Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwalliyar Matan Garin Gusau (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Kwalliyar Matan Garin Gusau (2)

NA

ƊAYYABA MUSTAPHA IBRAHIM

Kwalliya

BABI NA ƊAYA

1.0 GABATARWA

A wannan babi na farko za a duba ma’anar tsafta wadda ita ce mafarin kwalliya, dalilin gudanar da bincike, muhallin bincike, manufar bincike, hanyoyin gudanar da bincike, farfajiyar bincike, muhimmancin bincike, matsalolin bincike sai kuma kammalawa.

 

Tsafta a taƙaice kalmace da ke nufin kawar da ƙanta ko dauɗa ko datti da kuma mummunan wari ko kawar da duk wani abu da baya da kyawon gani. Dan haka tsafta ta shafi abubuwa da dama, kamar su tsaftar jiki, tsaftar kaya, tsaftar muhalli da sauransu.

 

1.1 DALILIN GUDANAR DA BINCIKE

Dalilin wannan bincike shi ne binciko wasu abubuwan kwalliya na mata saboda fito da su sarari dan sanin abin da mata ke yin amfani da su na kwalliyarsu ta yau da kullum.

 

Haka kuma gano wasu abubuwa wanda ba a san su ba da kuma waɗanda kakannin mu suka yi amfani da su domin adanasu saboda masu karatu da binciken tarihi.

1.2 MUHALLIN BINCIKE

A kowa ne bincike yana da muhallin gudanar da shi to wannan bincike nawa muhallin yin shi shi ne cikin garin Gusau da shiyoyin ta waɗanda suka haɗa da shiyar Mayana, shiyar Galadima, shiyar Tudun Wada sai kuma Shiyar Sabon Gari waɗannan shiyoyi a kan su ne bincike zai tsaya.

1.3 MANUFAR BINCIKE

Kowa ne irin aiki yana da manufar yinsa, to haka shi ma wannan aiki yana da manufofinsa da suka saka akayi wannan bincike, waɗannan manufofi sun haɗa da:

Manufar wannan bincike ita ce fito da ainihin kwalliyar matan garin Gusau domin yara masu tasowa su san ainihin kwalliyar da mata suke yi a wannan lokaci kamar yadda nima na samu.

 

1.4 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Kowa ne aiki ko bincike yana da hanyoyin da akebi wajen gudanar da shi kamar yadda Hausawa kance kowa yaɗebo da zafi bakinsa.

 

Wannan bincike ya bi muhimman hanyoyi domin kammala shi. Daga ciki waɗannan hanyoyi sun haɗa da duba ayyukan da suka gabata na kundayen bincike na digiri na ɗaya zuwa na uku, da littafai, da jaridu, da mujallu, da kasidu, waɗanda masu bincike suka yi rubutu akai masu alaƙa da wannan bincike.

 

Wannan bincike an yi amfani da hanyoyi daban-daban yadda ya dace, domin ko wane mai bincike yakan bi wasu hanyoyi daban-daban da suka dace da binciken sa kamar yadda masu iya magana kan ce “mai ɗaki shi yasan inda yake masa ruwa” to haka yake ko wane mai bincike shi yasan hanyoyin da suka dace ya bi domin gudanar da bincikensa.

 

1.5 FARFAJIYAR BINCIKE

Sanin kowa ne aiki na duniya yana da iyaka, sai ikon Allah ne kawai bai da iyaka; to haka ne wannan aiki nawa yana da iyaka, iyakar aikina shi ne a Gusau kawai zai yi shawagi nai ya gama. Wato zai binciko ma’anar kwalliya da asalinta da kuma ire-irensa da kuma masu yinta tare da tasirin ta ga mata.

 

1.6 MUHIMMANCIN BINCIKE

Muhimmanci kalma ce mai nuna abu mai daraja ko mai ƙima kamar yadda masana suka faɗi cewa, bincike shi ne gano wani abu domin a sanshi a kuma ƙara fahimtarsa da irin muhimmancinsa da kuma cigabansa ga rayuwar al’ummar Hausawa.

 

Haka kuma, bincike a kan kwalliyar mata a Hausa ko al’ummar Hausawa zai nuna ƙaruwar ilimi ga jama’a wanda ya haɗa da al’adun Hausawa da shi harshen kansa.

 

1.7 MATSALOLIN BINCIKE

Ita wannan kalma ta matsala ta zama wajibi ga kowa ne mai karatu ko mai bincike ko mai rubutu zai fuskanta a lokacin da ake yinsa. Haka wannan bincike ya haɗu da matsaloli daga ɓangarori daban-daban.

An samu matsala ta rashin isasshen lokacin gudanar da binciken, wanda wannan bincike ya kamata a ce ya samu aƙalla shekaru ana gudanar da shi ba yan watanni ba.

 

Sai kuma matsalar kuɗi masu gidan rana, saboda duk inda za a je wajen bincike sai an kashi kuɗi.

 

1.8 KAMMALAWA

A kammale wannan babi an duba abubuwa da yakamata kowa ne yatafi kai tsaye akan bincikensa. Wannan dalili shi ya sa mu ka fara duba dalilin dayasa za a yi wannan bincike, saboda shi ne farko kan komi da za a yi to a ka yi akwai dalilin yinsa, sai kuma muhallin yinsa, da kuma hanyoyin gudanar da shi da farfajiyar gudanar da shi sai kuma muhimmancinsa da matsalolinsa a taƙaice.

Post a Comment

0 Comments