Ticker

6/recent/ticker-posts

Ɗan Gaye

Hirar wani ɗan gaye da fasihin malami.

 Ɗan Gaye

BINYAMIN ZAKARI
(ABULWARAKAT AYAGI)
DAGA KUNDIN RUBUTATTUN WAKOKI NA “TABA-KA-LASHE
07082460196
abulwaraƙatayagi3@gmail.com

Dan gaye

Ɗan gaye hijabi mu yaye,       

Mui magana da kai kai ka waye.

 

Salamu alaika mai taje suma,   

Ban ‘yar two minute zan kiyaye.

 

Ya malam alaikassalamu,         

Ko ashirin ka so ba alaye.

 

Ka yo tsaf da an gan ka nawan,   

Kai ya cik kuɗi ya yi ƙaye.

 

Ai suma da ka gan ta ka san,

Ba yawa a birni da ƙauye.

 

Ga wandonka tamkar da fatar,    

Ya tsuke ka tamkar  na goye.

 

Fensir za ka ce ko suwaga,     

Ba mai sa shi sai in ya waye.

 

Da ai kun fi so yai balaulau,    

Nan ga ɗuwainiya sai ku yaye.

 

Juyin zamani ne a yanzu,           

Za ai dariya in kai ka juye.

 

Can a club da an gan ka kowa,     

Sai tafi ka danse da ƙaye.

 

Nan kwana yini, ko a yanzu,     

Kan harkar mutum kar ya janye.

 

Kana shafa’i idan har ka dawo,  

Ko nafilfili naf fiyayye?

 

Wanga batu ka basar, ka bar shi,  

Sai wataran batun kai musanye.

 

Ƙur’ani, yabo za ka kunnan,        

In addu’a ta jin ƙan iyaye?

 

Uhm uhm yanzu dai babu wannan,  

Sai music da raping na ƙaye.

 

To a wata kana yin karatun,      

Ƙur’an kad da haƙƙi ka tauye.

 

Kun ce bincike babu kyawu,    

Ku ne malamai kar ka ɓoye.

 

Ya Whatsapp da Instagram fa,      

Kai ko Facebook kai ka waye?

 

Babu awa da ba na taɓawa,          

Data ta kirawo ni maye.

 

‘Yan mata ka ce min suna shan,  

Kalmomi na so har ƙawaye.

 

Ai magana a miƙa wa Suda,         

Chatting sai ga mu kar ka tauye.

 

Ka san yaudara babu kyawu,   

Ga waccan da waccan ka janye.

 

Sun kai sha biyar ma a layi,      

Zaɓi zan na darje fiyayye.

 

An ce har kana shafe-shafe,     

Ko daudu kake so ka juye?

 

Hoda ce da ɗan mai ƙalilan,   

Too nice a showing , ahayye.

 

An ce an gano ka a camba,    

A loton karsashin shaye-shaye.

 

Shisa ce ka ƙara da others,

In an samu kodin a shanye.

 

Akwai cuta a kwalin sigari,     

Hukuma ta rubuta a sanye.

 

Kai kogo yake ai hayaƙi,        

Ya fi sinadari kai ya yaye.

 

Halayenka ni ba ni son su,        

Don haka bissalam za ni janye.

 

Malam yanzu kai min nasiha,   

Ko wa’azin hadisan Fiyayye.

 

Ka ji tsoronsa sarkin da yai ka,  

Don bauta ka bar jaye-jaye.

 

Duk aiki da zance hukunci,        

Sai ka bibiya ka kiyaye.

 

In ko ka ƙi ranar kiyayyar,         

Dillanci, da sharbar hawaye.

 

Sai mutuwa ta zo babu notis,    

Sai ƙabari a can za ka wanye.

 

Ita ko lahira babu rara,            

Gida biyu ce kamar ‘yan tagwaye.

 

Ga Aljanna sai mai nagarta,   

Sai fa Jahannamar masu maye.

 

Malam dakata ka tsumani,     

Kuma na tuba, gayun na janye.

 

Gun Tawwabu tuba ka miƙa,    

Bar kuka ka share hawaye.

 

Na gode a nan bissalami,       

Malam kai hijabin ka yaye.

Post a Comment

0 Comments