VISION FM
92.5 MHZ SOKOTO
TASKAR VISION RADIO SRIPTS
PRODUCER: ZUBAIRU AHMAD BASHIR (KASARAWA)
17/11/2020 VFMNEWS TASKA
CUE IN SIGNATURE TUNE
Taskar Vision kuke
saurare daga nan Gidajen Rediyon Vision FM Najeriya, dake yada shirye shiryensu
akan mita 92.1 a Abuja Babban Birnin tarayya da Katsina birnin Dikko, mita 92.5
a Jihohin Sokoto, Kano da Kaduna, a Birnin Kebbi kuwa a na sauraren Vision FM,
akan mita 92.9, sai kuma mita 92.7 a jihar Gombe.
Zaku iya sauraren Vision
FM kaitsaye a koda yaushe daga ko ina a fadin duniya, ta adireshin mu na
internet wato Visionfm.ng
Hakama zaku iya bibiyarmu
ta shafukanmu na Facebook, Twitter, da Instagram domin tafka muhawara akan
labaran da muke wallafawa, duka a Vision FM Nigeria.
CUE IN
TUNE………………………………..
Masu sauraro assalamu
alaikum, barkammu da warhaka Zayyanu Ibrahim Maradun ne ke farin cikin
kasancewa daku a Taskar ta yau, shirin da ke kawo muku labaran duniya har ma da
rahotannin abubuwan da ke faruwa a nan Najeriya da makwabciya Jamhuriya Nijar
har ma da sauran kasashen duniya.
A cikin rahotannin mu na yau zaku ji cewa:
1.
Rahotanni daga jahar Sakkwato na bayyana yau
Assabar din nan ne wata mata ‘yar asalin Jamhuriya Nijar ta tsallake rijiya da
baya, biyon bayan zargin wani jami’in hukumar shige da ficen Najeriya da
harbinta, a birnin Sokoto.
Cue………………………………..in
Wata Mata.
2.
Rashin samun tallafi daga gwamnati ya tilastawa
Manoman rani a jahar Kebbi yin Kaurar-dole zuwa Makwabtan jihohi domin neman Mafita. To ko me yayi zafi haka?
Cue in………………………………….Manomi
3.
Muna kuma tafe da shirin yan siyasa na iya
ruwa fidda kai a cikin taskar ta yau.
Cue in……………………………. Iya Ruwa
Zaku ji cikon wannan dama
shirin Najeriya a Makon Jiya tare da Nura Muhammad Ringim, to
amma bari mu fara da jin halin da duniya ke ciki tukunna.
TASKA
TUNE………………………………………….
LABARAN DUNIYA
AFGHANISTAN
Akalla mutum
takwas ne suka mutu yayin da fiye da 30 suka jikkata sakamakon harin rokoki da
aka kai rukunin gidaje a birnin Kabul na Afghanistan.
Roka fiye da 12
aka harba daga wata mota zuwa cikin birnin, a cewar ma'aikatar harkokin cikin
gida.
Ƙungiyar IS ta
yankin ta ɗauki alhakin kai harin, wanda aka kai a wanni kadan kafin tattaunawa
tsakanin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da wakilan ƙungiyar
Taliban.
A farkon makon nan ne gwamnatin Donald Trump ta sanar da
cewa za ta janye dakaru 2,000 daga Afghanistan nan zuwa watan Janairu.
Masu sharhi da dama na ganin sojojin Afghanistan ba su da
ƙarfin yin yaƙin da kansu idan sojojin ƙasashen waje suka fice.
VISION NEWS HAU
BRAZIL
Masu fafutikar adawa da wariyar launin fata a kasar
Brazil na zanga-zanga a gaban babban kantin Carrefour bayan ƴan sanda sun
aikata ƙazamin kisa kan wani mutum baƙar-fata da ke aiki a kantin.
Lamarin dai ya faru ne a kudancin birnin Porto Alegre a
daren Alhamis din data gabata, 'yan sanda sun yi amfani da ƙarfi wajen tarwatsa
dubban masu zanga-zangar.
Mutumin da jami'an tsaron suka kashe ɗan shekara 40 ne
mai suna Joao Alberto Silveira Freitas. Sai dai Mataimakin Shugaban Brazil,
Hamilton Mourao ya alakanta kisan da rashin ƙwarewa irinta jami'an tsaro sannan
ya dage kan cewa ba a nuna wariyar launin fata a kasar ta Barzil.
VISION NEWS HAU.
LABARUN
DUNIYA KUKE SAURARO DAGA NAN VISION FM NIJERIYA.
AMURKA
Zaɓaɓɓen
Shugaban kasar Amurka Joe Biden na neman kuɗin gudanar da shirye-shirye na karɓar
gwamnatin ƙasar saboda shugaba Trump ya ki bayar da haɗin kai domin miƙa mulki
ga tawagarsa.
Cikin
wata yekuwar neman tallafi da Biden ya wallafa a shafinsa na Twitter, ana neman
magoya bayansa da su tara kuɗin saboda Donald Trump ya ƙi aminta da shan kaye.
Sakon
na Joe Baden ya nuna buƙatar taimako daga magoya bayansa domin iya gudanar da
tsare-tsaren karbar gwamnati daga hannun shugaba Trump.
To sai dai a gefe guda kuma,
Donald Trump ya sake fuskantar gagarumin koma-baya a ƙalubalantar sahihancin
sakamakon zaɓen da yake yi.
'Yan majalisar Jihar Michigan
na jam'iyyar Republican ta Trump sun faɗa masa cewa ba su samu wasu gamsassun
bayanai da za su iya yin watsi da nasarar da Joe Biden ya samu ba a Jihar, don
haka dole a jingine duk wata matsala da za ta haifar da barazana ga kasar.
VISION NEWS HAU.
Labarun
duniyar kenan, yanzu kuma sai rahotanni shirye shiryen da Taskar take dauke
dasu.
TASKA
TUNE…………………………………………
21-11-2020 TASKA SOKOTO
Da sanyin safiyar Assabar din
nan ne wata mata ‘yar asalin Jamhuriya Nijar ta tsallake rijiya da baya, biyon
bayan wani harbin bindiga da ake zargin wani jami’in hukumar kula da shige da
fice ta Najeriya ya yi mata, lamarin da ya auku a tsakiyar birnin Sokoto.
Kamar yadda zaku ji a cikin
wannan rahoton da Abubakar Tauba ya aiko mana daga Sokoto, an garzaya da matar a
asibitin kwararru dake Sokoto, sai dai jami’in da yayi harbin ya sha da kyar a
hannun wasu fusatattun yan Najeriya da suka shedi yadda lamarin ya auku.
Ga dai rahoton da Tauban ya
aiko mana daga Sokoton.
Cue
in Sokoto: Start with voice of demonstrators
A gaida Tauba, sai ka dakace
mu domin zaka sake dawowa cikin taskar nan gaba kadan.
Cue
in Amadu Ajilo’s song…. ”Allah Wahidun Ka
taimaki ‘yan Najeriya, kasarmu ta zauna lafiya baki dai”
21-11-2020 TASKA KEBBI
Idan muka leka a jihar Kebbi
dake makwabtaka da sokoton kuwa, Manoman ranin jihar ne ke yin Kaurar-dole ta
hanyar barin jihar zuwa Makwabtan jihohi domin neman Mafita ko mafaka.
Manoman sun ce sun dauki
matakin ne saboda kasawar da suke zargin Gwamnatin jihar Kebbi ta yi wajen
taimaka musu da tallafin da zai basu kwarin quiwar tsayawa a fadammunsu na
gadin-gadin.
Bari mu ji halin da suke ciki
a cikin wannan rahoton da Muhammad Yazeed Umar ya aiko mana daga jihar ta
Kebbi.
Cue
in kebbi: The farmar’s voice………………….
Muhammad yazzed Umar kenan, yanzu
kuma sai shirin siyasa na wannan
makon wato Iya ruwa fidda kai tare da
Kabir Hassan Iyatawa.
Gareka Iyatawa.
Cue
in Iya Ruwa tune……………………………..
Shirin siyasa na Iya ruwa fidda kai kenan kuka saurara tare da Kabir Hassan Iyatawa, da fatar
yan siyasa da masu ra’ayin tofa albarkacin akan lamuran siyasa zasu tuntubi
wakilanamu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Cue
in tune.
BREAK
To
wadannan rahotanni na zuwa muku ne daga nan gidan rediyon Vision FM Najeriya dake
Birnin tarayya Abuja sai jihohin Katsina,
Kano da Kaduna, hakama ana sauraren shirin a jihohin Sokoto, Kebbi da kuma Gombe.
Za
ku iya saurarenmu kai tsaye ko karanta labaran da muke wallafawa a shafinmu na
Intanet wato, visionfm.ng ko tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta a
Vsion Fm Najeriya.
Taska
Tune…………….…………………………..
21-11-2020 TASKA SOKOTO
Madalla!
Rahotanni daga Jihar Sokoto
daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar ‘yan bindiga masu garkuwa da
mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya na cewa, a tsakiyar makon nan ne
masu garkuwa da mutane suka sako Hon. Sa’idu Gumburawa mai baiwa Gwamna Tambuwal
shawara akan ayukka na musaman bayan yin garkuwa da shi na tsawon kwanaki.
Ko ya aka yi har Gumburawan
ya kubuta?
Daga Sakkwato Abbakar Abbakar
Taubah na da cikon rahoton.
Cue
in…………………………… Tauba
Yanzu
kuma sai ku gyara zama domin kasancewa da shirin Najeriya a makon jiya tare da
Nura Muhammad Ringim!
Cue
in……….. Najeria a Makon Jiya
Nura
Muhammad Ringim kenan da shirinsa na Najeriya a makon jiya!
Cue
in…………………………… tune
To
ga baki daya da haka ne, Taskar ta yau ta kammala, a madadin Zubairu Ahmad
Bashir, wanda shine ya hada muna wannan taska ta yau, sai kuma Ukashatu
Bello Sakkwato, da ya kula muna da sauti ni Zayyanu Ibrahim Maradun da na
gabatar, ke cewa mu kasance cikin koshin lafiya. Sai dai kada ku manta a koda
yaushe kuna iya saurarenmu akan yanar gizo wato visionfmrdio.ng
Cue
in…………………………….Taska tune.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.