Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Amsa-Kama A Waƙoƙin Bakan
(2)
NA
SAMAILA ALIYU
BABI NA ƊAYA
1.0
Gabatarwa
Harshen Hausa, harshe
ne rayayye wanda a kullum sababbin abubuwa suna shigarsa, don haka yake samun
sauyawa da lokaci.
Masu nazarin nahawun
Hausa, sun yi ayyuka masu ɗimbin yawa game da al’amura daban-daban na nahawu. Waɗannan ayyuka a kullum
a na sake ziyartarsu da nufin kyautata su, saboda da wata sabuwar fahimta da ta
zo, wadda kuma ake ganin lalle ya kamata a yi nazarin nahawun Hausa bisa turbar
wannan fahimta. Galadanci (1976) aiki ne muhimmi a kan amsa-kama a jumlar
Hausa.
Wannan aiki ya yi niyyar gudanar da
nazari a kan amsa-kama a waƙoƙin baka na Hausa, da
nufin fito ko kuma zaƙulo abubuwan da suke boye na game da amsa-kama, a cikin
waƙoƙin baka, don ƙara bunƙasa harshen Hausa.
Don samun nasara wannan aikin, an kar kasa aikin zuwa babuka biyar (5).
1.1 Manufar
Bincike
Manufar wannan
bincike shi ne, sake duba aikin da aka gudanar a kan amsa-kama da nufin warware
matsalar da a ke cin karo da ita, ta fahimta a lokacin nazarinsa. Musamman a
muhallin da masana suka bar wasu gurabe a cinkushe ba tare da yin bayanin su
filla-filla ta yadda mai nazari zai iya fahimtarsa. Gudanar da aikin zai fito
da sabon cigaba da aka samu ta fuskar nazarin nahawun harshe.
1.2
Dalilin Bincike
Dalilin gudanar da
wannan bincike shi ne, don a yi ƙarin haske kan wasu
gurabe da aka bar su a cinkushe cikin ayyukan da Amfani (1996) da Bagari
(1986)da Charles H Kraft (1973) da Galadanci (1976) da N.Skinner (1977) suka
gudanar kan amsa-kama da nufin gano hanyoyin da za a warware su a cikin wannan
bincike.
Gudanar da bincike
makamancin wannan, ba sabon abu ba ne a ɓangaren nahawu da harshen Hausa. Amsa-kama
bisa ga karance-karancen da a ke yi, Allah bai sa an ci karo da wani aiki mai
take ɗaya da kuma manufa ɗaya da wannan bincike
ba.
Wannan ne ya sa aka
ga lallai ya da ce a gudanar da irin wannan bincike a dai-dai wannan lokaci.
Haka kuma ana sa ran cewa wannan bincike zai kasance a matsayin wata gudunmuwa
da aka bayar wurin ƙara ci gaban harshen Hausa. Har-ila yau kuma, wannan aiki
zai zama wani harsashi na kafa wani sabon bincike musamman a wannnan fanni na
nahawu da adabin Hausa.
1.3 Muhimmancin
Bincike
Babban muhimmancin wannan bincike shi ne,
don a magance ire-iren matsalolin da ake cin karo da su wajen fahimtar
amsa-kama a cikin waƙoƙin baka. Haka kuma, aikin zai kasance ƙarin abin dubawa ga
manazarta da ke makarantu daban-daban, ya kuma ba da damar kafa wani sabon
bincike a wannan fanni. Har ila yau kuma, idan har akwai wasu ayyuka makamantan
wannan da aka fara amma saboda waɗansu dalilai, ba a sami sukunin gamawa ba,
akwai yiyuwar wannan aiki ya ba da damar kammala su.
1.4 Farfajiyar
Bincike
Farfajiyar da aka keɓance wa wannan
bincike ita ce, amsa-kama a waƙoƙin baka. Inda aka
sake nazarin wasu muhimman waƙoƙin baka na makaɗa da su ka gudanar.
An takaita wannan bincike ne kan amsa-kama a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Da
nufin baje wasu waƙoƙi makaɗa da suka bar su a dunkule,ba tare da an fito da
bayaninsu filla-filla ba. Aikin ya samo tarsashin sa ne daga ayyukan da aka
gudanar kan amsa-kama da kuma waƙoƙin baka na Hausa.
Kamar irin ayyukan Yahaya (1992), da
Amfani (1996), da Bunza (2009),
da Bunza (2014), da Cole (1955), da Depereze (1991), da Galadanci (1976), da Murphy (1980), da Newman (1977), da Paul da Newman (2002), da
Stephen (2012), da Zair’a (1981), da suka gudanar.
1.5 Hanyyoyin
Gudanar da Bincike
Hanyoyin da aka bi
warin gudanar da wannan bincike su ne ta hanyar karanta, tare kuma da bin
diddigin ayyukan masana. Sannan kuma a wannan aikin, an yi amfani da yanar gizo
don binciko ayyukan masana da su ka saka a yanar, saboda samar da sabuwar
hanyar nazari ta zamani. Daga nan kuma aiki ya dubi kundayen digiri da aka
gudanar a jami’oi musamman waɗanda su ka shafi ginin jimlar Hausa inda aka karkata
akalar binciken akan ‘Amsa-Kama a Waƙoƙin Baka.’
1.6 Naɗewa
A cikin wannan babin
da ya gabata, an tattauna al’amuran da suka shafi wannan bincike tun daga
manufar bincike da kuma dalilin bincike, da muhimmancin bincike da kuma
farfajiyar bincike, da hanyoyin gudanar da bincike.
0 Comments
Post your comment or ask a question.