Ticker

6/recent/ticker-posts

Ingausar Yarbawa Da Hausawa A Garin Gusau, Jihar Zamfara (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Ingausar Yarbawa Da Hausawa A Garin Gusau, Jihar Zamfara (6)

NA

ADAMU SANI

Zamfara State

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 SHIMFIƊA

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, wanda ya baiwa ɗan-Adam fasahar karatu da rubutu, tare da bayar da dammar yin wannan aikin. Allah mun gode ma, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonmu Annabi Muhammad (S.A.W) tare da iyalansa da sahabbansa har zuwa ranar ƙarshe.

 

Wannan babin shi ne babi na ƙarshe a wannan aiki, yana ɗauke da abubuwa kamar haka; Taƙaitawa, da hasashen bincike, haka kuma akwai ta’arifin wasu kalmomi. Bugu da ƙari daga ƙarshe akwai naɗewa.

 

5.1 TAƘAITAWA

A wannan bagire za a taƙaita aikin ne gaba ɗaya ta hanyar haskaka ababen da aka binciko da kuma sakamakon binciken, da kuma kammalawar aikin. Wannan bicike ya ƙunshi babi biyar, za mu bayyana abin da kowane babi ya tattauna a taƙice kamar haka:

 

Babi na ɗaya an tattauna abubuwa kamar; dalilin gudanar da bincike, da muhallin bincike. Haka kuma an bayyana hanyoyin gudanar da bincike. Bugu da ƙari, an bayyana muhimmancin bincike kamar samar da abubuwan karatu, bayan waɗannan an bayyana matsalolin da aka fuskanta lokacin gudanar da binciken kamar ƙin bada haɗin kai daga wasu Yarbawa da sauransu.

 

A babi na biyu an waiwayi wasu ayuka na magabata da aka gabatar a kan ingausa da kuma wasu masu alaƙa da ita. Daga bugaggun littattafai, da muƙalu, da kuma kundin bincike.

 

Babi na  uku kuwa mai taken “Gusau ta Sambo”, an tattauna abubuwa da dama daga ciki akwai; Taƙaitaccen tarihin Gusau, an waiwayi kafuwar garin Gusau a shekarar (1806) da kuma zaman sa babban birnin jihar Zamfara a shekarar (1996). Haka kuma an bayyana yanayin garin, da kuma waɗanda suka fara zama a garin, bugu da ƙari an bayyana tattalin arzikin mutanen garin kamar noma da sauran wasu sana’o’i.

 

Haka kuma an bayyana addinin mutanen garin shi ne musulunci, amma sanadiyar zuwan baƙi an samu addinin masihiyya (Kiristanci) da mabiya addinin gargajiya. Bayan waɗannan an bayyana zuwan Yarbawa garin tun a (1920) da wasu lokuta mabambanta. Kuma an bayyana mu’amularsu da Hausawan Gusau tare da bayyana tasirin harshe da al’adun mutanen Gusau ga Yarbawa, kamar auratayya, sakatufafin Hausawa da Sauransu.

 

Babi na huɗu mai taken Ingausa an bayyana ma’anar harshe daga masana daban –daban, kuma an kalli harshen Hausa da Hausawa, tare da duban abokan zaman su Yarbawa da harshensu. Bugu da ƙari an bayyana ma’anar ingausa daga masana daban- daban, tare da kawo dalilan da ke haifar da ingausa kamar zaɓen kalmomi da sauransu. Haka an kawo amfani da illolin ingausa ga harshe. Bayan waɗannan an bayyana sakamakon binciken ta hanyar kawo misalign wasu jumlolin ingausar Yarbanci da Hausa cikin jadawali.

 

Babi na biyar mai taken “taƙaitawa” ya tattauna abubuwa kamar taƙaitawa, hasashen bincike, da ta’arifin wasu kalmomi da kuma naɗewa a ƙarshe.

 

5.2 HASASHEN BINCIKE 

An yanke shawarar gudanar da wannan bincike mai taken “Ingausar Yarbawa da Hausawa a garin Gusau” a matsayin wani hasashe na fitowa da tasirin da harshen Hausa ya yi ga Yarbawan garin Gusau, tare da aza batun a faifan nazarin harshe domin samar da abubuwan dubawa ga ɗalibai ‘yan’uwa da ma’abota bincike a kan harshe.

 

Haka kuma ana hasashen wannan bincike zai iya zama ƙofa ga masu nazarin harshe, inda za a iya kallon ingausar a wasu harsuna da ba Hausa da Yarbanci ba, ko kuma Hausa da Yarbanci a wata siga da ba wannan ba. Kamar ingausar Yarbanci a cikin waƙoƙin Hausa na zamani da sauransu.

5.3 TA’ARIFIN WASU KALMOMI

Ta’arifi ararriyar kalma ce daga harshen Larabci, wadda take nufin fito da ma’anar abu. A wannan bagiren za a fito da ma’anar wasu kalmomi ne na Yarbanci da aka yi amfani da su a cikin sakamakon binciken. Za a bayyana su a cikin jadawali kamar haka:

S/N

YRB

HAU

1.                  

Bami

Bani

2.                  

Gbe

Ɗauki

3.                  

Mode

Na zo

4.                  

Mofe

Ina so

5.                  

Tuntun

Sabo

6.                  

Mi

Ni

7.                  

Ni

Shi/kai

8.                  

Wo

Kallo

9.                  

Oni

Ba ka da

10.              

Aso

Tufafi

11.              

Odi

Sai

12.              

Oro

Magana

13.              

Omo

Wannan/wancan

14.              

Adugbo

Shiya/Unguwa

15.              

Obe

Miya

16.              

Monlo

Zan je

17.              

Iyawo

Amarya

18.              

Arewa

Kyakkyawa (Mace)

19.              

Yami

Aro mini

20.              

Jade

Fita

21.              

Funmi

Bani/ Sayo

22.              

Oti

Giya

23.              

Moje

Na ci

24.              

Olulufemi

Abin ƙaunata

25.              

Kosi

Babu

26.              

Tori

Saboda

27.              

Ana

Jiya

28.              

Omoge/Omidan

‘Yanmata

29.              

Dara-Lakunrin

Kyakkyawa (Namiji)

30.              

Age

Buta

31.              

Ose

Sabulu

32.              

Eko

Kunu

33.              

Omitutu

Ƙanƙara

34.              

Funfun

Fari

35.              

Elubo

Gari

36.              

Amun

Tulu

37.              

Ife

Kofi

38.              

Kanga

Rijiya

39.              

Oba

Sarki

40.              

Oluko

Aji

41.              

Gba

Karɓa/ansa

 

5.4 NAƊEWA

Daga ƙarshe za a ƙara jaddada godiya ga Allah (SWA) da ya bada ikon kamala wannan aikin, da fatar zai zama wata muhimmiyar gudummuwa a fagen ilimi wadda da ba a samu ba.

 

Wannan babin kammalawa ce ta aikin da aka gudanar a kan ingausar Yarbawa da Hausawa a garin Gusau. Babin ya yi bayani a kan abubuwa kamar; Shimfiɗa, da taƙaitawa game da aiki da aka gudanar, haka kuma an bayyana hasashen binciken, bugu da ƙari da ta’arifin wasu kalmomin Yarbanci zuwa Hausa, daga ƙarshe da naɗewar aikin baki ɗaya.

MANAZARTA

Tuntuɓi Amsoshi.

Post a Comment

0 Comments