Ticker

6/recent/ticker-posts

Adashen Mata A Garin Gusau (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Adashen Mata A Garin Gusau (1)

NA

AMINA ABUBAKAR

Kudi

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki ga iyayena, Allah ya gafarta masu, Allah ya sa su aljannah da rahama. Allah ya saka masu da alhairi, amin.

GODIYA

Da Sunan Allah mai rahama mai jinƙai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya sanar da Ɗan’adam abin da bai sani ba. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka bi tafarkinsa da kyautatawa.

Haƙiƙa wannan aiki ya samu gudummuwa da shawarwari daga mutane da dama wanda ya zama dole in miƙa cikakkiyar godiyata gare su. Godiya ta musamman tare da cikakkiyar girmamawa ga malam Isah S/Fada wanda shi ne ya ɗauki ɗawainiyar duba wannan aiki tun daga farko har ƙarshe. Allah ya ba da lada.

Bayan nan kuma ina miƙa cikakkiyar godiyata da fatar alheri ga Shehin malami, Prof. Aliyu M Bunza, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙaro cigaba a rayuwa.

Haka kuma ina sake miƙa godiya da fatar alheri ga babana Aliyu Rabi’u Ɗangulbi, tare da malam Abdullahi Musa, Allah ya saka masu da alkhairi, Allah ya ƙaro ci gaba a rayuwarsu.

Haka kuma ina ƙara miƙa cikakkiyar godiya tare da girmamawa ga malaman Jami’ar Bayero Kano, na Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Allah ya saka da alkairi, Allah ya taimake su a rayuwa, Allah ya sa su gama da duniya lafiya.

Haka kuma ina miƙa godiyata da fatar alkhairi ga malam Haruna Maikwari, malami a Kwalejin Ilimi da Ƙere-ƙere ta Tarayya da ke Gusau. Haka zalika ina miƙa godiyata ta musamman ga iyayena, marigayi Alh. Abubakar Moriki, da Fatima Muhammad Moriki Allah ya gafarta masu, ina miƙa godiyata ga yayyena irin su; Hajiya Hauwa’u Abu Moriki, Hajiya A’isha Abu Moriki, Jamilu Abu Moriki, Surajo Abu Moriki, Auwal Abu Moriki, Mustapha Abu Moriki, Bashar Abu Moriki, Aminu Abu Moriki, da Sanusi Abu Moriki.

Bayan nan ina miƙa cikakkiyar godiyata ga ƙannena irin su Murtala Abu Moriki, Mujtafa Abu Moriki, Muntaƙa Abu Moriki, da kuma yar uwa Zinnira Bello Maru da A’isha Ibrahim Muhammad.

Har ila yau ina miƙa cikakkiyar godiya da girmamawa tare da jinjinar ban girma ga mijina Muhammad Jamil. Allah ya saka mashi da Alheri, Allah ya sa ka gama da duniya lafiya, Allah ya sanya wa rayuwarka albarka, Allah ya kare ka ga dukkan sharrin dake cikin rayuwa.

Ina miƙa godiyata ga ‘ya’yana Sadiƙ da A’isha Allah ya albarkaci rayuwarku, Allah ya baku ilimi mai albarka.

Sai godiya ga abokan karatuna, irin su: Dayyaba M. Ibrahim, Abubakar Hassan Faskari, Mustapha Sa’idu Faskari, Abdulrashid S. Fawa, Abdulrahman Bala, Nasiru Hassan Kabara, Ahmad M. Kabir, Bashar Isyaku, Sani Adamu, Aliyu S. Ibrahim, Hizbullahi Ɗan Lami, Nura Kwatarkwashi, da Hassan Galadima, Allah ya saka muku da alheri.

 

A ƙarshen wannan bincike ina miƙa godiyata ga dukkan wanda bai ji sunansa ba, da sauran al’ummar musulmi baki ɗaya.

TSAKURE

Wannan bincike, zai yi bayani a kan adashe wato yanda ake gudanar da adashe a garin Gusau, da kuma muhimamncin adashe da matsalolin dake tattare a cikin adashe. Bugu da ƙari, binciken zai yi bayanin ire-iren adashe da ake da su da kuma yadda ake gudanar da su. Bugu da ƙari, za a yi bayani a kan taƙaitaccen tarihin garin Gusau. Daɗin daɗawa, bincike zai yi tsokaci a kan ire-iren sana’a da muhimmancin sana’a a ga al’umma. Daga ƙarshe kuma za a kammala bincike tare da shawarwarin da aka samu a wajen malamai da sauran ɗaiɗaikun mutane.

Post a Comment

0 Comments