Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwalliyar Matan Garin Gusau (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Kwalliyar Matan Garin Gusau (1)

NA

ƊAYYABA MUSTAPHA IBRAHIM

Kwalliya

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki nawa ga mahaifiyata Hajiya Maimunatu Aliyu, Allah ya jiƙanta da rahama, sai kuma mahaifina Alhaji Mustapha Ibrahim, da kuma yayata Hajiya Hadiza Mustapha Ibrahim waɗanda da taimakonsu ne cikin yardar ubangiji aka fara wannan karatu lafiya kuma aka gama lafiya. Allah ya saka da mafificin alheri.

TSAKURE

Wannan kundi yana ƙunshe da bayanai akan Kwalliyar Mata a Garin Gusau, da ire-irenta da nau’o’inta da amfaninta, da kuma yanda mata ƙanana ke yin kwalliya da ‘yan mata da zawarawa, da kuma matan aure.  Daga ƙarshe, an bayar da shawarwari a kan yadda za a bunƙasa Kwalliya. Akwai kammalawa da kuma manazarta.

 

GODIYA

Ina fara jaddada godiyata ga Allah (S.W.T) mai rahama mai jinƙai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) da sahabbansa da zuri’arsa da dukkan wanda ya bi tafarkinsa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka, ina miƙa godiya da jinjina zuwa ga mahaifiyata Hajiya Maimunatu da Mahaifina Alhaji Almustapha Ibrahim a bisa jajircewarta domin ta ga na kammala wannan karatu, kuma na gode da irin addu’o’in da take yi mini ba dare ba rana. Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, ya sanya Al-Janna Firdausi ta kasance makoma a gareta.

Bayan haka, sai godiya da jinjina zuwa ga yayyena da kuma ƙannena a bisa gudunmawarsu ta fuskoki daban-daban, tun daga addu’o’i, shawarwari da kuma kayan aiki daga cikinsu akwai; Aunty Hadiza, Aunty Hannatu, Yaya Babawo, Aunty A’isha, Aunty Halima da kuma kanene Attahir, da kuma Maimunatu da Fatima, da Sani, Rabiatu da kuma Hafsatu, duk Allah ya saka masu da mafificin alkhairi.

Godiya ta musamman ga malamai na musamman na sashenmu, dangane da gudummawar da suka bani da kuma shawarwari. Haka kuma ina miƙa godiyata ta musamman ga Malamai kamar su; Prof. Aliyu Muhammad Bunza, Prof. M.T Yakawada, Prof. Balarabe, Malam Rabi’u A. Ɗangulbi da malam Isah S. Fada da malam Musa Abdullahi da Dr. Nazir Abbas da Dr. Tahir da Dr. Fadama da Dr. S. Gulbi da sauransu. Allah ya saka da mafificin alheri.

Bayan haka, ina miƙa godiya da jinjina ga malamina kuma wanda ya duba wannan aiki Malam Musa Abdullahi bisa ɗorani a kan hanya da kuma haƙuri da ya yi da ni lokacin gudanar da wannan aiki. Allah ya saka da alheri.

Bayan haka ina miƙa godiya ta ga mutanen da aka yi hira da su a lokacin gudanar da wannan aiki, musamman yadda suke ba da lokacinsu sannan kuma suna da karamci, daga cikinsu akwai; Malama Halimatu, Malama Hurriya Mai Kwalliya da dai sauransu.

 

Haka kuma, ina miƙa godiyata zuwa ga abokan karatuna dangane da taimakon da su yi mini ta fuskoki daban-daban, nagode da kulawarku, Aunty Amina, Abubakar Hassan, Abdulrashid S. Fawa, Ahmad M. Kabir, Abdulrahman Bala (ABG), Aliyu S. Ibrahim, Bashir Isiyaku, Mustapha Sa’idu, Hassan Galadima, Nura S. Kwatarkwashi, Hizbullahi Ɗanlami.

Haka kuma akwai godiya zuwa ga abokaina na musmaman waɗanda ba zan manta da su ba, kamar irin su; Safiyya Ahmad, Wasila Sani, Rahila Aliyu da Zainab Sani

A ƙarshe ina miƙa godiya ta musamman ga Faisal Musa bisa ga addu’arshi da kuma jajircewa wurin hakar karatuna na gode, Allah ya saka da mafificin alheri.

Post a Comment

0 Comments