Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwalliyar Matan Garin Gusau (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Kwalliyar Matan Garin Gusau (6)

NA

ƊAYYABA MUSTAPHA IBRAHIM

Kwalliya

BABI NA BIYAR

5.0 GABATARWA

A wannan babi na biyar za a kammala wannan aiki inda za a duba shawarwari da kammalawa tare da saamakon binciken da kuma manazarta.

 

5.1 SHAWARWARI

Shawarwarin da zan ba ma ‘yan uwana ɗalibai masu tasowa da malamai na ita ce:

- A ko da yaushe idan za a bama ɗalibi mai bincike aiki ya kamata a duba cikin al’adunmu waɗanda ba a yi rubutu a kan su ba gudun sakan kan cewar wasu al’adu.

- Sannan kuma ina bama Malamai na shawara akan idan mai bincike ya binciko aiki yana da kyau su duba aikin da kyau dan ganin aikin ya tafi yadda ake so.

- Haka kuma ina bama Malamai na shawara kan; idan mai bincike ya binciko wani abu na al’adun mu na gado waɗanda suka fara ɓacewa a rinƙa bugasu a cikin littafai saboda yara masu tasowa.

- Shawara da zan ba ma yan uwa na ɗalibai, ita ce ako da yaushe zaka yi bincike yana da kyau ka yi bincike yadda ya kamata, domin ƙaruwarka da ta yan uwanka ɗalibai masu tasowa.

- Sannan kuma ɗalibai ‘yan uwana kudena kwafe aikin wani mai bincike, idan kunyi haka kunzama marasa kishin kanku da al’adunku.

5.2 KAMMALAWA

A cikin wannan aiki mai suna “Kwalliyar Matan Garin Gusau”, an duba abubuwa kamar haka. Babi na ɗaya an duba dalilin gudanar da bincike da muhallin bincike da manufar bincike da muhimmancin bincike da matsalolin bincike sai kammalawa.

 

A babi na biyu kuma an duba bitar ayyukan da suka gabata, sannan gabatarwa, kundayen bincike na ɗaya har zuwa na uku sai littafai da maƙalu, jaridu sai kammalawa.

 

Sai babi na uku inda aka duba samuwar kwalliya da ma’anar kwalliya da nau’oin kwalliya da amfanin kwalliya da kuma kammalawa.

 

Sai babi na huɗu inda nan ne gundarin aikin, an duba gabatarwa, kwalliyar matan Gusau, kwalliyar mata ƙanana, kwalliyar ‘yan mata, kwalliyar zawarawa, kwalliyar matan aure sai kammalawa.

 

Sai kuma babi na biyar inda a nan ne aka kammala wannan aiki, an duba gabatarwa da shawarwari, da kammalawa, tare da sakamakon bincike sai manazarta. Waɗannan sune abubuwa da aka duba a cikin wannan aiki mai taken “Kwalliyar Matan Garin Gusau:.

Wannan bincike ya samu sakamako masu muhimmanci da amfani gare ni da kuma waɗanda zasu duba wannan kundin bincike wato ɗalibai masu tasowa, sakamakon sun haɗa da:

-          Sakamakon wannan bincike aka samo tarihin samuwar kwalliya ta mata

-          Sakamakon wannan bincike an gano wasu kwalliyar tsaga na gargajiya da mata suke yi domin kwalliyar su ta yau da gobe

-          Sakamakon wannan bincike an gano wasu tufafi na mata na gargajiya waɗanda uwaye da kakanni suke amfani da su kamar. Bakurɗe, saƙi, tsamiya, bante, ɗanbarasoso, bunu, kuɗu, wajen kwalliyar su ta yau da kullum.

-          Sakamakon wannan bincike aka gano wasu riguna na gargajiya da ake amfani da su wajen kwalliyar yau da kullum.

-          Haka kuma sakamakon wannan bincike an gano kwalliyar mayafi da kallabi kamar su mayafin shata da kallabin soro, da taguma wajen kwalliya.

-          Sakamakon wannan bincike aka gano takalmi na gargajiya kamar balka, sambatsi da bindin shirwa.

-          Sakamakon wannan bincike an gano kayan kwalliya na mata na gargajiya kamar kayan kwalliya na hanci da na wuya, irin su sarƙa da kayan kwalliya na hannu kamar agogo da warwaro wajen kwalliyar su ta yau da kullum.

-          Sakamakon wannan bincike an gano kitson gargajiya irin su kitson Kwando, kabarin karuwa da sauransu.

-          Sakamakon wannan bincike an gano ire-iren kwalliyar da mata suke yi wa hannunsu na gargajiya kamar dayis da kuma lalle  

-          Sakamakon wannan bincike an gano kwalliyar fuska ta shafe-shafe na gargajiya waɗanda suke amfani da su wajen kwalliyar fuska kamar Hure, Katambin, Fankeke, Kwalli, gazal.

-          Sakamakon wannan bincike an gano wasu tufafin zamani bayan na gargajiya irin su shadda, Leshi, Atamfa, da sauransu na kwalliya.

-          Sakamakon wannan bincike an gano canjin riguna na zamani bayan na gargajiya kamar; rigar sitela. Amburela wajen kwalliyar su.

-          Sakamakon wannan bincike an gano wasu kitso na zamani da aka samu bayan na gargajiya kamar zane da wibin da kitson gana wibin da tuwistin wajen kwalliyar gashin kai.

-          Sakamakon wannan bincike an gano bayan kitso yanzu ana zuwa salon domin gyaran gashi inda ake amfani da shamfo, diraya da sitireca, domin kwalliyar gashin kai.

-          Sakamakon wannan bincike an gano sababbin kayan shafe-shafen da a ake amfani da su wajen kwalliya irin su hodar foundation da hoda da gazal da eye shadow da kwansila da jan baki da mascara domin kwalliyar fuska.

-          Sakamakon wannan bincike an gano bambanci tsakanin kwaliyar mata ƙanana da ta ‘yan mata da zawarawa da matan aure.

Waɗannan sune sakamakon binciken kwalliyar matan garin Gusau 

 

MANAZARTA

Aliyu, S. (1983). Dukanci a Birnin Kano a Matsayinsa na Ɗaya cikin Sana’o’in Hausawa na Gargajiya Kundin Digiri na Ɗaya, Kano. Jami’ar Bayero.

Augie, A. (1983) Tsagen Fuska da Muhimmancinsa ga Mutanen Jihar Sakkwato. Kundin Digiri na Ɗaya, Sakkwato, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ɓatagarawa S.A. (2014). Neman Wasu Au’du a kan Sana’o’in Gargajiya na Hausawa Mazauna Lakoja a Cikin Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa Zaria, Kundi na Biyu, Jami’ar Ahmadu Bello.

CNHN. (2006) Ƙamusun Hausa Zaria, Jami’ar Ahmadu Bello

Kado M. (1986). Saƙa Sana’ar Sarrafa Auduga a Ƙasar Hausa Tasirinta da

Muhimmancinta ga Al’ummar Hausawa, Kundin Digiri na Ɗaya Kano: Jami’ar Bayero.

Madabo M.H (1979). “Ciniki da Sana’o’in Ƙasar Hausa” Ikeja Lagos. Thomas Nelson Nigeria Limited.

Mam, A. (1966). “Zuwan Turawa Nigeria ta Arewa” Zaria NNPC.

Mashi, A.A (2000). “Zama da Maɗaukin Kanwa”: Tasirin Zamananci kan Rayuwar Hausawa, Kundin Digiri na Biyu Kano. Jami’ar Bayero

Musa B.A (1981). Sana’ar Kura a Birnin Kano Kundin Digiri na Ɗaya,Jami’ar Bayero

Musa, U. (1983). Wanzanci a Ƙasar Hausa, Kundin Digiri na Ɗaya Kano; Jami’ar Bayero. 74

Nadabo S. da Yola M (1989). Kwalliya da Adon Hausawa, Kundin Digiri na ɗaya, Sokoto; Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Sulaiman (1990), Tsagar Gargajiya a Ƙasar Kano, Nazarin Ire-iren Tsaga da Muhimmancinta tare da Matsayinta ga Al’ummar Hausawa  Kundin Digiri na Biyu, Kano Jami’ar Bayero.

Sallau B.A. (2000). Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’ar a Ƙasar Hausa: Kundin Digiri na Uku. Kano Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.

Sanda F.U. (2004). Sana’ar Kitso a Ƙasar Hausa Kundin Digiri na Ɗaya. Kano, Jami’ar Bayero.

Yakasai M.G. (1992) Tufafin Hausawa, Kundin Digiri na Ɗaya, Sokoto, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yola M.M (2014) “Nason Baƙin Al’adu a kan Kwalliyar Al’adan Hausawa Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Post a Comment

0 Comments