A cikin wannan takarda mai suna ‘Sharhin Waƙar Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’ ta Yahaya Bala Sama’ila Sauwa an yi sharhin waƙar ta fuskar babba da ƙananan jigogin da suka fito a cikin waƙar ta fuskar tallata ɗan takara a matsayin babba da kuma ƙanana da suka haɗa da yabo ta fuskoki daban-daban da habaici da zambo, kuma haɗi da addu’a. Takardar ta ci gaba da sharhin salailan da ke cikin waƙar da suka haɗa da kamancen fifiko da na daidaito da salon dabbantarwa da na abuntarwa da na aron kalmomin Larabci da na Turanci. Takardar ta kawo salon kinaya da kuma amfani da karin magana kamar yadda aka tsinta a cikin waƙar da aka yi sharhi mai suna ‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’ ta Yahaya Bala Sama’ila Sauwa.
Muhimman Kalmomi: Waƙa; Sharhi; Wutar Kara; Sauwa
Sharhin Waƙar
‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’ ta Yahaya Bala Sama’ila Sauwa
Dano Balarabe
Bunza (Ph. D.)
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
07035141980
1.0 Gabatarwa
Masana
da manazarta rubutattun waƙoƙin Hausa irin Hiskett (1975) da Furniss (1977) da
Abdulƙadir (1974) da Amin (2001) da Birniwa (1987) da Ɗangambo (1974) da Yahya (1982)
da Sa’id (2002) da Bunza (1994) da Yakawada (2002) da wasu da ba sai an ambaci
sunayensu a cikin takardar ba, sun yi nazari tare da sharhin waƙoƙin Hausa
daban-daban. Wasu daga cikinsu sun mayar da hankali ga waƙoƙin sarauta, wasu na
jama’a, wasu na sana’a, wasu na ban dariya, wasu kuma na siyasa kamar yadda
wannan takarda za ta yi sharhin waƙar siyasa mai suna ‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’
wadda Yahaya Bala Sama’ila Sauwa ya rubuta domin tallata ɗan takara, mai neman
kujerar gwamnan jihar Kebbi mai suna Ibrahim Muhammadu Mera Argungu (Chiroman
Kabi). Masana ba su bar waƙoƙin siyasa suddan ba tun daga na jamhuriya ta farko
zuwa yau face sun sami abin da suka yi tsokaci kansa dangane da jigo ko salo ko
zubi da tsarin wata waƙar siyasa daga cikin waƙoƙin da marubuta suka kattaba.
Jam’iyyun siyasa da ‘yan takara hajoji ne da ke buƙatar a tallata su ga jama’ar
da abin ya shafa saboda, siyasa jama’a ke yin ta kuma, abu ce da ke buƙatar a
tallata ga jama’a. A sanadiyyar tallar ce jama’a ke amincewa da jam’iyya da ɗan
takaran da ake talla. Kamar kowace sana’a, siyasa sana’a ce ga wasu mutane domin
da ita suke samun abin yin lalurorinsu. Wasu mutane ba su iya kowace sana’a ba
face siyasa. Takardar za ta bayyana abin da aka tsinta a cikin waƙar, mai alaƙa
da sharhin da aka yi na jigo da salo. A cikin sharhin da za a yi, za a yi
sharhin jigo (babban saƙo) tare da tubalan da aka gina shi da su (ƙananan saƙonni)
da kuma salailan da marubucin ya yi amfani da su a cikin waƙarsa. Babu shakka
maganar Yahaya ta raɗa wa waƙar suna gaskiya ce cewa, wutar kara izan masu ɗiya
ce domin, izan wutar kara ba a ɗagawa ga murhu. Idan aka ɗaga aka bar wutar
kuwa, ƙarshen wuta mutuwa.
2.0 Taƙaitaccen Tarihin Yahaya Bala
Sama’ila Sauwa
An
haifi Yahaya Bala Sama’ila Sauwa a garin Sauwa ta Ƙaramar Hukumar Mulkin
Argungu da ke cikin masarautar Argungun jihar Kebbi ranar Larba a shekarar
1982. Yankakken sunansa Yahaya, Bala kuma laƙabi ne da ke nuna ranar da aka
haife shi wato, wanda aka haifa ranar Larba. A ɗayan ɓangaren kuma, Sama’ila
sunan yayansa ne. Sunan mahaifinsa Muhammadu Lawwali, sunan mahaifiyarsa
A’ishatu Lawwali. Asali Lawwali Babarbare ne ta ɓangaren iyayensa, Hali da
Zainab kuma su ne kakannin Yahaya na ɓangaren uwa. Sunan mahaifan mahaifin
Yahaya su ne, Ɓaidu da Barinda (waɗanda Yahaya ke matsayin jika gare su) kuma
Barebari ne. Wannan ya tabbatar da cewa, Yahaya Babarbaren asali ne kuma,
Bakabe a ɓangaren mahaifiyarsa. A wannan shekara ta 2020 Yahaya na da shekara arba’in
da biyu a duniya.
An
sanya Yahaya makarantar firamare ta garin Sauwa (Sauwa Model Primary School) a
shekarar 1988. Bayan ya kammala karatunsa na firamare a 1994 ya zarce zuwa
makarantar sakandare ta garin Kamba (G.S.S. Kamba) a shekarar 1994 kuma ya
kammala a shekarar 2000. Yana ƙare karatun sakandare sai ya wuce zuwa School of
Nursing Sokoto daga 2001 zuwa 2004. Yahaya ya fara aikin gwamnati a shekarar
2005 a asibitin Sir Yahaya da ke garin Birnin Kebbi har zuwa 2009. Daga nan ya
sauya wurin aiki zuwa Jami’ar Fasaha da Ƙere-Ƙere ta garin Aliero a shekarar
2009. Ya yi aiki a asibitin jami’ar na tsawon wata uku zuwa huɗu. Yahaya ya
koma asibitin gwamnatin tarayya da aiki (Federal Medical Centre) da ke Birnin
Kebbi bayan baro Aliero a 2009. Ana cikin haka shugaban wurin ya ba shi damar
zuwa ƙaro karatu a makarantar da ke garin Kware ta jahar Sakkwato. Ya ɗauki
tsawon shekara biyu yana karatun ƙaro ilmin kula da masu taɓuwar hankali a
Kware daga 2013-2014. Tun ƙare karatunsa yana nan yana aiki tare da F.M.C.
Birnin Kebbi har zuwa yau (2020).
Allah
ya ƙaddari Yahaya da yin aure a shekarar 2007, sunan matarsa Malama Hadiza
Labaran Kalgo. A halin yanzu yana da ‘ya’ya uku, mata biyu (Zainab da Ummul
Aiman) da namiji ɗaya (Muhammadu Auwal). A fagen rubuta waƙa Yahaya bai gada ga
kowa ba, ta ɓangaren mahaifansa. Baiwa ce da Allah ya ba shi domin shi Allah mai
yin yadda ya so ne. Yahaya ya fara rubuta waƙa a shekarar 2004, idan ya rubuta
yakan ba wasu sautin da yake son su rera sai dai ba su gamsar da shi yadda yake
buƙata. Ganin ba a rera waƙoƙin yadda yake buƙata ya sa ya fara rerawa da kansa
a shekarar 2007. Waƙoƙin Yahaya ba su yi fice sosai ba sai da aka fara siyasar
ANPP da PDP a shekarar 2009. Kafin wannan lokaci ya rubuta waƙoƙi masu yawan
gaske. Yanzu haka ya rubuta waƙoƙin da suka fi ɗari ɗaya. Shi kaɗai ke rubuta
waƙoƙinsa ba tare da kowa ba, duk da yake yana da mai taimaka masa a salon
kama-in-kama lokacin rerawa. Sunan mai taya shi rerawa, Zuwaira Sama’ila Kano
sanannar mai rera waƙoƙin nan tare da Kabiru Classic. Haka kuma, duk lokacin da
Yahaya ya rubuta waƙa zai rera waƙarsa ya watsa cikin al’umma sannan, Kano yake
zuwa ya rera tare da mai taimaka masa, daga baya ya komo gida. A can ma studio
(ɗakin rerawa) suke shiga su rera. A halin yanzu Yahaya na daga cikin mutane huɗu
da ke rera waƙoƙinsu ta hanyar kama-in-kama duk da yake mai kama masa ba ta da
ko kalma ɗaya ta kanta a cikin waƙar sai rerawa kaɗai. Bayan shi akwai Kabiru
Classic da wani ɗan jahar Zamfara mai suna Kabiru Birnin Magaji da Habibu Bakura.
Yahaya na tsage gaskiya komai ɗacinta ya faɗa a cikin waƙoƙinsa kamar yadda ya
yi a cikin waƙar Chiroman Kabi da takardar za ta yi sharhi a kanta. Haka kuma,
yana daga cikin mawaƙan siyasar jihar Kabi ko arewacin Nijerya baki ɗaya,
musamman idan aka yi la’akari da irin salon rera waƙa na zamananci da yake
amfani da shi mai suna kama-in-kama da amshi a cikin waƙa, wanda a da abin ba haka
yake ba.
3.0 Tarihin Waƙar
Tarihin
da za a kawo na waƙar shi ne wanda mawaƙin ya faɗa da bakinsa kafin rera ta. Ga
abin da ya ce: “Assalamu alaikum al’ummar jahar Kebbi baki ɗaya. Ga Yahaya Bala
Sama’ila Sauwa ɗauke da wata sabuwar waƙa mai suna ‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’.
Na yi wannan waƙa ne zuwa ga Alhaji Ibrahim Muhammadu Mera wato, Chiroman Kabin
Argungu, mai neman tsayawa takarar kujerar gwamnan jahar Kebbi 2019. Ina miƙa
godiya ta musamman zuwa ga Alhaji Abu Hali tare da tallafawarshi na yi wannan
waƙar. Don neman ƙarin bayani sai a kira ta lambar waya kamar haka:
08068076503, a yi ta sauraro lafiya”. Abin da zan ƙara kaɗai shi ne, mawaƙin da
ɗan takarar masarauta ɗaya suka fito. Saboda haka, ina da fahimtar zuma ce ta
yi wa kanta zaƙi a cikin waƙar. Haka kuma, takardar na da fahimtar cewa, da
lauje cikin naɗi ko kuma, mawaƙin ya yi nuni da cewa, yaƙin mutum gaban
sarkinsa. Wannan ya faru saboda ɗan takarar basarake ne ga mawaƙin kuma, ƙasa ɗaya
suka fito. Wannan ne dalilin da takardar ta hango na faɗin wannan maganar cewa,
zuma ce ta yi wa kanta zaƙi.
4.0 Sharhin Jigo/Saƙon Waƙar ‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya
Kowace
waƙa na da saƙon da take ɗauke da shi da marubucinta ke son ya isar ga al’umma.
Saƙo iri biyu ne, kamar yadda bayani ya gabata. Akwai babba da kuma ƙarami ko ƙanana
a cikin waƙoƙi da dama. Kowace waƙa na ɗauke da babban saƙo ɗaya, sauran saƙonni
kuma su kasance ƙanana. Ana kiran babban saƙon da waƙa ke ɗauke da shi, babban
jigo ko muhimmin saƙo. Su kuma ƙananan jigogi ana kiran su ƙananan saƙonnin da
waƙa ke ɗauke da su ko tubalan ginin saƙo.
Babban
jigo ko saƙon waƙar ‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’ shi ne tallar ɗan takara. Mawaƙin
ya faɗakar da mutane manufofi da halayen ɗan takaran ta fuskar tallata shi gare
su. Dangane da ma’anar faɗakarwa an sami masana da dama sun tofa albarkacin
bakinsu dangane da fahimtarsu na waƙa. Kafin ci gaba, za a kawo ma’anar jigo
kafin ta talla domin jin abin da masana suka ce.
4.1 Ma’anar Jigo da Talla
Masana
da yawa sun bayyana ma’anar jigo yadda suka fahimce shi sai dai za a taƙaita
kawo na kaɗan daga cikinsu. Daga cikinsu akwai wanda ya ce “Abin da ake nufi da
jigo shi ne saƙo, manufa, ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a
kai” (Ɗangambo, 1981).
Daga
cikin masanan wani kuma cewa ya yi “Jigo a fagen waƙa yana nufin saƙo ko manufa
ko bayani ko ruhin da waƙa ta ƙunsa wanda kuma shi ne abin da waƙar ke son
isarwa ga mai sauraro ko karatu ko nazarin ta, (Yahya, 2001).
A
wani wuri kuma, cewa aka yi, “jigo shi ne saƙo na musamman da marubuci ke ƙoƙarin
bayyana wa jama’a a ƙagaggen labari ko wasan kwaikwayo ko waƙa, (Ƙamusun Hausa,
2006:217)”.
Talla
kuma na nufin (i) yawo da kaya don sayarwa (ii) rubuta bayanin wani abu a
jaridu ko maƙalu ko takarda a bango ko jikin wani abu, don neman mai saye (iii)
bayyana sirrin wani (Ƙamusun Hausa, 2006:423).
A
fahimtata, talla na nufin yawo da abin sayarwa kowane iri da bayyana amfaninsa
da ingancinsa na gaskiya ga al’umma ba tare da bayyana aibinsa ba, wani lokaci
har da sukar hajar wasu.
Bayan
haka, ya dace a bayyana abin da siyasa ke nufi ganin tallar da ake magana ta siyasa
ce. A wani wuri cewa aka yi (i) siyasa na nufin tafiyar da al’amurran jama’a ta
hanyar neman ra’ayinsu da shawarwari da su (ii) rangwame musamman a ciniki
(iii) dabara ko wayo (iv) iya hulɗa da jama’a (Ƙamusun Hausa, 2006:397).
Ga
abin da wani ya ce dangane da ma’anar siyasa: “Siyasa wata hanya ce ta gudanar
da zaɓaɓɓiyar gwamnati ta hanyar dimokaraɗiyya a ƙarƙashin tsarin mulkin ƙasa,
inda za a zaɓi shugabanni masu tafiyar da ita a ƙarƙashin kafaffun jam’iyyu”
A
fahimtata, siyasa na nufin sha’anin gudanar da shugabancin al’umma da mutane ke
zaɓar wa kansu waɗanda suke buƙatar su mulke su bisa amincewarsu, ba tare da an
tursasa musu ba. Haka kuma ana iya cewa, siyasa sha’anin mulki ne na farar hula
inda mutane ke zaɓar shuwagabanninsu ta hanyar jefa musu ƙuri’a, da ra’ayinsu
ba tare da an sayi ƙuri’un ko satar su ba, idan har za a bi ƙa’idar zaɓe.
4.1Jigon Tallar Ɗan
Takara
A
sha’anin siyasa jam’iyya da ɗan takara hajoji ne da ake tallar su ga jama’a
domin neman goyon baya a lokacin da ake gudanar da kamfen. Babban jigo/saƙon waƙar
“Wutar Kara Izan Masu Ɗiya” shi ne Talla. Tallar kuma ba ta wata haja ba ce
face ɗan takarar matsayin gwamnan jihar Kebbi. Haka kuma, ɗan takaran da ake
nufi shi ne Ibrahim Muhammadu Mera Argungu (Chiroman Kabi) ɗan takarar gwamnan
jihar Kebbi a shekarar 2019. A cikin tallar, mawaƙin ya tallata shi da wasu
kyawawan manufofi da halaye a cikin waƙarsa. An tsinci hakan a cikin wasu
baitoci kamar haka:
Sallama
nikai al’umma na jaha tamu, ga ni nan da sabon launi kun ji ni,
Yahaya
Sauwa ne da Zuwaira ta Kanon Dabo, za mu aika saƙon waƙa don nuni,
Abin
da zan faɗi ban sa son raina ciki ba, gwargwadon fahimta ku tsaya ku yi auni,
Rashin sani ka sa kaza kwana bisa
damma, safiya ta waye ta yi ƙwacen tsaba.
Ga
Chiroma Ibrahim nan mai adalci, ya fito mu taru mu goya bayanshi,
Cigaban
jihar Kebbi shi ne manufa tashi, wanda bai sani ba ka shakkar halinshi,
Bai
shigo siyasa don tara kuɗaɗe ba, tausayi wajen al’umma halinshi,
Taimako yake yi can baya ga al’umma,
bai yi don siyasa da gwadin girma ba.
A
baitin farko da aka kawo, layi na biyu mawaƙin na nufin saƙon waƙarsa shi ne
nuni mai nufin tallar ɗan takara. A baiti na biyu kuma, mawaƙin ya fara faɗin ɗaya
daga cikin halayen ɗan takaran, wato adalci mai nufin adili ne ba azzalumi ba.
Biye da wannan a layi na biyu ya kawo manufar ɗan takaran ta buƙatar kawo cigaba
a jihar Kebbi ba mayar da ita baya ba. Wata manufa ta bayyana a layi na uku ta
cewa ba ya da manufar cin amanar jama’a don ya tara kuɗi, a’a. Ya shigo siyasa
da manufar samar da cigaba ba zaluntar al’umma ba kamar yadda bayani ya gabata
a layi na biyun baiti na biyu da aka kawo. A cikin layi na uku har yanzu, mawaƙin
ya ƙara tallata ɗan takarar da cewa tausayin al’umma na daga cikin halayensa.
Domin tabbatar wa al’umma gaskiyar manufofi da halayen ɗan takaran da aka
bayyana a cikin baitin, mawaƙin cewa ya yi a layi na ƙarshe, taimakon al’umma
halin ɗan takaran ne domin tun babu siyasa yake taimakon al’umma kuma, bai yi
saboda shigowa siyasa ko nuna na isa ba. Saboda haka, ana iya cewa, taimakon
al’umma tamkar hali ne zanen dutse ga ɗan takaran. Ga wasu baitoci kamar haka:
Chiroma
ɗan sarauta ne bai iya ƙarya ba, du’ abin da ya ce shi ne manufarshi,
Wanga
lokaci kan talakawa ya waye, wanda bai da halin kirki mun bar shi,
Chiroma
ka zamo ɗan gatan masu siyasa, jiharmu ba ka ƙullin sheri sai kishi,
Chiroma bai da girman kai don matsayi
nashi, wanda ya’ ishe shi da fara’a ya tarba.
Chiroma
na da ilmin boko da na addini, mai yawan ibada mai tsoron Allah,
Mai
sanin mutuncin jama’a ne ɗan zaki, ba ya nuna ƙyamar jama’a don daula,
Wanda
duk ka hulɗa da Chiroma yana shaida, zantukanshi babu baɗala ko illa,
Kowane irin matsayi Chiroma ka dace,
tunda adili kake ba mai zalun ba.
Kira
nikai wajen talakawa ku tsaya ku jiya, kar ku je ku faɗa rame don naira,
Ku
sa idon basira ku yi hangen ceton kai, mun daɗe muna shan wahala sun dara,
Za
su zo sunai muna ƙaryar ƙare dangi, tunda yanzu ga shi siyasa ta fara,
Ku zaɓi wanda ke iya share muku
kukanku, tunda kun gwada ba ku gane komai ba.
Baiti
na uku mawaƙin ya bayyana wa al’umma wani halin ɗan takaran da cewa ba maƙaryaci
ba ne kuma, hasali ma ɗan sarauta ne da aka san su da faɗar gaskiya komai ɗacinta
domin shi kam kalamun wahid ne halinshi. Mawaƙin ya faɗa cewa kan talakawa ya
waye, ba su zaɓar mai halin banza. Wani halin ɗan takaran shi ne, kishin ƙasa
don haka ba yadda za a yi a same shi cikin masu ƙulla wa wani sharri balle ƙasarsa.
Haka dai har yanzu an faɗi wani halin ɗan takaran da cewa, ba mai girman kai ba
ne domin mutumin mutane ne, babu tsangwama tsakaninsa da al’umma sai fara’a da
su a cikin al’amurran da ke tsakaninsu .
A
baiti na huɗu an nuna ɗan takaran ba jahili ba ne a fannin boko da karatun
addini, hasali ma, yana da tsoron Allah da yawan ibada domin neman yardar
Allah. Ya san darajar jama’a kuma ba ya ƙyamar kowa domin ganin ya sami ɗaukaka
fiye da su, domin mai ilmi ne ba jahili ba. Haka kuma ba mai maganganun banza
ba ne (baɗala). Mawaƙin ya faɗi cewa Chiroma ya dace da kowane matsayi domin
adili ne ba azzalumi ba.
Har
yanzu, dangane da tallar ɗan takaran mawaƙin ya yi kira ga talakawa cewa, kar
kwaɗayi ya ja su su zaɓi mai zaluntar su. Ya ce jama’a su tsaya su yi aiki da
basirarsu domin su ceto kansu daga cutar da aka daɗe ana yi musu, kuma kar su
koma aminta da ƙaryar da ake yi musu da rantse-rantsen banza da babu gaskiya a
ciki, musamman idan siyasa ta zo. Ya ƙara da cewa, mafita ita ce, su zaɓi mai
share musu hawaye daga koke-kokensu, kar su koma ga turke mai caɓo (kar su ƙara
zaɓar masu zaluntar su), saboda sun sha zaɓe ana cin amanarsu. Idan aka dubi
baitocin da aka kawo a sama babu shakka akwai tallar ɗan takara a ciki ta fuskar
faɗar halayensa na kirki da manufofinsa na alheri. Babu shakka haja ta tallatu
kuma, sai a ce wa al’umma, da rashin sani akan bar araha.
4.2 Ƙananan Jigogi/Saƙonnin Waƙar
A
nazarin waƙa ƙananan saƙonni su ake kira tubalan ginin jigo. Akan sami wasu saƙonni
a cikin waƙa bayan babban saƙon da take ɗauke da shi. Ita ma wannan waƙa na ɗauke
da ƙananan saƙonni da ke zaman ‘yan rakiya ga babban saƙonta. Ga ƙananan
jigogin da aka gano a cikin waƙar kamar haka:
4.2.1 Yabo Ta Fuskar Addini
Yabo
na nufin faɗar wata kalma mai daɗi ga wani mutum da ya aikata wani kyakkyawan
abu. Misali mutane na yabon mutum saboda wani taimako da ya yi musu. (Ƙamusun
Hausa, 2006:476). Duk da haka ina da
fahimtar cewa yabo na nufin furta daɗaɗan kalmomi zuwa ga wani ko wasu a
sanadiyyar soyayya ko wani abin a zo a gani da ya aikata da ke nuna halinsa na
kirki.
Addini
kuma na nufin hanyar bauta wa ubangiji (Ƙamusun Hausa, 2006:3). Addinin da
wannan takarda ke nufi shi ne na Musulunci da ke nuna ɗan takarar musulmi ne.
Mawaƙin ya yi yabo ga ɗan takaran, yabon da ya dace da shi ta fuskar riƙo ga
addini gwargwadon hali tare da bin karantarwar Musulunci sawu da ƙafa. Ga abin
da sha’irin ya ce:
Chiroma
na da ilmin boko da na addini, mai yawan ibada mai tsoron Allah,
Mai
sanin mutuncin jama’a ne ɗan zaki, ba ya nuna ƙyamar jama’a don daula,
Wanda
duk ka hulɗa da Chiroma yana shaida, zantukanshi babu baɗala ko illa,
Kowane irin matsayi Chiroma ka dace,
tunda adili kake ba mai zalun ba.
Chiroma
duniya ba ka ɗauke ta da girma ba, ka san rashi da samu Allah yay yi su,
Kai
ba irin waɗanda ka nuna isar banza ba, in sun shigo cikin al’umma a gane su,
Waɗansu
‘yan siyasa ba su da tsoron Allah, sun ɗau talakka tamkar bola a wurinsu,
Amma da lokaci na siyasa ya kankama,
sai ɗai su zo da su aka yawon gararamba.
Tun
farko a baitin da aka kawo mawaƙin ya faɗi cewa, ɗan takaran mai ilmin zamani
ne da na addini kuma, mai tsoron Allah ne. Ya san mutuncin jama’a, yana
darajanta su ba tare da ƙyama ba. Duk maganganunsa na hikima ne ba na wulaƙanta
jama’a ba, hasali ma adili ne wanda ba mai zaluntar al’ummarsa ba. A baiti na
biye mawaƙin ya faɗi cewa ɗan takaran bai ɗauki duniya bakin komai ba saboda ya
san samu da rashi daga Allah suke, ba kamar wasu ‘yan siyasa marasa tsoron
Allah, masu wulaƙanta talakawa ba. A cikin baitocin da ke sama guda biyu akwai
yabo ta fuskar addini da mawaƙin ya yi zuwa ga ɗan takaran da ya yi wa waƙa.
4.2.2 Yabo Ta Fuskar
Halayen Kirki
Akan
yabi mutum da halayensa na kirki, su kuma halayen banza sukar sa ake da su ta
hanyar yi masa zambo. Wanda aka yaba da halayen kirki farin ciki yake yi, wanda
kuma aka zarga da rashin kirki damuwa yake samu da ɓacin rayuwa. Yahaya ya yabi
ɗan takaran gwamnan jihar Kebbi na shekarar 2019 ta hanyar ambaton sa da
halayen kirki kamar haka:
Chiroma
na da ilmin boko da na addini, mai yawan ibada mai tsoron Allah,
Mai
sanin mutuncin jama’a ne ɗan zaki, ba ya nuna ƙyamar jama’a don daula,
Wanda
duk ka hulɗa da Chiroma yana shaida, zantukanshi babu baɗala ko illa,
Kowane irin matsayi Chiroma ka dace,
tunda adili kake ba mai zalun ba.
Mai
taimakon marayun Allah ba ka nadama, halinka ba irin na katangan kasko ba,
Ka
tallafa wa mai ciwo har da maras ciwo, in ba ka nan jihar Kebbi wahala mun
diba,
Duk
wanda bai da gata fanni na biɗar ilmi, kai ne uwa-uba a gare su ka saba,
In ka shigo jahar Kabi naƙasassu na
murna, sun more arzikinka ina mai tambaba?
Mai
yawan ibada da tsoron Allah ya yi dace da halin kirki domin ana kyautata haɗuwarsa
da Allah za ta yi kyau. A sami mutum ya san mutuncin jama’ar da yake tare da su
kuma ba ya ƙyamar su hali ne mai kyau da kowa ke son a san shi. Haka kuma idan
aka sami mutum ba ya da maganar banza tsakaninsa da kowa, ana ganin mutuncinsa
saboda ba azzalumi ba ne, ya dace da halin kirki. Irin waɗannan halaye da aka
jero a sama cikin baitin su kowane mutumin kirki ke so ya kasance da su, sai in
so bai samu ba. Idan aka ce mutum mai taimakon jama’a ne halinsa na kirki ne,
balle a ce marayu yake taimaka ma. Haka kuma yana taimaka wa marasa lafiya haɗi
da masu lafiya baki ɗaya. Haka kuma shi ne gatan duk maras gata a fannin neman
ilmi, wato shi ne matsayin mahaifi ga marasa gata domin ya ɗauke lalurar
karatunsu baki ɗaya. Gajiyayyun jihar Kebbi har farin ciki suke yi idan ya
shigo jiha sanin irin tallafin da yake ba su kuma, wannan bai zama abin musu ba
domin halinsa ne.
Wanda
duk aka samu da halayen da aka ambata a sama babu shakka halinsa na ƙwarai ne,
kuma mutane na murna da samun irinsa ya kasance shugabansu ba tare da fargaba
ba. Dangane da yabon ɗan takarar da halayen kirki har yanzu, ga abin da mawaƙin
ya ce:
Sarakunan
jihar Kebbi na goyon bayanka, sun tabbata akwai alheri zaɓo ka,
Sun
ce idan kana nan ba za su bi kowa ba, don taimako kakai a gare su sun san ka,
Inuwar
da ba ta ƙyamar kowa baban Ansar, duk wanda yat taho zai huta a cikinka,
Ka
taimaka ma mai hali har da maras hali, mai arzikin da bai ci amanar kowa ba.
Wanda
sarakunan jiha baki ɗaya suka tsaya kai da fata don goya masa baya saboda sanin
alherinsa ya isa mai halin ƙwarai da ya cancanci a sheda wa waɗanda ba su sani
ba domin su sani. Haka su tsaya kan bakarsu cewa ba za su goya wa kowa baya ba
sai shi saboda taimakon da yake yi musu ya tabbatar da mutumin kirki ne mai
halin da ake maraba da shi. A nan ana iya fahimtar Chiroma mutumin kirki ne kuma
mai halin kirkin da al’umma ke nema ruwa a jallo ya shugabance su a cikin
al’amurransu. Hausawa sun ce shedun duniya shi ne na lahira. Don haka, shedar
da mawaƙin ya yi wa ɗan takaran da ta sarakuna da naƙasassu da marasa gata da sauransu
ya kasance sheda ga ambaton da aka yi masa da halin kirki. Wannan ya yi daidai
da karin maganar da Hausawa suka ce, “Na gari na kowa, mugu sai uwar da ta
haife shi”. Saboda haka Chiroma na kowa ne ba ya da bare a wurinsa.
4.2.2 Yabo Ta Fuskar Jaruntaka
Akan
yabi mutum mai jaruntaka kuma a lokaci ɗaya a kushe raggo. A fahimtata,
Jaruntaka na nufin tsayawa kai da fata domin ganin an cimma duk buƙatar da aka
tunkara ta hanyar amfani da ƙarfi da ƙarfe. Ana iya cewa, jaruntaka na nufin yin
fice ta hanyar samun nasara ga dukkan ƙalubalen da aka haɗu da shi, idan kuma
na kokawa ne, a sami mutum shi ya yi kaye ba shi aka kayar ba. Mawaƙin ya yabi ɗan
takaran ta fuskar jaruntaka a cikin amshin waƙarsa kamar haka:
Dogaronka
Allah zaki ɗan zaki,
Ga Chiroma
nan Ibrahim na gidan Mera,
Ko alama
ba ya da shakkar artabu,
Yanzu
dai jahar Kebbi ba gwarzo bayanka,
Kai
muke kira ka yi gwamna ka dace,
Baban
Khalifa baban Ansar ba mu da shakka,
Mai
riƙon amanar jama’a ka saba.
Abin
da aka kawo a sama amshin waƙar ne. A layin farko aka fara tabbatar da ɗan
takaran jarumi ne saboda kiran sa zaki kuma ɗan zaki. Hausawa na yi wa zaki
kirari da cewa “Zaki mai ƙashi guda don ƙarfi” kuma, ana ce masa manyan dawa.
Bayan haka ana yi masa kirari da”Zaki mai kashe wa kainai nama”. Kiran ɗan
takaran zaki ya nuna jarumi ne inda a layi na uku aka ƙara tabbatar da
jaruntakar da cewa, ko alama ba ya da shakkar artabu. Idan aka ce artabu ana
nufin yaƙi ko faɗar da ba a san kanta ba. A fagen artabu ana amfani da kowane mugun
makami wanda mutum ya sani da wanda bai sani ba. Don haka idan aka ce mutum ba ya
shakkar artabu, ana nufin ba ya tsoron abokan karawarsa don haka, duk inda
jarumi ke kai ya kai. Mawaƙin ya ƙara da cewa, babu wani gwarzo a jahar Kebbi
bayan Chiroma, wanda a nan ma jaruntaka ce aka nuna. Ga wani baiti kuma:
Na
san kiɗan farauta na gane kiɗan yaƙi, Chiroma zaɓi wanda ya dace wajjenka,
In
ka yi kuskure ka ɗauki kiɗi na farauta, to ni Zuwaira zan saki layin bayanka,
Kamar
maza tana ga muzuru ke mai waƙa, na san Chiroma layin yaƙi zai ɗauka,
To tunda dai Chiroman Kabi ka gado
yaƙi, na so a mai da baya ta zan yau mu ci riba.
Mawaƙin
na magana da ɗan takaran cewa ya san kiɗan farauta kuma, ya san kiɗan yaƙi don
haka Chiroma ya zaɓi kiɗan da ya dace da shi a cikin biyun. Ya nuna idan ya
kuskura ya ɗauki kiɗan farauta ta bakin Zuwaira (mai kama masa rerawa) za ta
bar shi ta koma ga wani ɗan takara. Yahaya ya gaya mata cewa kamar maza na ga
muzuru, kuma ɗan takaran jarumi ne don haka ya san kiɗan yaƙi zai ɗauka ya bar
na farauta. A layi na ƙarshe ta ce, tunda Chiroma ya yi gadon yaƙi, ta so
zamanin da ya wuce na yaƙe-yaƙe ya komo yau domin su ci riba mai nufin su sami
rinjaye a kan abokan hamayya. Wannan wuri kaɗai ya isa a gano cewa akwai yabo
ta fuskar jaruntaka. Ga wani wuri har yanzu da jaruntaka ta fito kamar haka:
Yanzu
dai talakkawa ka faɗin ka dace, ko’ina kana da darajja ɗan zaki,
Chiroma
yanzu ka zama gwanki mai rangwangwan, a ja da kai a kwanta ɗaki a yi raki,
Ka ɗau
mutum ka ɗau kayanai ko bai so ba, angon Halima ba ka da shakka ko raki,
Sai ba ka nan maza suka ƙaryar nuna
bajinta, in ka fito kamar ba maganar sun kai ba.
A
layi na biyu da ke cikin baitin sama akwai yabo ta fuskar jaruntaka inda mawaƙin
ya kira Chiroma gwanki kuma mai rangwangwan. Rangwangwan asiri ne da ko abokin
faɗa ya taso zuwa ga wanda suke karawa kafin ya kai gare shi, faɗuwa ƙasa yake
yi. Haka kuma a layi na uku mawaƙin ya faɗi cewa Chiroma ba ya da shakkar komai
balle ya yi raki. Ƙare da ƙarau ma a layi na ƙarshe mawaƙin cewa ya yi, duk ƙaryar
da maza ke yi sai idan Chiroma ba ya nan ne. Idan ya fito kuma, sai su laɓe
tamkar ba su ce komai ba. Idan aka yi la’akari da wannan kaɗai ya isa a ce
Chiroma jarumi ne domin ya zama dodo sai raɗa. Wanda ya kai matsayin masu kiran
kansu ko waɗanda ake kira maza su yi maganar bugun gaba idan ba ya nan, idan
kuma ya zo su yi shuru kamar ba su ce komai ba, ya fi su jarunta, don haka an
sami yabo ta fuskar jaruntaka a cikin baitocin da aka kawo a sama ba tare da wani
musu ba.
4.2.3 Yabo Ta Fuskar Mulki
An
sami ganin kalaman yabo ta fuskar mulki zuwa ga ɗan takaran kamar yadda mawaƙin
ya shirya a cikin waƙarsa kamar haka:
Chiroma
yanzu kai ne Kanta kai ne Mera, duk
martabarsu na wajjenka sabbene,
Mai
kwarjini kama da daren salla ɗan zaki, manya da yara na ra’ayinka mun gane,
In
ka shigo mutane kowa sai ya tashi, ba wanda zai tare maka hanya ƙarya ne,
Ka gadi martaba da muhibba a gidan
mulki, ba mai buga ma bukka kwano na duba.
Akan
sami yabo ta fuskar mulki a cikin waƙoƙin siyasa kuma ba yanzu aka fara ba. Duk
lokacin da ɗan takaran da ke neman wani matsayin siyasa, akan ji a bakin mawaƙinsa
idan ya yi gadon mulki ko asali ta fuskar zuri’ar da ya fito. Idan aka sami
abokin karawarsa bai fito daga gidan mulki ba, za a ji a bakin mawaƙin da ake
hamayya da ubangidansa. Chiroman Kabi ya fito daga gidan sarauta har mawaƙin ya
danganta shi da kakanni da iyayensa a cikin waƙar da nuna tabbatacin hakan a
cikin waƙar. Haka kuma, mawaƙin ya faɗi cewa ɗan takaran na da martaba da
muhibbar gidan mulki, hasali ma, yana riƙe da matsayin Chiroman Kabi kafin
likkafa ta ci gaba wata rana. Babu ƙage balle ƙaƙale a cikin maganar mawaƙin
domin matsayin da yake riƙe da shi na Chiroman Kabi don kawar da tababa. Ɗan
takarar ɗan sarauta ne, har ma yana riƙe da matsayin Chiroman Kabi. Maganar ba
a kasuwa aka saya aka sanya masa ba, gado ya yi kamar yadda mawaƙin ya ambata.
Ke nan, an sami yabo ta fuskar mulki a cikin waƙar ‘Wutar kara izan masu ɗiya’.
4.3 Zuga
Zuga
na nufin harzuƙa ko tunzura wani ko hura shi (Ƙamusun Hausa, 2006:495). Akan
sami zuga a cikin waƙoƙin siyasa daga mawaƙan siyasa ta hanyar hura wani mutum
tunzura shi da wasu maganganun idan ya ji su, babu batun komawa baya sai dai ƙara
ƙaimi domin da ma ana yin zuga don ƙara wa mutum ƙwarin guiwa don ya yi wani
abu. An sami wani wuri da mawaƙin ya zuga ɗan takaran inda ya ce:
Na
san kiɗan farauta na gane kiɗan yaƙi, Chiroma zaɓi wanda ya dace wajjenka,
In
ka yi kuskure ka ɗauki kiɗi na farauta, to ni Zuwaira zan saki layin bayanka,
Kamar
maza tana ga mazuru ke mai waƙa, na san Chiroma layin yaƙi zai ɗauka,
To tunda dai Chiroman Kabi ka gado
yaƙi, na so a maida baya ta zan yau mu ci riba.
Chiroma
yanzu kai ne Kanta kai ne Mera, duk martabarsu na wajjenka sabbene,
Mai
kwarjini kama da daren salla ɗan zaki, manya da yara na ra’ayin ka mun gane,
In
ka shigo mutane kowa sai ya tashi, ba wanda zai tare maka hanya ƙarya ne,
Ka gadi martaba da muhibba a gidan
mulki, ba mai buga ma bukka kwano na duba.
…………………………………………………………………………………..,
Chiroma
yanzu kai muka dubi in ka shirya, tafiya da kai gwani ba wahalar banza ba.
A
cikin baitin farko da ke sama mawaƙin ya ba Chiroma zaɓin ɗaya daga cikin kiɗa
biyu, kiɗan farauta da na yaƙi. An sheda masa idan ya ɗauki kiɗan farauta ba a
tare da shi. Nan take mawaƙin ya ce babu shakka kiɗan yaƙi Chiroma zai ɗauka
domin ko ba komai, ya gadi yaƙi wajen kakanninsa har ya yi fatar a maido
lokacin yaƙi na da domin su sami nasarar kayar da abokin jayayyar ɗan takaransu
saboda an fi nuna bajintar yaƙi a zamanin da fiye da yau.
A
baiti mai bin na sama kuma, mawaƙin ya ci gaba da zuga ɗan takaran ta hanyar
cewa, shi ya maye matsayin Mera da Kanta domin martabobinsu sun komo wajensa.
Chiroma ya gadi martaba da muhibbobin gidan mulki, ba kamar abokin karawarsa
ba. A cikin baiti na ƙarshe ma akwai zuga wurin da mawaƙin ya ce, Chiroma yanzu
kai muka dubi in ka shirya domin tafiya da gwani ba wahalar banza ba ce. Kiran ɗan
takaran gwani zuga shi ne domin, nuna tafiya da shi ba wahala ba ne da mawaƙin
ya faɗa. A taƙaice, akwai zuga a cikin baitocin da aka kawo a sama kamar yadda
aka gani.
4.4 Zambo
Masana
da dama sun bayyana ma’anar zambo kamar yadda aka gani a cikin rubuce-rubucensu
inda waɗansunsu suka ce:
Kalmar
zambo tana nufin aibanta wani mutum ko wani abu dangane da sifarsa ko aƙidarsa,
ta yin amfani da wasu lafuzza na aibantawa ko muzantawa (Dunfawa, cikin Ɗunɗaye).
Wani kuma cewa ya yi, wasu kalmomi ne na muni da ɓata wa wani mutum muruwa da
ake amfani da su kai tsaye ga wanda ake buƙata, (Gusau, 1988). Shi kuma Ɗangambo
cewa ya yi,”Shi kuma zambo ba kamar habaici ba, zagi ne na kai tsaye, idan an
kwatanta shi da habaici. A cikin zambo ana siffanta mutumin da ake nufi da duk
siffofinsa, halayensa, ɗabi’unsa, danginsa, iyalansa da dai duk wani abu da ya
shafe shi wanda zai taimaka a gane da shi ake. Saboda haka idan aka yi maka
zambo, duk wanda ya san ka zai gane da kai ake. Babbar gaba, ita ce ke haddasa zambo
(Cikin Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa). Ga abin da
wani ya ce, “Zambo kishiyar yabo ne kuma a kaikaice yabo ne ga gwarzon waƙar da
ake yi. Mawaƙi kan ambaci wasu abubuwa na kasawa da wani ya yi domin cewa bai
kai tauri ko dambe ko kokawa ko satar gwarzon da ake yi wa waƙa ba, (Yahya,
1997).
An
sami wakanar abubuwan da masana suka bayyana game da zambo a cikin waƙar “Wutar
Kara Izan Masu Ɗiya” kamar haka:
…………………………………………………………………………………,
Wasko
na Jega bai yi halin ɗauki ga banza ba, Allah ya wa ragi albarka na gode,
Badamasi Augie Allah ya tsare ka ga
‘yan iska, magana ta gaskiya ba ta koma ƙarya ba.
A
taƙaice, kalmar ‘yan iska da mawaƙin ya yi amfani da ita zuwa ga wasu abokan
gaba, shi ne zambon da ya yi amfani da shi a cikin waƙar, da ya fito ɓaro-ɓaro
idan aka yi la’akari da abin da masanan suka bayyana. Ambatar mutum da abin da ba
ya so zagi ne, zagin mutumin da ake adawa da shi domin a muzanta shi cikin
jama’a kuwa shi ne zambo. Ba wannan kaɗai ne zambo da ke cikin waƙar ba amma,
shi ya fito fili fiye da sauran da ke akwai.
4.5 Habaici
Habaici
hanya ce da wasu mawaƙa suke amfani da ita domin su ƙasƙantar da wani mutum ko
kuma su muzanta shi, ko su zage shi, ko kuma su caka masa magana a fakaice
(Abba da Zulyadaini, 2000). An sami irin waɗannan maganganu a cikin waƙar
‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’ da Yahaya Sauwa ya yi ta Chiroman Kabi a lokacin da
ya ƙuduri takarar matsayin gwamnan jihar Kebbi a shekarar 2019. Wannan ya yi
daidai da maganar Hausawa da suka ce “Ba a rasa nono rugga”. Manufa, ba yadda
za a yi waƙar siyasa ba tare da an sakaɗa habaici a ciki ba, kamar yadda Yahaya
ya yi a inda ya ce:
…………………………………………………………………………..,
Karen
gida akwai rigima bai kashe ɓera ba, ƙarfin karan gado ya fi na sandag gwadda,
Ina
ganin ka ba ka gani na ɗan babule, mai jan faɗa ya ɓoye ai ba gwarzo ba.
Ga
rijiya tana ba da ruwa don ceton mu, guga tana hana muna ɗiba don sheri,
Baƙin
cikinki guga ya sa ki shiga ƙangi, mugun halinki ya hana igiya tasiri,
To
yanzu lokacin rankon gayya ya kama, ba wanda zai rage miki wahala sai ƙari,
Mai dundumi duhun hadari ya sa ka ɓoye,
mai ƙunzugu rage cuta ba don ni ba.
……………………………………………………………………………………….,
In
don ganin hurar wani bari tudda hura taka, ɗan ƙwaƙwale wutakka daban ce la
shakka,
Tafarnuwa ina son ki ina jin shakkun
ki, kowat taɓa ki ba zai yi rashin wari ba.
A
cikin baitin farko da ke maganar habaici an kira wanda ake yi wa habaicin karen
gida da bai taɓa kashe ko ɓera ba kuma an ce sandag gwadda ne saboda rashin ƙarfin
farin jini ga jama’a saboda bai kai abokin hamayyarsa karɓuwa ba. Bayan haka, an
kira shi matsoraci saboda duk lokacin da ya ja rigima, maimakon ya tsaya a
gwabza, ba ya yin hakan sai dai ya je ya ɓoye saboda tsoro. Matsoraci kuwa ba
ya taɓa zama gwani domin ko Dr. Alhaji Mamman Shata Katsina cewa ya yi:
Shata:
Mai tsoro ba ya gwaninta ko wane ne,
Kuma ko ɗan wa,
Allah ko,
Matsoraci ba ya zama gwani, ko wane ne,
To, to, to,
Amshi:
Alo-alo mai ganga ya gode,
Yaran mai ganga sun gode.
A
baiti na biyu an kira wanda aka yi wa habaicin ɗan sheri/masharranci ta inda
yake hana a yi wa al’umma alheri har aka kamanta shi da gugar da ba ta da
amfani a bakin rijiya, ko ana ganin ruwa ba a ɗebo su da ita ko ga igiya
lafiyayya. Duk abin da yake yi ana kallon sa, kuma yanzu lokacin ramuwa ya zo ,
ramawa za a yi ba tare da an tausaya masa ba kamar yadda ya ƙi tausaya wa
al’umma. Don haka babu batun rage wa guga wahala sai dai a ƙara mata ya kasance
sakamako ga abin da ta yi wa al’umma domin ita ma ta ji idan da daɗi. Haka kuma
mawaƙin ya nuna mutumin ba ya gani sosai saboda rashin lafiyar dundumi da yake
fama da ita. Ya ƙara da cewa idan hadari ya yi duhu sai ya nemi wuri ya ɓuya.
Ba wannan kaɗai ba, mawaƙin ya ƙara kiran sa macuci ta inda ya ba shi shawarar
ya rage cutar al’umma ba don kansa ba. A baiti na ƙarshe an kira shi ɗan ƙwaƙwale
(mai sanya hannunsa a gindin ƙananan yara mata), inda ya ce wutar da za a sanya
shi ta musamman ce. A taƙaice mai yi wa yara mata ƙanana da ake ce wa fingering da Turanci. Mawaƙin ya nuna ba
ra’ayin sa ne ba ya yi ba, a’a. Yana shakkun ya kasance halinsu na ƙwaƙwalar
yara ya zama ɗaya. Wannan ne dalilin da ya sa ya bar shi. Babu shakka duk
mutumin da aka kira kare, raggo, ɗan sheri (masharranci), ɗan baƙin ciki da sauransu
an yi masa habaici ba kaɗan ba. Wannan ya ƙara tabbatar da cewa, habaici na ɗaya
daga cikin ƙananan saƙonnin waƙar ‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’ da Yahaya Sauwa
ya yi wa Chiroman Kabi.
4.6 Addu’a
Addu’a
kalmar Larabci ce mai nufin roƙo ga wanda ake bauta Hausawa suka ara suna
amfani da ita da ma’anarta ta Larabci. A wani wuri cewa aka yi addu’a na nufin
roƙon ubangiji (Ƙamusun Hausa, 2006:3).
Dangane
da ma’anar addu’a an sami wani mai bincike ya ce “Addu’a tun asali kalma ce ta
Larabci wadda ke nufin ‘Da’autu fulan’ wato na kira wane, ina neman shi da ya
fuskanto ni. A cikin addinin Musulunci kuwa, sai ma’anar ta faɗaɗa zuwa wani
nau’i na yin ibada ta hanyar fuskantar ubangiji Allah (SWT) da kiran sa da
ganawa da shi da ƙasƙantar da kai da nuna kasawar bawa zuwa ga Mahalicci
(Allah) domin kwaɗayin samun taimakonsa na alherin duniya da na lahira. Haka
kuma da neman kariyarsa ta hanyar tunkuɗe duk wani sharri da bala’i da yayewar
baƙin ciki ko gusar da jin tsoro da tabbatar da aminci zuwa ga mai yin addu’a”
(Ainu, 2007).
A
tawa fahimta, addu’a na nufin kai koke da bayi ke yi a wurin Allah da roƙon a
biya musu buƙatunsu na alheri da waɗanda ba su ba, musamman a fagen siyasar
zamanin da ake ciki.
Ga
misalai kaɗan kamar haka:
……………………………………………………………………………….,
Wasko
na Jega bai halin ɗauki ga banza ba, Allah ya wa ragi albarka na gode,
Badamasi Augie Allah ya tsare ka ga
‘yan iska, magana ta gaskiya ba ta koma ƙarya ba.
…………………………………………………………………………………..,
Sai
godiya Aminu Suleiman gwauron dutse, mai tallaba kanai mashi illa na gode,
Sai
godiya Suleiman na Chiroma akwai himma, Allah ya bar ka tare da manya na gode,
Sai godiya magajin Sabla na gidan
mulki, faɗa da aljani ba riba na duba.
Duk
addu’o’in da ke cikin baitocin biyu na alheri ne zuwa ga masoya. Da farko
kyauta aka yi wa mawaƙin, shi kuma ya yi addu’a ga wanda ya ba shi kyautar da
cewa, Allah ya sanya albarka cikin dukiyarsa tare da yin godiya ga kyautar da
aka yi masa. A baitin kuma an sami mawaƙin ya ƙara yin irin addu’ar Allah ya yi
wa mutumin da ya ba shi kyauta tsari daga ‘yan iska. A baiti na biyu kuma mawaƙin
ya ƙara yi wa wani addu’ar Allah ya tsawaita zamansa da manya (Chiroma) saboda
alherin da ya yi masa a madadin Chiroma. A taƙaice an sami addu’o’in alheri a
cikin waƙar ba na sharri ba. Wannan bai hana a sami baƙar addu’a a cikin wata
waƙa ba.
5.0 Salailan Da Ke Cikin Waƙar
Masana
da dama sun bayyana abin da ake nufi da salo a nazarin waƙa. Daga cikinsu akwai
Abdullahi Bayero Yahya da ya ce:
“Salo yana nufin
duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda ake bi domin isar da saƙo, ita
wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga
mai sauraro ko mai karatun waƙar”.
Mawaƙin
ya yi amfani da irin wannan dabara domin isar da saƙonsa ga jama’a ta hanyar
amfani da salailai kamar haka:
5.1 Kamancen Fifiko
Kamancen
fifiko na nufin kawo abu biyu a wuri ɗaya tare da cewa ɗayan ya fi ɗaya.
Kalmomin da ake amfani da su domin nuna fifiko sun haɗa da fi da zarce da take
da wuce da ɗara da gota da tsere da sauransu, (Yahya, 1997).
Mawaƙin
waƙar ‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’ ya yi amfani da salon kamancen fifiko a
wurare da dama a cikin waƙarsa sai dai, za a kawo kaɗan daga cikinsu a matsayin
misali. Ga su kamar haka:
………………………………………………………………,
Karen
gida akwai rigima bai kashe ɓera ba, ƙarfin karan gado ya fi na sandag gwadda,
Ina
ganin ka ba ka gani na ɗan babule, mai jan faɗa ya ɓoye ai gwarzo ba.
Ɗan
kanzagin siyasa mai siffar ɗagutu, ni na daɗe ina son huce haushinka,
Wai
wane ɗan sarauta ne ko ɗan sa ɗaki? Wallai Chiroma ya fi gabanka ɗan kuka,
In
don ganin hurar wani bari tudda hura taka, ɗan ƙwaƙwale wutakka daban ce la
shakka,
Tafarnuwa ina son ki ina jin shakkun
ki, kowat taɓa ki ba zai yi rashin wari ba.
Idan
aka yi la’akari da abin da Yahya, 1997 ya ce, babu shakka an sami salon
kamancen fifiko a inda kalmomin ya fi suka fito a cikin baitocin biyu ta hanyar
da aka kawo abu biyu aka nuna ɗaya ya fi ɗaya. A nan an sami tabbacin fifiko
ake nunawa tsakanin karan gado da sandag gwadda da kuma fifikon da ke tsakanin
Chiroma da mutumin da ba a faɗi sunansa ba, mawaƙin na nuna cewa Chiroma ya fi
mutumin nesa ba kusa ba idan aka yi zancen kirki da sauransu.
5.2 Kamancen Daidaito
Kamancen
daidaito shi ne kamancen da ake cewa abu kaza daidai yake da abu kaza. An sami
irin hakan a cikin waƙar da ake sharhin jigoginta da salailanta inda aka sami
mawaƙin ya fito da su a wurare da dama, sai dai an kawo ƙalilan domin misali
kamar haka:
Chiroma
yanzu kai ne Kanta kai ne Mera, duk martabarsu na wajjenka sabbene,
Mai
kwarjini kama da daren salla ɗan zaki, manya da yara na ra’ayinka mun gane,
In
ka shigo mutane kowa sai ya tashi, ba wanda zai tare maka hanya ƙarya ne,
Ka gadi martaba da muhibba a gidan
mulki, ba mai buga ma bukka kwano na duba.
A
baitin, mawaƙin ya daidaita kwarjinin Chiroma ga jama’a da daren salla ƙarama
ko babba. Babu shakka ba yara kaɗai ba, har manya na marmarin daren kowace
salla domin muhimmin abu ce ga al’umma baki ɗaya. Mawaƙin ya nuna jama’a na
ra’ayin Chiroma kamar yadda ake marmarin daren salla domin farin cikin da ke
ciki na ƙawa da sauransu. Haka kuma, a baitin an kawo magana mai kama da
hakanan inda ya ce, Chiroma shi ne Kanta kuma shi ne Mera. Ƙari ga hakanan
kuma, inda ya ce duk martabobin waɗannan manyan mutane na wajen Chiroma. A taƙaice,
yana nufin da halin Kanta da na Mera da na Chiroma duk kat da kat suke bai rago
komai daga halayensu ba don haka shi ne su, musamman idan aka yi zancen
martabar gidan mulki. Wannan ma na nuni da cewa kamancen daidaito ne da aka
tsamo a cikin waƙar ‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’.
5.3 Dabbantarwa
“Salon
dabbantarwa na nufin ɗaukar wata sifa ta dabba a aza wa mutum ita da niyyar
girmamawa ko kuma wulaƙantawa ta hanyar aza wa mutum hali ko sifar dabbar da
aka yi amfani da ita a wajen zaɓen halittar ko ɗabi’arta domin a aza wa mutum
ita, (Yahya, 1997)”.
Mawaƙin
ya yi amfani da salon a inda ya wulaƙanta wani ta fuskar ambatar sifarsa da
halinsa wurin da ya kamanta shi da wata dabbar ruwa da ake kira boɗami da kuma
dabbar gida mai suna kare. Ga abin da ya ce:
……………………………………………………………………………………….,
Na
Chiroma Garba Garus mai ja maka ya taɓe, a gidan Chiroma ba ka da gefe na duba,
Ka kama gaskiya da amana ka wuce
gori, halinka ba irin halin boɗami ba.
Karen
gida akwai rigima bai kashe ɓera ba, ƙarfin karan gado ya fi na sandag gwadda,
Ina
ganin ka ba ka gani na ɗan babule, mai jan faɗa ya ɓoye ai ba raggo ba.
A
taƙaice, mawaƙin ya aibanta wani mutum ta fuskar danganta shi da halin rashin
kirki. Wanda duk ya san boɗami (kifi ne mai shigewa cikin laka, ya zauna tsawon
watanni shi kaɗai ba mai koma ganin sa sai ruwa ya komo ko kuma idan an fito da
shi saboda wani dalili na daban,amma ba ya fito da kansa ba. Mawaƙin ya yabi
Garba Garus da halin kirki ta hanyar faɗar cewa halinsa ba irin na boɗami ba
ne. Wannan ya nuna boɗami ba ya da hallin kirki kamar yadda aka ambata a baya.
Ma’ana, ɗan kaza ne, idan ya samu sai ya gudani dangi.
5.4 Abuntarwa
Abuntarwa
na nufin mayar da mutum ko dabba ko tsuntsu ko wani abu mai rai ya zama abu
maras rai (Yahya, 2007:46). Mawaƙin ya yi amfani da wannan salon wurin da aka
sami ya mayar da Aminu Suleiman dutse amma, ta hanyar ɗaukaka darajarsa ba wulaƙanta
shi ba kamar haka:
…………………………………………………………………………………..,
Sai
godiya Aminu Suleiman gwauron dutse,
mai tallaba kanai mashi illa na gode,
Sai
godiya Suleiman na Chiroma akwai himma, Allah ya bar ka tare da manya na gode,
Sai godiya magajin Sabla na gidan
mulki, faɗa da aljani ba riba na duba.
Mawaƙin
ya siffanta Aminu Suleiman da gwauron dutse (babban dutsen da ya fi gaban ɗauka
ga kowa) wanda duk ya ce ya tallabe shi wahala ce rabonsa domin ba ya iyawa, ƙarshe
sai ya halaka mutumin da ya ɗauke shi. Wannan ya tabbatar da cewa, mawaƙin ya
mayar da Aminu wani abu ta hanyar kiran sa dutse kuma gwauro (babba) ba ƙarami
ba. Ba za a ce wannan ne kaɗai salon abuntarwa a waƙar ba sai dai, shi aka kawo
a matsayin misali, don tabbatar da wannan salon a cikin waƙar.
5.5 Aron Kalmomi
Wannan
na nufin amfani da kalmomin Larabci ko Turanci da sauransu a cikin waƙa da mawaƙi
ke yi a cikin waƙarsa, (Yahya, 2007). Mawaƙin na amfani da kalmomin domin nuna ƙwarewa
da harshe da iya waƙa da kuma samar wa waƙarsa amon da ya dace da ita. Yahaya
ya yi haka a cikin waƙarsa inda ya yi amfani da kalmomin Larabci da na Turanci
a cikin wasu baitoci masu yawa kamar yadda ya kawo a cikin waƙarsa kamar haka:
………………………………………………………………………….,
In
don ganin hurar wani bari tudda hura taka, ɗan ƙwaƙwale wutakka daban ce la
shakka,
Abin
da kak kashe a baya a fatin APC, Allah kaɗai yake sakayya na duba,
………………………………………………………………………………….
Mai
hanƙuri Bala ceza (chaser) Bagudo mai Allah, zama da kai akwai alfanu na gode,
……………………………………………………………………………………..
Zagi
ɗan gwaggo duniya ba ka ɗauke ta da girma ba, na Chiroma dole in gaishe ka na gode,
Isah
direba shi ma bai yo mini ƙarya ba, ƙauna da ni da kai sai Allah na gode,
Ga
gaisuwa ga Ibrahim direba dottijo, sarkin gudu a bar maka hanya na gode,
Ɗan Sauwa ɗan sarauta ne Ɗahiru na gode,
mai hanƙurin zumunci ne ba raggo ba.
………………………………………………………………………,
Zan
je na iske Sani thirty-fourty (3040) manya, na Magaji ba a jin kukanka na gode,
Wasko
na Jega bai yi halin ɗauki ga banza ba, Allah ya wa ragi albarka na gode,
Badamasi Augie Allah ya tsare ka ga
‘yan iska, magana ta gaskiya ba ta koma ƙarya ba.
…………………………………………………………………………………………,
Ga
odalen Chiroma Bashar tafi da ƙarfinka, halinka ba irin na birai ba na gode,
Sai
godiya Bashar Ɗanmalam ka san hanya, tuƙinka ba irin na direban mata ba.
A
cikin waƙar an yi amfani da kalmar Larabci (la shakka) da na Turanci da suka haɗa
da party da APC da chaser da driver da thirty da fourty da orderly da sauransu.
Duk kalmar da aka yi amfani da ita ta hanyar aro sai da aka dubi wurin da ta
dace aka sanya ta, kuma ta fito da abin da mawaƙin ke son ya faɗa a cikin waƙarsa
domin samar da kari ko sautin waƙarsa. Kalmomin da aka yi amfani da su na ɗauke
da ma’ana kamar haka: La shakka= babu shakka, babu kokwanto, tabbas. Party=
fati. APC (All People’s Congress)= Fati haɗa kan al’umma, Jam’iyyar Kawo
Cigaban al’umma. Chaser = mai biyar abu har sai ya kai ga biyan buƙata. Driver=
mai tuƙi/direba a matsayin kalmar aro ta Turanci. Thirty=talatin. Fourty=
arba’in. Orderly= mai tsaron mutum/mai kula da mutum/sarkin yaƙi/zagin wani
mutum.
5.6 Kinaya
Kinaya
na nufin kiran abu, musamman mutum, da sunan da ba shi ne nasa da aka san shi
da shi ba, domin wannan suna ya bayar da ma’anarsa da kuma tunanin da ma’anar
za ta kawo zuwa ga wanda aka kira da wannan suna, shi ake kira salon kinaya
(Yahaya, 1997). Mawaƙin ya yi amfani da wasu sunaye da ya kira Chiroma da su da
suke ɗagawar daraja yake nufi kuma wanda aka kira da sunayen ya yi na’am da su
ba tare da ya kore ba. Sunayen sun faranta masa rai kuma a bayyane ɗagawar
daraja ce ga wanda aka yi wa waƙar. An sami wuraren da mawaƙin ya kira mutumin
da sunayen da ba a san shi da su ba, amma sunayen sun ba da ma’ana kuma,
tunanin ma’anar za ta kawo zuwa ga wanda aka kira da su. Ma’ana wanda aka kira
da sunan zai ji daɗi, shi kuma wanda ya kira shi da sunan ya yi ne domin ya ji
daɗi. Babu shakka Chiroma ya ji daɗin sunayen da aka kira shi da su domin ɗaukaka
shi aka yi ba ƙasƙantar da shi ba. Ga abin da mawaƙin ya ce:
Yanzu
dai talakawa ka faɗin ka dace, ko’ina kana da darajja ɗan zaki,
Chiroma
yanzu ka zama gwanki mai rangwangwan, a ja da kai a kwanta ɗaki a yi raki,
Ka ɗau
mutum ka ɗau kayanai ko bai so ba, angon Halima ba ka da shakka ko raki,
Sai ba ka nan maza suka ƙaryar nuna
bajinta, in ka fito kamar ba magana sun kai ba.
A
cikin daji babu dabbar da ta kai zaki daraja da martaba da iko. Akwai tsammanin
cewa, duk inda saniyar gaba ta sha ruwa nan ta baya ke sha. Wannan ya sanya
mawaƙin ce wa Chiroma zaki ɗan zaki, saboda ɗaga darajarsa ya yi ba nakasa shi
ba. Haka kuma, kiran da aka yi masa da cewa gwanki mai rangwangwan cicciɓa shi
aka yi zuwa ga matsayin da wani bai sami kai gare shi ba. Rangwangwan magani ne
da duk yadda ‘yan adawa suka buƙaci kai ga jikin mutum, ba za su iya ba, hasali
ma kafin su kai gare shi sun faɗi ƙasa. A taƙaice, ana nufin Chiroma ya buwayi
‘yan adawa ta kowace fuska, domin ya fi ƙarfinsu.
5.7 Karin Magana
Karin
magana wani gajeren zance ne mai ɗauke da bayani mai yawa idan za a tsaya a yi
bayani sosai. Doguwar magana ce aka kakkarya ta koma gajeruwa domin taƙaita
wasu maganganu ta hanyar furta ta. Mawaƙa na amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu
a wasu lokuta domin taƙaita wasu maganganu da suke da a zukatansu. Sukan yi su
domin ɓatar da bami a cikin wata magana kuma sukan yi domin aika habaici ga
wani ko wasu mutane dangane da wani al’amarin da ba sai an bayyana sosai ba.
Yahaya Sauwa na daga cikin mawaƙan da ke amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsa
koyaushe. Hasali ma, yakan samar da sunayen wasu waƙoƙinsa ta hanyar amfani da
karin magana. Duk mai sauraron waƙoƙinsa ya san da haka idan yana fahimtar
abubuwan da ke cikin waƙoƙinsa. An tsinci wasu karin maganganu a cikin waƙar
‘Wutar Kara Izan Masu Ɗiya’ da suka haɗa da waɗannan:
……………………………………………………………………………………….,
Musa
a gaida ɗan Ɗakingari na al’umma, mai haƙuri
yana dafa dutse gwarzo ne,
Tungar Rini za ni na in iske
Abdullahi, kwas sanka bai ganin laifinka na duba.
…………………………………………………………………………,
Kura
da shan bugu gardi da karɓe kuɗɗinshi, mai yaudara ba zai iya halin girma ba,
Wallahi to Abu Hali ka kai dottijo,
ka ba su baya ba da buƙatar komai ba.
Sallama
nikai al’umma na jaha tamu, ga ni nan da sabon launi kun ji ni,
Yahaya
Sauwa ne da Zuwaira ta Kanon Dabo, za mu aika saƙon waƙa don nuni,
Abin
da zan faɗi ban sa son raina ciki ba, gwargwadon fahimta ku tsaya ku yi auni,
Rashin sani ka sa kaza kwana bisa
damma, safiya ta waye ta yi ƙwacen
tsaba.
A
baitoci uku na sama an sami karin magana a cikin kowane. A baiti na ɗaya akwai karin
maganar nan da Hausawa ke cewa “Mai haƙuri yana dafa dutse har ya sha romonsa”,
ammasaboda lalurar waƙa aka yanke maganar aka tsaya nan. Haka kuma a baiti na
biyu akwai karin maganar da Hausawa ke cewa, “Kura da shan bugu Gardi da karɓar
kuɗi”. A na uku kuma, mawaƙin ya kawo karin maganar nan mai cewa “Rashin sani
ya fi dare duhu”. Daga nan aka alaƙanta kaza da kwana a kan dame don rashin
sani domin tsaba kaza ke nema da rana ruwa a jallo, a ce ta kwana a kan dame? Babu
shakka rashin sani ya tabbata.
6.0 Kammalawa
A
cikin takardar an tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da tsakure da
gabatarwa da kawo taƙaitaccen tarihin mawaƙin haɗi da tarihin waƙar kanta. Biye
da waɗannan an kawo sharhin jigogin waƙar babba da ƙanana da suka haɗa da
tallar ɗan takara da ƙananan jigogin yabo ta fuskoki daban-daban da suka haɗa
da addini da halayen kirki da jaruntaka da mulki da zuga da habaici da zambo da
kuma addu’a. Haka kuma an yi sharhin salailan da suka fito a cikin waƙar da
suka haɗa da kamancen fifiko da na daidaito da salon dabbantarwa da na
abuntarwa da aron kalmomi da salon kinaya da kuma amfani da karin magana. A ƙarshen
takardar, kammalawa ta biyo baya tare da manazarta.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.