba Yandi Ɗanfodiyo (Islamic
Health Center), bisa taimakona da suka yi na gode. Allah ya saka ma kowa da
alheri.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.