Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Bilicin

Waƙar gyara-kayanka ga yanmatan zamani da suke burshine fuskarsu da kayan kwalliya, da sunan ado.

Mai Bilicin

 BINYAMIN ZAKARI
(ABULWARAKAT AYAGI)
DAGA KUNDIN RUBUTATTUN WAKOKI NA “TABA-KA-LASHE”
07082460196
abulwaraƙatayagi3@gmail.com

Budurwa
 

1. Wai mafarki ne nake yi?

Duniyar na ga ta yi sauyi

Ga ni baƙo mai kaɗaici.

 

2. Na yi war haka duk a mata

Ba baƙaƙe ai a fata

In ka ƙirga sun karanci

 

3. Sai farare har yalaye

Fatsfatsi duk sun ka juye

 Sun fa ɗauki ragon azanci

 

4. Masu fuskoki kaloli

Masu yin tafiya slowly

Ba ku burge mai mutunci

 

5. Har da mai siffa ta jinnu

Ko ko dodanni da shanu

Har da masu adon tsiraici

 

6. Dan uwa wata in ka ganta

Ba ka gane salsalarta

Shin mutum, dangin kumurci?

 

7. Mai bilitin ga ni ga ki

Me ya sa kika ɓata kanki?

Ɗan gaya min daina ƙunci

 

8. In miji kika so da wannan

Ba ki samu sai irin nan

Mai baƙar cuta a zuci

 

9. In kikai wanka ya gan ki

Sai ka ce tayar Suzuki

Sai saki ko ko fatauci

 

10. Rabbi ya ƙimanta kowa

In ya so ko da a giwa

 Sai ya yi ki kalar habaici

 

11. Kin ga duk wata kwalliyarki

Shafa mai, gwalli, adonki

Ba ki dawowa mutunci

 

12. Mai bilitin ai da kyanki

Kin ka zaɓi ki ɓata kanki

Kar ki haike wa haramci

 

13. Shi baƙin in dai da wanka

Ya wuce a gani a tanka

Ko a ƙauye babu faci

 

14. ‘Yar uwa Ka’aba, idonki

Ko wata da baƙi, jikinki

Har a gashi babu ƙunci

 

15. Ga farin zabiya da kyandir

Ko na yadi, jan tumatir

 In kina so mai butulci

 

16. Yadda Rabbu ya so ganinki

Ya fiye miki duk baƙinki

In akwai kyawu a zuci

 

17. Ga shi amma kin yi raini

Kin yi aikin nuna muni

Kyau na kantin kasuwanci

 

18. Kin asarar dukiyarki

Duk a saɓon Khaliƙinki

Ba ki burge mai azanci

 

19. Ba ki burge maza gaba ɗai

Sun fada ɗai-ɗai da ɗai-ɗai

 Ba su ƙaunar mai tsiraici

 

20. Ni maza sun ba ni saƙo

Zan isar na haɗa da roƙo

Sai ki karɓa mai karamci

 

21. Sun ka ce na gaya wa mata

Mayuka, hoda ta fata

 Sun sani har ma A-cuci

 

22. Ba a cutar mai tunani

Sai fa gaula jinni-jinni

 Ko ko dolo mai garanci

 

23. Wai a kayan kwalliyar ma

Har da cuta kun ka sama

Sai glass a ido da faci

 

24. Zamani ne, na ji amma

In da saɓo kar ki kama

 Kar ki wa Allah butulci

 

25. Ni kirana ai yi wanka

Kwalliya a haɗa da sarƙa

 Ba bilitin, gyara zuci

 

26. Kar ki zam bususu ya jaka

Dingiringingin ya jarka

Sai ka ce ke ce talauci

 

27. Mai bilitin zan tsaya nan

Kin sani ni tun a ran nan

Kishinki nake a zuci

 

28. Za ni goge wanga suna

Mai bilitin, ni kirana

 Don ki zamto ‘yar mutunci

 

29. Fa’ilatun, fa’ilatun

 Ga karin, kin san shi ma tun

 Can Aruli babu kunci

 

30. Bissalam ya ‘yar uwata

Na sani kuma kin fahimta

 Ni da ke sai dai zumunci

Post a Comment

0 Comments